Premier League 'kakar korar kociyoyi' - wa ye zai fara rasa aikinsa a gasar?

Asalin hoton, Getty Images
Kociyoyin Premier League ku yi hattara
Wannan ba shi ne irin labarin da kocin Manchester United Michael Carrick zai so ya karanta ba, musamman yayin da matsin lamba ke karawa kan makomarsa bayan kunyar da kungiyar ta sha a hannun Como a gasar Champions League ranar Laraba, domin lokacin korar kociyoyi na gab da farawa.
Sai dai ba shi kadai ba ne yake cikin fargabar abin da zai iya biyo baya kan akinsa.
A kakar wasan da ta gabata, kociyoyin Premier League ko kuma manyan masu horaswa kamar yadda akasarinsu ake kiransu a yanzu, da suka bar mukamansu sun yi matsakaicin kwanaki 310 kacal a kan aikinsu.
Shin wata 10 sun isa ga koci ya aiwatar da abin da kungiya take bukata, daga ciki har ya dauko 'yan wasan da yake bukata, su kuma taka rawar da ta da ce, kuma ya gina alaka da magoya baya?
A kakar 2025-26, kociya 11 aka kora daga aikinsu, yayin da kociyan Chelsea, Enzo Maresca ne kadai ya yi mjurabus don radin kansa.
Ya zuwa yanzu a wannan kakar wasan ta bana, dukkan kociyoyin kungiyoyin Premier League 20 suna kan mukamansu, babu wanda aka kora.
Amma yaushe ne ainihin abin da aka saba kira "lokacin korar kociyoyi" a Premier League? Kuma su waye ke cikin hadari a wannan mataki na farko na kakar wasan bana?
Yau she ne za a fara korar kociyoyin?
Wannan ba labari ne mai dadi ga kociyoyin da ke fuskantar matsin lamba da fara kakar bana ba.
Watan Nuwamba da Disamba su ne lokutan da aka fi yawan korar kociyoyi a tsakiyar kakar wasa, inda kusan kashi daya bisa uku na dukkan sauye-sauyen kociyoyi ke faruwa a wadannan watanni biyu kadai.
A cikin kakar wasanni 34 da aka kammala, ana iya ganin wani tsari a sarari inda shugabannin kungiyoyi ke zabar yin sauyi a lokacin hutun wasannin kasa da kasa na kaka, da kuma kafin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.
Haka kuma, wani muhimmin lokaci shi ne kafin bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta hunturu, wadda aka fara amfani da ita a Ingila a shekarar 2003.
A irin wadannan lokuta ne kungiyoyin ke yawan yanke hukuncin sauya koci domin ba sabon wanda zai zo damar tsara kungiyar da kuma dauko 'yan wasan da yake bukata a lokacin kasuwar cinikayya ta Janairu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wataƙila mafi rashin kyautawa da aka yi wa koci, shi ne korar Les Reed na Charlton Athletic a jajibirin Kirsimeti a shekarar 2006, bayan ya yi nasara a wasa ɗaya daga bakwai a lig da ya jagoranta, inda ya tara maki huɗu kacal.
Zaman Reed na kwanaki 40 shi ne mafi gajarta wa'adin kocin Premier League a kusan shekara ashirin, har sai da aka kori Sam Allardyce a 2022-23 wanda ya yi kwana 30 kacal a Leeds United, kafin ƙungiyar ta faɗi daga gasar.
Ange Postecoglou kuma ya yi kwana 39 kacal a matakin kociyan Nottingham Forest a bara.
Daga cikin fitattun kociyoyin da suka rasa aikinsu a watan Nuwamba akwai Roberto di Matteo na Chelsea a 2012, Mauricio Pochettino na Tottenham Hotspur a 2019 da kuma fitaccen tsohon ɗan wasan Manchester United Ole Gunnar Solskjaer a 2021.
Di Matteo ya jagoranci Chelsea zuwa lashe Kofin FA da kuma Champions League a wani abin mamaki a matsayin kocin riƙon kwarya na wata shida kacal kafin a naɗa shi cikakken koci, amma ya rasa aikinsa bayan kasa kare kofin zakarun Turai da ya dauka a matakin ana gwada shi.
Watan Disamba kuwa ya zama watan da José Mourinho ya rasa aiki sau biyu.
A shekarar 2015 dan kasar Portugal ya rasa aikinsa na horar da Chelsea, wadda ke rike da kofin Premier League a lokacin, bisa amincewar su raba gari a tsakaninsu, sannan a shekarar 2018 Manchester United ta kore shi daga aiki.
A yanzu kwanaki nawa kociyoyin ke yi kan mukami?
