Shin da gaske ne ana fifita Argentina a Gasar Cin Kofin Duniya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Dale Johnson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Football issues correspondent
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Argentina na yin duk abin da za ta iya domin ganin ta kare kambun ta na gasar cin kofin duniya - kuma dole ne ya sa ta yin hakan.
Bayan an yi tsammanin za su doke Cape Verde da Masar a zagayen kifa-ɗaya-ƙwala, sai da La Albiceleste ta yi aiki tuƙuru kafin ta ti nasara da ci 3-2.
Amma nasarar da ta samu a kan Masar ta zo da ce-ce-ku-ce yayin da ƙasar ta Afirka ta nemi Fifa ta kori alƙalan wasan da suka gudanar da wasan da aka yi waje da ita a zagayen ƴan 16 na gasar bana.
Masar ta yi zargin nuna son kai ga Argentina da kuma nuna son kai ga fitaccen ɗan wasanta, Lionel Messi.
Bayan wasan, koci Hossam Hassan ya ce an "yi wa Masar rashin adalci" kuma "ba a kyautata mata ba".
Hassan ya ci gaba da zargin Fifa da nuna son kai.
"Wataƙila suna son mai riƙe da kambun gasar ta ci gaba da kasancewa a gasar. Wataƙila suna son Messi ya ci gaba da fafatawa a gasar ta bana," in ji shi.
BBC Sport ta bincika ko akwai kamshin gaskiya a cikin zarge-zargen da ake yi na cewa ana shirya komai don Argentina ta yi nasara.
Ko Masar na da hujjar yin ƙorafi?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Za a iya fahimtar dalilin da ya sa Masar za ta ji takaici sosai bayan an doke ta da ci 3-2 a ranar Talata.
Ƴan wasan na Afirka sun jagoranci wasan da ci 2-0 inda ya rage saura mintuna 11 a kammala wasan, kuma ta na daf da buga wasan daf da na kusa da ƙarshe a karon farko a tarihinta.
Sai dai abin ya ci tura yayin da Argentina ta farfaɗo ta farke ƙwallo biyu ta kuma ci na uku a cikin ƙarin lokaci.
Masar ta yi iƙirarin akwai wani alamar tambaya kan yadda wasan ya gudana. Ta ɗaura alhakin ficewarta daga gasar kan abin da ta kira "kuskuren alƙalan wasa" daga alƙalin wasa ɗan ƙasar Faransa Francois Letxier da tawagarsa.
An soke ƙwallon da Masar ta ci bayan da na'urar VAR ta shiga tsakani.
Ta kuma yi iƙirarin cewa ya kamata a hana ƙwallo na uku da Argentina ta ci, kuma aka ba ta bugun fanareti a madadin hakan.
Mostafa Zico ne ya zura ƙwallon da aka soke bayan an hukunta Marwan Atia saboda taka ƙafar Lisandro Martinez.
An yi ta cece-kuce, amma suna kan gaba da ci 1-0 kuma sun ƙara zura ƙwallo ta biyu bayan mintuna tara. Ba za a iya tabbatar da cewa sakamakon wasan zai sauya ba da ba a soke ƙwallon da Zico ya ci ba.
Masar ta yi imanin cewa akwai bugun fanareti guda biyu da ya kamata a ba ta kafin Enzo Fernandez ya farke ƙwallon.
Hamdi Fathy ya faɗi kasa yana mai iƙirarin cewa Alexis Mac Allister ne ya riƙe shi, wanda ba a iya tabbatar da hakan ba, yayin da Mohamed Salah ya ce Julian Alvarez ya taka masa ƙafarsa.
Akwai wasu kamanceceniya tsakanin abubuwan da suka faru da Martinez da kuma na Salah, inda aka samu harɗeswar ƙafafuwan ƴan wasa biyu, amma bai kai wadda za a iya bayar da bugun fenariti ba.
Da Salah ya kasance a wajen da'itra ta 18 ne da za a iya duba yiwuwar soke ƙwallon . VAR za ta yanke hukunci kan ƙeta ne kawai - kamar yadda aka yi wa Martinez - maimakon bugun fanareti.
Da gaske ne lamarin na da sarƙaƙiya? Amma ba hujja ce ta makarkashiyar goyon bayan Messi ba.
An ƙi bai wa Messi jan kati kuma daga baya ya ci ƙwallo biyar

Asalin hoton, Getty Images
Idan aka tuna farkon gasar lokacin da ake ganin ya kamata a bai wa Messi jan kati.
Messi bai ma sami katin gargaɗi ba bayan ƙetar da ya yi wa kyaftin ɗin Algeria Aissa Mandi.
Sannan, a makon da ya gabata, an ga ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka faru a gasar cin kofin duniya.
An kori Folarin Balogun a lokacin da aka duba VAR a wasansu da Bosnia a wni yanayi makamanci wannan yanayi.
Ana kyautata zaton Amurka ta bayar da wannan misalina lokacin da take fafutukar ganin an janye jan katin da aka bai wa Balogun.
Da an kori Messi, da ba zai zura ƙwallayensa na biyu da na uku a ragar Algeria ba, haka kuma ba zai zura kwallaye biyu a ragar Austria ba, domin da an dakatar da shi – sai dai idan Fifa ta yanke shawarar amfani da doka ta 27 kamar yadda ta yi wa Balogun.
Da luma Messi bai samu damar buga wasan rukuni na ƙarshe da Jordan ba, lokacin da ya sake zura ƙwallo a raga.
