Matar da ta samu ciki ɗaya daga mazaje biyu

Asalin hoton, David Zorrakino/Europa Press via Getty Images
- Marubuci, Santiago Vanegas
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Mundo
- Lokacin karatu: Minti 4
A shekarar 2018, wata mata ta je ɗakin gwaje-gwajen ƙwayoyin halitta a Jami'ar National University ta Colombia domin tabbatar da ainihin mahafin tagwayenta maza masu shekara biyu a duniya.
Sai masu bincike suka gudanar da gwaje-gwaje, sannan suka sake maimaitawa.
Sun maimaita ne domin tabbatar da abin da suka gani na mamaki. Ita ce mahaifiyar tagwayen, amma kowanne mahaifinsa daban.
Wannan wani yanayi ne da ba a cika samu ba da ake kira heteropaternal superfecundation.
Kusan sau 20 ne kacal aka samu labarin irin haka a mujallun kimiyya a duniya.
Masana a jami'ar su ce za su iya samun haka, amma ba su taɓa ganin haka ba.
Wannan ya sa suka ƙara ƙaimi wajen zurfafafa bincike.

Asalin hoton, Drs Producoes via Getty Images
Yadda binciken ya wakana
Domin gwajin gano asalin iyayen tagwayen, masana a cibiyar nazarin ƙwayoyin halitta a Jami'ar National University ta Colombia sun yi amfani da wata kimiyya da ake kira microsatellite markers.
A taƙaice kimiyyar na nufin nazartar ƙananan ƙwayoyin halitta na kowane yaron da mahaifiyar da kuma waɗanda ake tunanin su ne iyayen maza, sai a kwatanta sakamakon da ke ƙunshe a cikin bayanan kowace ƙwayar halitta.
"Mun ɗauki ƙwayar halittar DNA na kowane daga cikin su tsakanin ɓangare 15 zuwa 20 da ake kira microsatellites sai muka kwatanta su ɗaya bayan ɗaya," in ji Farfesa William Usaquén, daraktan ɗakin gwaje-gwajen a zantawarsa da BBC Mundo.
Sai dai tsarin bincike na da faɗi da girman da ya wuce yadda aka saba na haska ƙwayar halittar da na'urar kallon ƙananan ƙwayoyin halitta.

Asalin hoton, Getty Images
Sai su saka ƙwayoyin halittar a wata na'ura da ke ƙara girman abu, sannan suka nazarce su ɗaya bayan daya.
Bayan nan ne sai a tura sakamakon ta wata kwamfutar, wadda za ta sake nazartar kowane sakamako tare da mayar da sakamakon ya zama hoto mai ɗauke da lambobi da ake kira electrophoresis.
A ƙarshe sai masana kimiyyar su yi amfani da sakamakon wajen gano aininin mahaifin kowane yaron daga ciki.
Idan rabin ƙwayoyin halittar yaron ya yi kamanceceniya da na mahaifiyarsa, sannan ɗayan rabin ya yi daidai da wanda ake tunanin shi ne mahaifin, shi ke nan an tabbatar da iyayen jaririn.
Sakamako mai ɗaure kai
Da masana suke nazarin ƙwayoyin halittar tagwayen na Colombia, sai suka nazarci ƙananan ƙwayoyin halitta 17 na mahaifiyar da tagwayen da wanda ake tunanin shi ne mahaifin su.
Sai suka gano ƙwayar halittar mutumin ya yi daidai ne da ɗaya daga cikin tagwayen, amma bai yi daidai da na ɗayan ba.
"Kusan shekara 26 ke nan ina daraktan ɗakin gwaje-gwajen nan, amma wannan ne karon farko da na ga irin wannan sakamakon," in ji Usaquén.
"Mun samu labarin cewa ana iya samun irin wannan lamarin, amma ba a cika samu ba," in ji Andrea Casas, masanin kimiyyar ƙwayoyin halitta a Jami'ar National University ta Colombia.

Asalin hoton, andipantz via Getty Images
Me ya sa ba a cika samu ba?
A wata maƙala da aka rubuta 2014 a wani ɗakin gwaje-gwaje a Baltimore da ke Amurka, an gano cewa a cikin gwaje-gwajen gano asalin iyaye guda 39,000 da aka yi, an samu irin wannan yanayin guda uku.
Usaquén ya yi bayanin me ya sa ba a cika samun haka ba.
"Da farko dole ya kasance matar tana saduwa da maza biyu. Na biyu ya kasance ta sadu da su a jere, wato ba tare da ɗaukar dogon lokaci ba, sannan ya kasance tana cikin yanayin da ake sako ƙwai biyu ko sama da haka a tare," in ji shi.
"Sannan na ƙarshe ya kasance dukkan ƙwan ne suka haɗu da maniyyin suka hayayyafa," in ji Usaquén.

Asalin hoton, Getty Images
Rayuwar sirri
A lokuta da dama, dama ƙwayaye da yawa ne suke fitowa, idan ɗaya ya fara hayayyafa, sauran sai su mutu a hankali.
Wannan ya ƙara bayyana abin da ya sa ba a cika samun yanayin ba, saboda dole ɗayan ƙwan ya fara hayayyafa kafin ya mutu.
Sannan cibiyar ɗakin karatun likitanci na Amurka ta bayyana cewa kowane ƙwai na rayuwa ne na aƙalla awa 24 bayan fita.
Sai dai Andrea Casas ta ƙara da cewa ba dole ba ne ya kasance ƙwayayen sun fita a lokaci guda.
"Wani lokacin, ƙwai ɗaya ne yake fara fita, sai bayan kwana biyu ko uku wani ya fito," in ji ta.
Wannan ya sa samun haɗuwa da hayayyafar ƙwayaye biyu a lokaci ɗaya ke wahalar gaske.
Sannan wani abu shi ne yawancin mutane ba su damuwa da gwajin gano ainihin iyaye, wanda hakan na cikin abubuwan da suka sa ba a cika samun matsalar ba.