A kakar wasan da ta gabata, matsakaicin tsawon lokacin da kociyoyin da suke rasa mukamansu ya kama daga kwana 310, wanda shi ne na biyu mafi kankanta a tarihin Premier League.
A kakar 1994-95 kadai ce ta yi kasa da wannan lissafin, inda matsakaicin lokacin da koci ke yi a kan aiki shi ne kwana 154.
A tsawon shekaru, ana samun dangantaka na yin tsami tsakanin shugabannin kungiya da masu horarwa tana karuwa ko raguwa lokaci zuwa lokaci, inda aka samu karancin korar kociyoyi sosai a kakar 1995-96.
A baya-bayan nan kuma lokacin da aka yi mai tsawo ba tare da korar koci ba shi ne a 2021-22, koda yake an danganta lokacin da zamanin cutar korona, wadda ta sa kungiyoyi suka ci gaba da aiki da kociyoyin koda ba sa taka rawar gani, domin duniya gabaki daya ba lafiya ana ta neman yadda za a samu sauki.
Sai dai kuma tun lokacin da abubuwa suka komai daidai, sai hakuri ya ragu tsakanin shugabannin kungiyoyi wajen sallamar koci, har ma ya zama dan karamin lokaci sai ka ji an sallami koci duk da kasa bashi lokacin da ya da ce.
An kori Ange Postecoglou daga Nottingham Forest a yan kwani kadan da fara aiki, haka kuma Tottenham ta raga gari da Igor Tudor a kwana 44 a kan mukamin bayan wasa biyar da ya ja ragama a lig.
A wannan kakar ta bana adadin kungiya tara daga 20 sun fara da sabbin masu horar da tamaula, kuma biyar daga cikinsu suna mataki a kasan teburin Premier League, kenan za su fara fuskantar barazanar korar kenan.
Kungiyoyin kan yanke hukunci nan take duk lokacin da suke fuskantar barin gasar, duk da batun kasa sayo fitattun yan wasa da bai wa koci dama, sannan ga matsin lamba daga magoya baya da kuma kafafen sada zumunta.
Wane koci ne ke cikin damuwa kawo yanzu?
Ko da yake babu wani kocin gasar firimiya da aka kora a wannan kakar kawo yanzu, amma kuma akwai da dama da ke cikin fargaba makomar aikinsu kafin hutun wasannin kasa da kasa na watan Nuwamba.
Matsin lamba kan Michael Carrick ya kara tsananta, bayan mummunar shan kashin da Manchester United ta yi da ci 4-1 a hannun Como a filin wasa na Stadio Giuseppe Sinigaglia a Italiya.
Ana kuma takaicin abin da ya faru da kungiyar a Champions League, sai Bournemouth ta je har Old Trafford ta doke United 3-0 a Premier League.
Hakan ne ya sa United ta yi nasara biyu daga karawa 12 a dukkan fafatawa, an kuma cire ta daga Carabao Cup, sannan tana ta 16 a kasan teburin Premier League bayan wasa takwas da fara karawar bana.
Magajin Tudor a Spurs, wato Roberto de Zerbi ya rage matsin lambar da ke kansa bayan nasarori biyu a jere da suka kai Tottenham matsayi na 12 a Premier League, yayin da kocin Fulham Alvaro Arbeloa shi ma ya samu saukin matsin lamba bayan cin Hull City da kuma Coventry da cin 1-0 kowanne.
Sai dai sabon kocin Nottingham Forest, Oliver Glasner da kuma kocin Sunderland Regis le Bris, wanda kungiyarsa ke buga gasar Europa League da ta cikin gida, tabbas za su kasance cikin damuwa a halin yanzu, saboda rashin samun sakamako musu kai a lig.
Marco Rose, ya dan samu sararawa, saboda yadda Bournemouth ta je har Old Trafford ta doke Manchester United har 3-0 a Premier League.
Kuma kafin nan ya doke AC Milan a Europa League, wanda hakan zai kara rage masa lamba a halin yanzu.
Kocin Crystal Palace, Pierre Sage ya nemi afuwar magoya baya, saboda shan kashi da ci 5-0 a hannun Brighton ranar Lahadi, kuma yanzu yana fuskantar fafutukar kare aikinsa watanni hudu kacal bayan komawa Ingila daga Lens.
Kawo yanzu ana sa ran wa za a fara korar a bana, shin za a kai cikin watan Nuwama ko sai a watan Disamba za a fara raba gari da koci, shin guda nawa za su rasa aikinsu a kakar nan?


























