BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Har yanzu tsugune ba ta ƙare ba a yaƙin Iran - Netanyahu
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 19/04/2026
Da gaske hasken waya na haifar da matsala ga bacci?
Yadda rage haske da maraice ya ke taimakawa wajen samun bacci cikin sauƙi
Wane ne fir'aunan da ya yi zamani da annabi Musa?
Littattafan addini na baya su ma ba su ambato sunan wannan "Fir'aunan" ba, wanda ya mulki Misra kuma ya yi rayuwa da Annabi Musa.
Yadda zargin sakaci ke janyo salwantar rayuka a asibitin Jami'ar Maiduguri
Jama'a a Najeriya na ci gaba da korafi kan zargin sakaci da aiki, da rashin kyakkyawar kulawar da ta dace ga majinyata a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri a jihar Barno, al'amarin da ake zargin yana jefa majinyatan cikin mawuyacin hali, har ma da kai wasunsu ga rasa rayukansu.
Wurare 5 da suke nuna tarihin cinikin bayi a Afirka
Tsananin azabar da aka sha lokacin cinikin bayi, musamman a yankunan baƙar fata na ƙara tabbatar da yadda bauta ta taka muhimmiyar rawa a tarihin nahiyar Afirka.
Wankan safe ko na dare: Wanne ya fi amfani?
Wanke muhimman wurare a jiki tare da yin wanka na wasu kwanaki a mako zai haifarwa da mutum rayuwa cikin ingantacciyar lafiya
Ba za mu buɗe Hormuz ba sai Amurka ta buɗe tashar ruwanmu - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Asabar 18/04/2026
Hanyoyin daidaita lokacin motsa jiki domin samun sakamako mafi kyau
Masu tashi da wuri, wato yan safe kenan ya kamata su motsa jiki da safe domin samun cikakken amfani, yayin da wadanda suke yan dare ne ya fi dacewa su motsa jiki da yamma, in ji masu bincike.
Yadda wasu kurame suka gudanar da aikin Hajji
A kowace shekara, miliyoyin mutane suna zuwa Saudiyya domin yin Umrah, wato ibadar da Musulmi ke iya yi a kowane lokaci, sabanin Hajji wanda wajibi ne sau ɗaya a rayuwa kuma yana gudana a watan karshe na kalandar Musulunci.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 20 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 19 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 19 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 19 Aprilu 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Haaland ya ci Arsenal karo na huɗu a jere a Premier League
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Lahadi 19 zuwa Juma'a 24 ga watan Afrilun 2026.
Madrid na son dawo da Mourinho, Onyeka zai koma Conventry
Real Madrid na tunanin nada tsohon kocinta Jose Mourinho wanda ke jagorantar Benfica
Liverpool za ta Fafata da Man U kan Wharton, Newcastle za ta sayar da Wissa
Liverpool ta bi sahun Manchester United a yunkurin dauko dan wasan Ingila Adam Wharton daga Crystal Palace, wadda ke son akalla fam miliyan 80 kan dan wasan .
Caicedo ya tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a Chelsea
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Lahadi 12 zuwa Juma'a 18 ga watan Afrilun 2026.
Babu tabbacin Rashford zai ci gaba da zama a Barca, Gardon na son komawa Munich
Babu tabbas a makomar Marcus Rashford a Barcelona, Anthony Gordon na duba makomarsa yayin da Bayern Munich ke harin ɗan wasan, yayin da Manchester City ke son ɗaukar Eduardo Conceicao, plus more.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Da gaske matsalar tsaro ta fi ƙaruwa gabanin zaɓe a Najeriya?
Ƴan Najeriya na ta muhawara kan kalaman da shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Godswill Akpabio ya yi cikin wannan mako game da alaƙar matsalar tsaro da zaɓen ƙasar na 2027 da ke tafe.
Ina ce mashigar Malacca da ka iya haɗa Amurka da China yaƙi?
Kafin cimma yarjejeniyar da ta sa ƙasar Iran buɗe mashigar Hormuz, ɗaya daga cikin manyan hanyoyin ruwa a duniya, hankalin duniya ya koma kan wata muhimmiyar mashigar.
''Ya kamata jama'a su rungumi tubabbun 'yan tada kayar baya''
Yayin da mutane da dama ke nuna fargabata kan mu'amala da tubabbun yan tada kayar bayan nan sama da 700 da gwamnatin Najeriya ta saki, wasu masana halayyar dan adam sun yi gargadin rashin jan su a jiki, na iya janyo su sake komawa ruwa.
Ina ce mashigar Hormuz da ƙasar Iran ta buɗe?
Duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana samun nasara sosai a yaƙin, wani abu da ake ganin tamkar ya tsaya masa a wuya shi ne batun datse mashigar ta Hormuz.
Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2026 na naira tiriliyan 68
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ƙasar na 2026 da yawansa ya kai naira tiriliyan 68.32.
Illoli 7 da zafin rana ke yi wa ƙananan yara da yadda za a kauce musu
Yara ƙanana ba su da cikakken ƙarfin jure zafi kamar manya. Jikinsu ba ya iya daidaita zafin jiki yadda ya kamata, lamarin da ke sa su cikin saurin kamuwa da matsalolin da ke tattare da zafi. kamar yadda wata likitar yara Dr. Amina Yusuf ta shaida wa BBC.
'Tun da Buhari ya yi shekara takwas, dole Tinubu ya yi wa'adi biyu'
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara na musamman, Bayo Onanuga ya ce: ''Abin da kawai Atiku ya kamata ya yi shi ne ya manta da batun sake yin takara, saboda har yanzu lokaci ne na Kudu a zaben 2027.''
Me zai biyo baya a rikicin Amurka da Iran? Abu huɗu da za su iya faruwa
Shin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka za ta dore kuma diflomasiyya za ta ci gaba?
Me sabuwar dokar zaɓen Najeriya ta ce kan yin takara da takardun bogi?
Ɗaya daga cikin dokokin da ke ta da ƙura ita ce wadda ta hana a ƙwace wa ƴan takarar da suka ci zaɓe da takardar bogi, sannan ta tanadi hukunci ga wanda ya kai su ƙara bai yi nasara ba.
Iran ta amince ba za ta mallaki makamin nukiliya ba - Trump
Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran muhimman labarai a sassan duniya na 16/04/2026.
Wakilan Amurka za su koma Pakistan don ci gaba da tattaunawa da Iran
Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran muhimman labarai a sassan duniya na ranar 17/04/2026
Abin da muka sani game da tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Lebanon
Yarjejeniyar ta tsawon tsagaita wutar ta tsawon kwanaki 10 ce, amma da yiwuwar a tsawaita idan an samu fahimtar juna a tattaunawar da ake yi.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.

































































