BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Jirgin ruwa ya ratsa ta mashigar Hormuz duk da barazanar Trump
Wannan shafi na kawo muku sahihan bayanai dangane da wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya
Me ya sa gwamnan Kano ke jan ƙafa kan naɗin mataimakinsa?
Yanzu an kwashe kusan mako uku tun bayan da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam ya sauka daga muƙaminsa bayan rikicin siyasa da ya turnuƙe sanadiyyar sauya sheƙar gwamnan jihar zuwa APC mai mulki a Najeriya.
Lokuta bakwai da manyan ƙungiyoyin Premier suka yi 'dakon teburi'
Yayin da Arsenal ke neman kore taken da ake yi mata na mai "dakon teburi", mun duba wasu lokuta a baya da manyan ƙungiyoyin Premier suka gaza kai bantensu bayan an kyautata musu zato.
Lokuta 13 da jiragen yaƙin Najeriya suka kai harin 'kuskure' kan fararen hula
Jiragen yaƙi na sojojin Najeriya sun kai hare-haren kuskure kamar yadda suke bayyana su a kan fararen hula har sau 12 a ciki da wajen Najeriya, a tsawon shekaru takwas, wani abu da masana ke cewa akwai rashin ƙwarewa.
Me ya sa ake caccakar shugaban INEC, Joash Amupitan?
"Ko Tinubu ya yarda kwallon mangoro ya huta da ƙuda ko kuma shi Amupitan ya ajiye aikin ya huta da sukar 'yan hamayya"
Me zai faru bayan gaza cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran?
Wakiliyar BBC Lyse Doucet ta ce sa'oi 24 sun yi kaɗan a yunƙurin ɗinke ɓarakar da ke tsakanin Iran da Amurka mai tarihin shekara 47.
'Ko su kashe mutum ko mutum ya kashe kansa': in ji wata da ta tsira daga hannun masu safarar kwaya
Gano wasu tarin takalma da sauran amfanin mutane a wani sansani na masu safarar kwayoyi a bara ya rikita Mexico tare da jan hankalin duniya. BBC ta tattauna da Sandra Romandia wata ‘yar jarida da ta tattauna da waɗanda suka tsira daga sansanin a littafinta mai suna The Truth They Tried to Hide at Rancho Izaguirre.
Abin da tarin gajiya ke yi wa fata – kuma me za ka yi a kai
Gajiya kan yi tasiri daban-daban, kama daga fitowar kuraje a fuska da kuma bushewar fata - hakan kuma na ƙara barazanar kamuwa da cutuka kamar su kyasfi da sauransu.
Luguden bam na jirgin yaƙi ya kashe gomman fararen hula a Borno da Yobe
Rahotonni daga jihohin Borno da Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani harin jirgin yaƙi ya kashe gomman mutane da suka je cin kasuwar Jilli da ke kan iyakar ƙananan hukumomin Gubio da Geidam a jihohin biyu.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 14 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 13 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 13 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 13 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Man City ta farfaɗo da damar lashe Premier League na bana
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Lahadi 12 zuwa Juma'a 18 ga watan Afrilun 2026.
Arsenal na neman ɓarar da garin Man U kan Jeremy Monga, Liverpool da Chelsea na son Kroupi
Newcastle na son Ugarte, Spurs da West Ham na zawarcin wani dan Barcelona, Liverpool da Chelsea na fafatawa kan Kroupi.
Sakamakon wasannin ƙarshen mako: Arsenal da Real sun yi tuntuɓe
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Talata 7, zuwa Asabar 11 ga watan Afrilun 2026.
Wane mai tsaron raga ne ya fi tashe a wannan lokaci?
David Raya da Manuel Neuer sun nuna hazaƙa a wasannin gasar Champions League da ƙungiyoyinsu suka buga a baya-bayan nan - to amma ko suna cikin mafiya hazaƙa a duniya?
Man U na neman Anderson, Liverpool ta samo magajin Salah
Arsenal da Manchester City sun shiga takarar neman dan wasan baya na Real Betis, Oscar Mingueza, Real Madrid na zawarcin Nico Schlotterbeck.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Za mu toshe mashigar Hormuz - Trump
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Lahadi 12/04/2026
Yadda mu'amala da mutane ke inganta kwakwalwarku da saka ku farin ciki
Shafe lokaci tare da mutane yana da alfanu sosai ga lafiyar kwakwalwa, in ji likitan kula da kwakwalwa, Ben Rein.
Me ya sa Amurka da Iran suka gaza cimma matsaya a Pakistan?
Babu dai tabbacin ko za a ƙara wani yunƙuri a cikin makonni biyun tsagaita wuta da aka ƙula, ko kuma akwai shirin gudanar da wani zaman na daban. Bayan tashi taron tattaunawa a Pakistan ba tare da fahimtar juna ba.
'Na san an samu kuskure': Iyalan da suka haihu da maniyyin da ba nasu ba
Wasu iyalai bakwai sun yi imanin cewa an yi amfani da maniyyi ko ƙwayayen da ba nasu ba yayin aikin dashen ɗantayi.
Bayanin da Melania Trump ta yi kan binciken Epstein ya dawo da hannun agogo baya
Ana ta raɗe-raɗin cewa wani kan-da-garki ne ta yi domin ana sa ran wasu sabbin bayanan da za su fito masu alaƙa da Epstein, sai ta fake da cewa tun tuni ta yi bayani duk mai son ji daga gareta ya tuntubi lauyanta.
Iran ta ƙaryata cewa jiragen Amurka sun ratsa ta mashigar Hormuz
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya, Asabar 11/04/2026
'Burinmu ƴaƴa mata su yi karatu su zama likitoci da ma'aikatan asibiti'
Gidauniyar bunƙasa ilimin ƴaƴa mata a garin Zaria mai suna Center for Girls' Child Education ta ce ta tashi tsaye wajen taimaka wa mata wajen kawar da ƙalubalen da ke hana su samun ilimin.
An sace mutane 1,100 cikin watanni uku a Najeriya - Amnesty
Amnesty International ta ce dole ne gwamnain shugaba Bola Tinubu ta gaggauta ɗaukar matakan magance wannan matsala da ke ƙara muni, musamman a tsakanin al'ummar karkara da mazauna sansanonin ƴan gudun hijira.
Mutane 5 da ke wakiltar Amurka da Iran a tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Iran
Yayin da wakilan Amurka da Iran suka isa birnin Islamabad domin tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Iran da Amurka, hankula sun koma kan su wane ne wakilan ɓangarorin biyu.
Su wane ne masu ɗaukar nauyin ta'adanci a Najeriya?
A baya dai Najeriya ta sanar da matakin ladabtarwa kan wasu mutanen da kamfanoni, kamar yadda kwamitin tsaro na majalisar Dinkin Duniya ya gindaya, kuma cikin matakin da aka ɗauka harda na rufe asusun ajiyar su da kuma taƙaita tafiye-tafiye gare su.
Tsagaita wuta: Wurare 5 da sharuɗɗan Iran suka ci karo da na Amurka
Duka ɓangarorin biyu sun gabatar da sharuɗɗan kawo ƙarshen da aka shafe kimanin kwana 40 ana gwabzawa.
Martanin da Abba Kabir ya mayar wa Kwankwaso
A karon farko gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya mayar da martani ga tsohon ubagidansa na siyasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tun bayan raba gari da mutanen guda biyu suka yi.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.
































































