Man United na harin Fermin Lopez, Arsenal na son Tresoldi

Asalin hoton, Getty Image
Manchester United na harin ɗan wasan Barcelona Fermin Lopez, a yunƙunrin Red Devils ɗin ke inganta ƴan wasan gaban ƙungiyar a watan Janairu. (Mail - subscription required)
Ɗan wasan bayan Manchester United Lisandro Martinez na shirin barin ƙungiyar a ƙarshen kakar wasa, in da ya fara jan hankulan Barcelona da Atlentico Madrid. (AS - in Spanish)
Arsenal ba ta da wata damuwa idan ta biya kuɗaɗen masu yawa kan ɗan wasan Club Brugge Nicolo Tresoldi kan fam miliyan 42, inda ake hasashen cewar farashin ɗan wasan zai ƙaru a kakar wasannin mai zuwa. (Football Insider)
Wasu ƙungiyoyin da ake buga gasar Firimiya na nazarin ɗan wasan Minnesota United Kelvin Yeboah, inda Everton ke kan gaba wajen ɗaukar ɗan wasan. (Talksport)
Manchester United na son ɗaukar ɗan wasan Najeriya da Fulham Calvin Bassey. (Teamtalk)
Barcelona na iya ɗaukar ɗan wasan Inter Milan Alessandro Bastoni a watan Janairu, bayan ta gaza ɗaukarsa a wannan kaka. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Leeds na matuƙar son ɗauko ɗan wasan Maccabi Tel Aviv Issouf Sissokho. (Football Insider)
Manchester United za ta mayar da hankali wajen samo ƴan wasan baya da na gaba a kakar siyen ƴan wasa mai zuwa. (Times - subscription required)
Crystal Palace za ta fuskanci zazzafar gogayya daga ƙungiyoyin Italiya wajen ɗauko ɗan wasan Lecce Tiago Gabriel. (Teamtalk)
Ɗan wasan Nottingham Forest Omari Hutchinson, da ke matsayin ɗan wasan aro a AC Milan, zai komo gida a kaka mai zuwa, a dai-dai lokacin da ƙungiyar ke harin ɗan wasan Real Madrid Endrick. (Gazzetta - in Italian)
























