KACRAN ta buƙaci Tinubu ya tabbatar da aikin ma'aikatar bunƙasa kiwo

Asalin hoton, KACRAN
Ƙungiyar makiyaya Kulen Allah Cattle Rearers Association of Nigeria, KACRAN buƙaci shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya dage wajen ganin ma'aikatar bunƙasa harkokin kiwo ta gudanar da ayyukanta kamar yadda aka tsara a farkon ƙirƙiro ta.
Ƙungiyar ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da shugabanta na ƙasa Khalil Mohd Bello ya fitar, inda a ciki ya yaba wa jajircewar shugaban wajen nuna muhimmancin bunƙasa harkar kiwo a Najeriya ta hanyar kafa kwamitin na musamman a ƙarƙashin jagorancinsa, tare da Farfesa Attahiru Jega a matsayin mataimakin shugaban kwamitin.
"Fiye da shekara 60 makiyayan Najeriya sun kasance suna kokawa kan watsi da su, da cin zarafi da kuma nuna musu wariya daga gwamnatocin da suka gabata. Saboda haka, kafa wannan kwamitin da samar da ma'aikatar bunƙasa kiwo abin farin ciki ne ga miliyoyin makiyaya a faɗin ƙasar," in ji shi, sannan ya ya yaba da naɗa Alhaji Idi Mukhtar Maiha a matsayin minista.
Sai dai ya ce KACRAN, "wadda ta kasance cikin ƙungiyoyin da suka yi fafutukar kafa ma'aikatar kiwo, tana tunatar da shugaban ƙasa cewa har yanzu kwamitin na musamman da ma ma'aikatar ba su da cikakken ƙarfin gudanar da aikinsu, sakamakon ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa da kuma rashin cikakken tsarin aiki."
Ya ƙara da cewa idan ma'aikatar ta fara cikakken aiki, za a samu abinci, za a samar da ayyuka ga matasa, sannan za a rage rikicin makiyaya da manoma a ƙasar.




























