Me ya sa wasu ƙasashe ke fargaba game da sabbin sauye-sauyen WhatsApp?

Asalin hoton, Getty Images
Somaliya ta zama ƙasa ta baya-bayan nan da ta shiga jerin ƙasashen da ke nuna fargaba da shakku kan sabbin sauye-sauyen da kamfanin Meta ya ɓullo da su a dandalinsa na WhatsApp.
Ƙasar wadda ke gabashin Afirka na daga cikin ƙasashen da suka dogara sosai kan WhatsApp domin sadarwa.
Bayanai sun ce ƙasar ta yi watsi da sabbin sauye-sauyen ne saboda zargin cewa za su iya haifar da laifuka da tsaron intanet.
Wani jami'i a hukumar sadarwar ƙasa, da ya zanta da BBC ya ce Somaliya na buƙatar kamfanin ya tattauna da mutane kafin aiwatar da sauye-sauyen.
A farkon watan nan ne WhatsApp ya fara bai wa masu amfani da shi damar ajiye sunan da suke so su riƙa amfani da shi a dandalin, sauyin da ake ganin zai fara aiki nan gaba cikin wannan shekara.
Dandalin ya ce ya ɓullo da sauyin ne domin bayar da dama ga masu amfani da shi kusan biliyan uku su yi hulɗa ba tare da musayar lambar waya ba.
A makon da ya gabata ne, Indiya ta buƙaci kamfanin na Meta ya jinkirta sauye-sauyen, saboda fargabar hakan zai haifar da ƙaruwar zamba da intanet.
India na da masu amfani da WhatsApp fiye da miliyan 600, lamarin da ya sa ƙasar ta zama wadda ta fi kowace ƙasa amfani da dandalin.
A nata ɓangare Somaliya ba ta bayyana dalilanta na watsi da matakin ba, amma wasu ƙwararru sun danganta hakan da dalilai na tsaro, musamman ayyukan ƴanta'adda da masu laifukan intanet.
Ƙungiyar mayaƙan al-Shabab ta ɗauki kusan shekara 20, tana shirya hare-hare a ciki da wajen ƙasar.
Wane sauyi WhatsApp ya kawo?

Asalin hoton, WhatsApp
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
WhatsApp na shirin bai wa mutane damar yin magana da juna ba tare da bayyanar lambobin wayoyinsu ba, ta hanyar musayar sunayen da za su riƙa amfani da shafin.
Kamfanin ya ce wannan fasalin zai kasance ga masu amfani a faɗin duniya cikin watanni masu zuwa, wanda zai amfani kusan mutum biliyan uku da ke da suka yi rajista da shafin.
Tun daga wannan makon, masu amfani za su iya fara zaɓar da adana suna na musamman da za su riƙa amfani da shi a manhajar, duk da cewa ba wajibi ba ne su yi hakan.
Kamfanin ya ce mutane za su iya cire ko kuma sauya sunayensu a kowane lokaci.
Da zarar an fara amfani da wannan fasalin gaba ɗaya, masu amfani da WhatsApp za su iya haɗuwa da juna ta hanyar musayar sunayensu kawai, ba tare da sun ba juna lambobin waya ba.
Duk da haka, za a ci gaba da samun hanyoyin toshe mutum ko kai rahoton saƙonnin da ba a so.
Za a iyakance tsawon sunan zuwa haruffa 35, kuma ba za a sanya ƙa'idoji masu yawa ba.
Sai dai wasu sunayen manyan masu riƙe da muƙamai da fitattun mutane, waɗanda ba za a bari wasu su yi amfani da su ba.
Mene ne hikimar sauye-sauyen?

Asalin hoton, Getty Images
Akwai yiwuwar WhatsApp za ta taƙaita yawan mutanen da za su iya amfani da wasu sunaye a dandalin. Misali kamar na Donald Trump.
Kamfanin Meta ya bayyana matakin da ƙarfafa sirrin masu amfani da shafin.
Alice Newton-Rex shugabar tsare-tsare ta WhatsApp ta ce ta ji daga mafi yawan masu amfani da dandanlin cewa ba sa son yaɗa lambobinsu ga wasu, musamman waɗanda ba su sani ba sosai.
Ta ce tana fatan sabon sauyin ''zai bai wa masu amfani da manhajar damar zaɓin abin da suke so'' game da dandalin.
Wasu masana na cewa za a iya samun ƙaruwar hatsari daga sabon sauyin.
"Haɗarin da ke tattare da wannan shi ne, mutumin da ya mallaki sunan zai iya ɗauka cewa ba za a gano shi da sauƙi ba, don haka zai iya yin komai, babu wani abu da zai hana shi," in ji Said Haji Yasin, ƙwararre kan tsaron intanet wanda ya daɗe yana bibiyar wannan batu sosai.
Ya ƙara da cewa Meta bai tuntuɓi gwamnatocin ƙasashen duniya ba, a lokacin bijiro da sabbin sauye-sauyen, amma kuma yanzu yana son jin ta bakin ƙasashen duniya kan batun.











