Dars Hausa: BBC za ta ƙaddamar da shirin ilmantar da yaran da ba sa zuwa makaranta

Ma'aikatan Dars
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

BBC World Service ta faɗaɗa shirin ilmantarwa na "Dars" da ya samu lambar yabo zuwa harshen Hausa domin yara a Yammacin Afrika.

Za a gabatar da darussa ga yara a talabijin da rediyo da kuma kafofin sada zumunta na intanet da suka hada da Youtube da Facebook da X da Instagram da kuma Tiktok.

Dars Hausa, wanda sashen Hausa na BBC zai ƙaddamar, shiri ne da zai yi ƙoƙarin bayar da gudunmawa wajen magance ƙalubalen bukatar gaggawa ta ilimi a yankin, ta hanyar isar da darussa ga yara 'yan shekara 11 zuwa 16 daga cikin ingantattun kayan koyarwa na BBC.

Najeriya na cikin ƙasashen duniya da ke da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewa kusan yara miliyan 19 ne ba sa samun ilimi.

Barazanar ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da kuma fargabar satar ɗalibai ne suka yi tasiri wajen hana yara zuwa makaranta.

A arewacin Najeriya, shekarun da aka shafe ana rikici da gudun hijira da rashin tsaro sun tilasta wa miliyoyin mutane barin gidajensu, kuma sun ƙunshi dimbin yara wanda hakan ya kawo cikas ga ci gaba da karatunsu.

Samun damar zuwa makaranta ga yawancin yaran da aka raba da gidajensu wani babban ƙalubale ne, lamarin da ya haifar da matuƙar buƙatar samar da wasu hanyoyin samun ilimi na daban.

Mene ne shirin Dars na BBC?

Dars da ke nufin "Darasi" zai samar da darussa a fannoni daban-daban da suka haɗa da Inglishi da Lissafi da Kimiyya cikin harshen Hausa, tare da ƙarin darussa kan lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma labarai na ƙarfafa guiwa.

Za a ƙaddamar da shirin a ranar 17 ga Nuwamban 2026.

An fara ƙaddamar da Dars a shekarar 2023 a harsunan Pashto da Dari domin ba yaran Afghanistan da aka hana zuwa makaranta damar ci gaba da samun ilimi. Sannan aka ƙaddamar da Dars Arabic a watan Fabrairun 2025.

Babbar Daraktar BBC World Service, Fiona Crack, ta ce: "Ilimi hakki ne ga kowa, amma har yanzu shiga aji babban ƙalubale ne ga yara da rikici ya raba da gidajensu.

An tsara Dars Hausa ne domin isar da ingantaccen ilimi mai jan hankali kai tsaye ga yara masu magana da Hausa da ke fuskantar ƙalubalen samun ilimi, baya ga darussan Dars da ake da su a harsunan Pashto, Dari da Larabci."

Su wane ne masu gabatar da shirin?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Za a gabatar da shirin ne a ofishin BBC Hausa da ke Abuja, ƙarkashin jagorancin Awwal Ahmad Janyau, kuma masu gabatar da shirin sun hada da...

  • Aisha Babangida

Ƙwararriyar ƴarjarida ce mai samar da labarai na bidiyo da rahotanni a rediyo da rubutu a intanet da kuma a shafukan sada zumunta.

Aisha yar asalin jihar Kano ce kuma ta fara aikin jarida a Gidan Radiyo da Talabijin na Jigawa , sannan ta yi aiki da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) da Trust TV kafin ta fara aiki da sashen Hausa na BBC a 2023, inda take rubuta labarai da yin rahotanni na bidiyo a Hausa da Inglishi.

  • Ahmad Kabo Idris

Ƙwararren ɗanjarida ne da ke da gogewa wajen gabatar da shirye-shirye da karanta labarai da kuma fassara.

Ya yi aiki a bangaren rediyo da talabijin da kuma kafofin sadarwa na intanet. Dan asalin jihar Kano ne amma yana zama a Abuja.

Ahmad ya yi aiki a matsayin ɗanjarida mai gabatar da labarai da edita mai yin fassara a kafofin yaɗa labarai da suka haɗa da Arewa Radio da Freedom Radio a Kano kafin ya fara aiki da BBC, inda ya yi rahotanni da dama a fannin tsaro da lafiya da siyasa da kuma zamantakewa.

  • Abdulrahman Salihu

Matashin danjarida ne da ke samar da labarai cikin bidiyo a kafofin sada zumunta. Ya yi aiki a matsayin mai hada shiri a rediyo da talabijin.

Ayyukansa sun fi mayar da hankali kan aikin jarida na hidimar jama'a da kyautata rayuwarsu ta hanyar shirye-shirye a kafafen yada labarai da fito da al'amuran da suka shafi rayuwar jama'a ta yau da kullum.

Abdulrahman na amfani da gogewarsa a aikin jarida wajen ƙirƙirar abubuwan ilimantarwa masu jan hankali ga yara da matasa, domin tallafa wa manufar shirin Dars na BBC samar da ilimi cikin sauƙi ga yara masu magana da harshen Hausa.

  • Awwal Ahmad Janyau

Babban ɗanjarida ne kuma shi ne shugaban shirin Dars Hausa, ya shafe shekara 19 yana aikin jarida a kafofin yada labarai na ƙasashen waje kuma yana da gogewa a fannin yada labarai a intanet da samar da shirye-shirye da kuma shugabanci.

Awwal ya fara aiki da BBC a 2017 kuma ya yi aiki na jagorancin hadawa da shirya labarai da kuma karfafa hanyoyin samar dalabarai masu armashi a bangaren rediyo da kuma kafofin sada zumunta na intanet.

BBC Hausa za ta rika watsa shirin Dars Hausa a rediyo duk ranar Lahadi da ƙarfe 6:30 na safe agogon Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi wato 05:30 agogon GMT da Ghana.

Za a maimaita da ƙarfe 7:30 na yamma agoyon Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi wato 7:30 agogon GMT da Ghana.

Sannan za a samu shirin a shafukan BBC Hausa na YouTube, Facebook, X, Instagram da TikTok.

Za a iya kallon cikakkken shirin a Shafin BBC Hausa na YouTube. Sannan masu saurare za su iya sauraren shirin Dars Hausa a tasoshin FM abokan huldar BBC.