Hakan da ya kwashe biyar daga cikin ƙwallo takwas da ya ci a gasar.
Shin wannan nuna son kai ne ga Messi?
Ko alƙalan wasa ba sa bai wa Argentina katin gargaɗi kamar yadda ake bai wa wasu?
Wasan kwata-fainal yana tattare da haɗari. Ƴan wasa goma sha bakwai suna da fuskantar dakatarwa idan suka samu katin gargaɗi a wasanninsu.
Babu wata babbar barazana ga Argentina, inda Gonzalo Montiel ne kawai ke cikin haɗarin rasa wasan kusa da na ƙarshe da Ingila ko Norway.
Kocin Ingila Thomas Tuchel yana da ƴan wasa huɗu da ke cikin wannan haɗari, kuma sun haɗa da manyan ƴan wasa Jude Bellingham da Declan Rice.
Norway, wadda ta sami mafi ƙarancin katin gargaɗi, tana da Antonio Nusa ne kawai da ke fuskantar wannan matsalar.
Don tantance wannan, kuna buƙatar la'akari da yadda ƙungiya ta kasance mai buga 'ƙazamin wasa'. Shin adadin katin gargaɗin da suka samu ya yi daidaiu da yawan ƙetar da suka yi?
Argentina ta sami kati bayan ƙeta guda 19.7.
Ƙungiyoyi uku ne kawai - Jamhuriyar Czech (37.0), Norway (24.0) da Tunisia (27.0) - suke da mafi girman kason kati idan aka kwatanta da yawan ƙeta.
Daga cikin ƙungiyoyin da har yanzu ke gasar, an fi yi wa Ingila mummunan aiki, inda ta ke samu katin gargaɗi bayan kowane ƙeta guda 7.7.
Argentina ta yi ƙeta fiye da Ingila, duk da haka ta sami adadin katin da aka ba ta. Wannan na iya nuna cewa ana yi wa Argentina kyakkyawan zato idan aka kwatanta da adadin laifukan ƙeta da ta aikata.
Yadda Infantino ya tabbatar da cewa Messi ya buga wasa a baya

Asalin hoton, Getty Images
Da alama shugaban Fifa Gianni Infantino yana son ganin Messi a gasan da Fifa ke shiryawa.
A ɗauki gasar cin kofin duniya na ƙungiyoyi na farko da aka yi a Amurka a bara.
An ɗan samu jinkiri kafin a tabbatar da wace ƙungiya ce za ta wakilci ƙasar da ta karɓi baƙuncin gasar.
Tabbas ya kamata ya zama zakarun 2025? Saboda ai gasa ce ta zakarun gasannin ƙwallon ƙafa.
Kusa, amma ba sosai ba.
Inter Miami ta lashe gasar 'MLS Supporters' Shield' ta 2024, wadda ake bai wa ƙungiyar da ke da mafi yawan maki.
Sai dai LA Galaxy ce ta zama zakarar gasar MLS bayan ta lashe wasan ƙarshe na gasar.
Amma duk da haka an zaɓi Inter Miami a gasar cin kofin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa ta duniya..
Hakan ya bai wa Messi damar buga wasan farko, a filin wasa na Hard Rock na Inter Miami, da Al Ahly.
Jadawalin wasanni ya kyautatawa Argentina
Fifa ta yi ƙaramin sauyi mai mahimmanci a yadda ake shirya jadawalin wasanni na gasar cin kofin duniya a watan Disamba.
An fitar da ƙasashe huɗu da ke kan gaba a jerin ƙasashen duniya da suka haɗa da Faransa da Argentina da Spain da Ingila zuwa ɓangarori daban-daban.
Idan da a ce waɗannan ƙasashen za su yi nasara a rukuninsu -ba za su iya haɗuwa ba har sai zuwa wasan kusa da na ƙarshe.
Faransa da Spain dai suna ɓangvare guda kum za su haɗu a wasan kusa da na ƙarshe, yayin da Argentina da Ingila ke ɓangare guda kuma za su iya haɗuwa da juna a wannan matakin.
Manufar ita ce a iyakance damar samun haɗuwar manyan tawagogi tun a farkon gasar.
Amma, ya danganta da yadda aka ƙarƙare matakin rukuni na gasar, hakanan yana ba wa waɗannan ƙasashe hanya samun hanuya mai sauƙi na kai wa wasan ƙarshe.
A zagaye biyu na farko a matakin kifa-ɗaya-ƙwala , an yi karawa biyu ne kawai na manyan ƙasashe 10 na duniya – Netherlands da Morocco da Spain da Portugal.
Alamu na nuna cewa Argentina ta samu hanya mafi sauƙi, duk da cewa kawai ta doke Cape Verde (na 67 a duniya) da Masar (29) 3-2.
A zagayen kwata fainal za ta kara da Switzerland (19).
Argentina tana yawan samun bugun fenariti
Lokacin da Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya a 2022 ta kafa sabon tarihi a gasar.
Fenareti guda biyar da aka ba ta shi ne mafi yawa da kowace tawaga ta taɓa samu a gasa ɗaya.
A shekara ta 2026, ta sake kasancewa kan gaba jerin ƙasashen da aka bai wa bugun fenariti - ko da yake Messi ya ɓarar da biyu daga cikinsu, a karawar da suka yi da Austria da kuma wanda suka yi da Masar.
An bai wa Ingila da Switzerland fenariti guda biyu, yayin da Belgium, Faransa da Norway a ke da guda ɗaya kacal.











