Wane zaɓi ya rage wa ADC da PDP bayan Kotun Ƙolin Najeriya?

Kotun Ƙoli

Asalin hoton, Supreme Court/ADC/PDP/Website

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu ne Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke hukunci na makomar shugabannin jam'iyyar PDP tsagin Kabiru Tanimu Turaki, da kuma shugabannin ADC tsagin David Mark.

A hukuncin, wanda mai shari'a Stepehen Adah ya sanar, ya bayyana cewa taron da PDP ta gudanar a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban 2025 a Ibadan rashin ɗa'a ne ga hukuncin babbar kotun tarayya da mai shari'a James Omotosho ya yanke inda ya dakatar da su daga gudanar da babban taron.

Kotun Ƙolin ta kuma soki ɓangaren Turaki game da zuwa kotun da ba ta da hurumi, a madadin zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

Saboda haka, kotun ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ta yanke na haramta taron PDPn a jihar Oyo.

Alƙalai uku cikin biyar ne suka amince da wannan hukuncin, "idan jam'iyya ta ji hukuncin da kotu ta yanke, ya zama wajibi ta yi amfani da shi," in ji alƙalin kotun.

Sauran alƙalan guda biyu, Mai shari'a Haruna Simon Samani da Mai shari'a sun ce harkokin shugabancin jam'iyya na jam'iyya ne.

A game da shari'ar jam'iyyar ADC, Kotun Ƙoli ta tabbatar da shugabancin tsagin David Mark na wucin-gadi, tare da watsi da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ta buƙaci kowa ya tsaya a matsayin da yake.

Wannan shari'ar na nufin kotun na ƙoli ta ba ɓangaren David Mark gaskiya a shari'ar kan shugabanci.

Sai dai kotun ta bayar da umarnin a koma babbar kotun tarayya a fara sauraron shari'ar da ke tsakanin Nafiu Bala da David Marka.

'Yanzu za a fara shari'ar ADC'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Audu Bulami Bukarti lauya ne mai zaman kansa a Birtaniya, ya ce akwai kuskure a kan yadda ake ruwaito shari'a da hukuncin da aka yanke game da shugabancin ADC.

''Abin da Kotun Ƙoli ta ce shi ne an janye umarni na ƙwarya-ƙwarya da aka bayar na dakatar da kowane ɓangare wanda da shi ne dama INEC take amfani wajen daina amincewa da shugabancin David Mark," in ji shi.

Bukarti ya ce da wannan shari'ar ta Kotun Ƙoli, za a iya cewa David Mark da tsaginsu sun samu nasara ta wani ɗan lokaci.

"Yanzu tsagin David Mark ya samu nasara ta ƙwarya-ƙwarya saboda INEC za ta ci gaba da kallon sa a matsayin shugaban ADC," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa asalin shari'ar ADC ma ba a fara ba.

Ya kuma ce asalin shari'ar ita ce wadda Nafiu Bala ya shigar, inda ya buƙaci kotu ta masa fassara ko David Mark da sauran waɗanda suka shiga jam'iyyar halastattun ƴan jam'iyya ne.

"Idan kuma halastattu ne, yana neman sanin ko hanyar da suka bi wajen zama shugabanni halastacciya ce," in ji Bulama.

Lauyan ya ce kafin a fara shari'ar ne Nafiu Bala ya nemi kotu ta bayar da umarni na wucin-gadin a daina kallon David Mark a matsayin shugaba, inda ya samu nasara.

"A shari'ar ce aka yanke hukuncin cewa kowa ya tsaya a inda yake. Wannn shari'ar ce ta kowa ya tsaya a inda yake aka yi har Kotun Ƙoli."

Bulama ya ce wannan hukuncin ne Kotun Ƙoli ta warware, "shi ya sa ta yi umarnin a kom babbar kotu domin cigaba da sauraron asalin shari'ar," in ji shi.

Me hukuncin kotun ƙoli ke nufi ga PDP?

Wannan hukuncin na nufin cewa shugaban jam'iyyar PDP ya koma tsagin Ministan Abuja, Nyesome Wike ke nan, wanda a yanzu yake ƙarƙashin shugabancin Abdulrahman Mohammed.

A watan Maris na shekarar 2026 ne tsagin ya gudanar da wani sabon babban taron, inda suka zaɓi Abdulrahma a matsayin shugaban jam'iyyar, da kuma Samuel Anyanwu a matsayin sakatare.

Aƙalla wakilai 2,000 daga jihohin Najeriya da Abuja suka taru a babban birnin ƙasar, inda suka amince da shugaban jam'iyyar a wani taro da suka yi a filin wasan Moshood Abiola.

Tun da farko, babbar kotun tarayya da kotun ɗaukaka ƙara sun yanke hukuncin cewa taron da aka zaɓi shugabancin tsagin Kabiru Turaki ba shi da inganci.

A game da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke, Barista Audu Bulama Bukarti ya ce shari'ar na nufin kotu ta lalata babban taron PDP da aka yi a Ibadan a shekarar da ta gabata.

"A taron ne aka zaɓi Kabiru Tanimu Turaki a matsayin sabon shugaba da sauran shugabanni. A doka tunda an rusa taron da aka zaɓe shi, shi ma an rusa shi. Ke nan daga yazu ba shi ba ne shugaban PDP," in ji Bulama.

Lauyan ya ce hujjoji biyu Kotun Ƙoli ta bayar wajen yanke hukuncin kamar haka:

  • Ɓangaren Tanimu Turaki bai yi zaɓukan shugabannin jihohi ba.
  • Ba a ba Sule Lamiɗo damar shiga zaɓen shugabancin jam'iyyar ba.

Zaɓin da ya rage wa Turaki

A game da ko wane mataki ya kamata tsagin Turakin ya ɗauka, Bulama Bukarti ya ce kasancewar daga yanzu INEC ba za ta amince da shi ba, zai fi kyau su koma su sake shiri domin a cewarsa, ko ƴantakara ya miƙa ba za a karɓa ba.

"Yanzu sai dai su koma su duba, idan akwai wata ƙofa da za su yi zaɓen jihohi, sai su yi, sannan su ba Sule Lamido dama sannan su yi sabon, idan suna da lokaci ke nan. Idan kuma babu lokaci, sai dai su shiga wata jam'iyyar."

Da ma dai ɓangaren na Tanimu Turaki sun gana da ƴan jam'iyyar ADC a jihar Oyo inda masu fashin baƙi suka hasaso afkuwar haɗin gwiwa tsakanin jam'iyyun da ke fuskantar matsala kusan irin ɗaya.