Liverpool na neman Beukema, Man Utd da Chelsea da Newcastle na son Malen

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta gabatar da bukatar sayen dan bayan Netherlands Sam Beukema, mai shekara 27, daga Napoli, inda ake ganin cinikin zai kai yuro miliyan 28. (AreaNapoli, daga Teamtalk)
An bai wa Arsenal, da Chelsea, da kuma Manchester United, damar sayen dan wasan gaba na gefe Rafael Leao, na Portugal, mai shekara 26, daga AC Milan, wadda a shirye take ta karbi tayin wajen yuro miliyan 50. (The Hard Tackle)
Haka kuma Manchester United za ta iya zawarcin tsohon dan wasan tsakiya na Nottingham Forest Danilo, mai shekara 25, wanda a yanzu yake wa kungiyar Botafogo ta kasarsa Brazil, wasa. (Fogao.net daga SportWitness)
A shirye Roma take ta yi amfani da damar da take da ita ta sayen Donyell Malen daga Aston Villa a kan yuro miliyan 25 (£21.6m). Dan wasan mai shekara 27, na Netherlands wanda ke zaman aro ya ci wa kungiyar ta Italiya kwallo 12 tun da ya je a watan Janairu. (Voetbal International daga Express & Star)
Sai dai kuma, Manchester United, da Chelsea, da kuma Newcastle United su ma suna son Malen, din wanda farashinsa zai iya kaiwa yuro miliyan 30 (£25.9m). (Corriere Dello Sport daga Manchester Evening News)
Aston Villa da Newcastle United suna son mai tsaron ragar Manchester City da Ingila James Trafford, mai shekara 23, da kuma golan Real Sociedad Alex Remiro, dan Sifaniya mai shekara 31. (Football Insider)
Goncalo Ramos, mai shekara 24, na son ganin ana sa shi a wasanni sosai tun daga farkon karawa, saboda rashin samun hakan zai iya barin Paris St-Germain a karshen kakar nan, inda kungiyoyi da dama suke son dan gaban na Portugal. (Fabrizio Romano)
Leeds United na son fam miliyan 10 a kan dan wasan gaba na gefe Largie Ramazani, na Belgium, mai shekara 25, wanda ya ci kwallo shida a wasa 13 da ya yi tun bayan da kungiyar ta karbi aronsa na kaka daya daga Valencia. (Football Insider)








