Buɗe mashigar Hormuz ba zai daidaita al'amura nan take ba - Starmer
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya yi gargaɗin cewa tattalin arzikin ƙasarsa ba ''zai koma daidai ba'', ko da an sake buɗe mashigar Hormuz.
Yayin wata hira da BBC, Mista Starmer ya ce halin da ake ciki yanzu na buƙatar sabbin salo, domin tunkarar matsalar tattalin arziki da aka riga aka samu sakamakon yaƙin.
Da aka tambaye game da yiwuwar samun hauhawar farashi sakamkon tashin farashin man fetur, firaministan ya ce gwamnati ba za ta kya hana aukuwar hakan ba.
''Muna fuskantar yaƙi har guda biyu'', kamar yadda ya bayyana.




