Me ya sa kowace ƙasa ke son doke Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Najeriya na shirin fara kare kofinta na Wafcon da ta ɗauka a gasar da ta gabata.
Super Falcons ta lashe gasar sau 10 a tarihi inda ta ci ta ƙarshe a Moroko a watan Yulin bara.
Ƴanmatan na Najeriya a yanzu su ne madubin dubawa a gasar Kofin Afrika ta Mata.
Babban ƙalubalen da ke gabansu shi ne kare matsayinsu, abin da suka yi a 2018, lokacin da suka ci sau uku a jere.
"Yanzu da muke gwarazan gasar kowace tawaga za ta so taga ta janyo mun ƙasa", in ji kocin tawagar Justin Madugu, wanda ya ja ragamar gasar ta bara ya samu nasara da ci 3-2 kan masu masaukin baƙi.
Ya shaida wa BBC Sport Africa cewa "Ba abu ba ne mai sauƙi ba. Mun kwana da sanin haka, kuma mun shirya sosai."
A yau Talata ne Najeriya za ta fafata da Malawi da ta fara zuwa gasar a karon farko, kafin daga bisani ta zo ta fafata da Zambia da Egypt da suke Rukunin C tare.
"Ko wacce ƙasa na son doke Najeriya," in ji mataimakiyar kocin, Ann Chiejine wadda ta lashe kofin sau huɗu a matsayin 'yar wasa.
"Shi ya sa za mu fara wasannin da gaske ta hanyar atisayen da ya kamata."
Tawagar ɗauke take da wasu fitattun 'yan kwallo na nahiyar Afrika.
Kyaftin Rasheedat Ajibade ita ce gwarzuwar gasar ta bara, Chiamaka Nnadozie ita ke riƙe da matsayin mai tsaron ragar da tafi kowacce a yanzu, sai kuma wadda ta ci kyautar 'yar wasan Afrika sau shida ita ma tana cikin tawagar.
Duk da cewa Justin Madugu ya ƙaro wasu sabbin 'yan wasa biyu matasa, yar wasan gaba Joy Omewa, wadda ke taka leda a Sweeden ta kuma kalli nasarar da tawagarsu ta samu a bara daga nesa.
"Ta bara gaskiya ta ƙayatar, duka wasanni sun yi kyan gani.
"Ina ganin ta bana za ta fi zama gagaruma."
'Ba wani matsi da muke fuskanta'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Najeriya ɗaya ce daga cikin ƙasashe uku da suka taɓa lashe Wafcon.
Sun mamaye gasar inda suka lashe ta sau 10 cikin 13 da aka fara a 1998, sai Equatorial Guinea da ta lashe sau biyu a shekarun 2008 da 2012, yayin da Afrika ta Kudu ta ci a 2022.
A wannan lokacin za su fuskanci gagarumin ƙalubale, ko ta ɓangaren yawan wasanni da za a yi saboda faɗaɗa gasar daga ƙasashe 12 zuwa 16.
Fifa ta sauya tsarin yadda za a riƙa samun tikitin gasar kofin duniya da za a yi ta gaba a Brazil inda ƙasashe huɗu da suka je wasan kusa da ƙarshe za su samun tikitin kai tsaye.
"Abu na farko shi ne mu samu tikitin kofin duniya. Bayan nan sai mu fara batun kare kanbunmu," inji 'yar wasan gefe ta tawagar Francisca Ordega.
"Ba ma cikin wani matsin lamba. Za mu iya fafatawa da duk wata tawaga daga Nahiyar Afrika."
Najeriya ta wakilci Afrika a gasar kofin duniya guda tara tun daga wadda aka fara a China a 1991.
Cape Verde da Malawi su ne sabbin ƙasashen da za su fara fafatawa a gasar a bana.
Malawi ce ta 153 a jadawalin kasashen duniya, idan aka kwatanta da Najeriya da take ta 36.
Dole Najeriya ta mayar da hankali idan za ta yi wasa da Zambia saboda yar wasanta ta gaba da ke da ƙwarewa, Barbra Branda da kuma takwararta Racheal Kundananji da duka suke buga wasa a Amurka.
"Bai kamata mu raina abin da wani zai iya yi ba a gasar," inji Madugu bayan an fitar da jadawalin gasar an haɗa su da sabbin hawowa.
Cakuɗen kwararru da matasa

Asalin hoton, Getty Images
A baya an ga yadda lokaci ya so ya ƙurewa tawagar saboda rashin shiri da wuri, amma yanzu koci Madugu da tawagarsa sun samu damar shiri ta yadda suka yi wasannin sada zumunta domin haɗa wannan tawagar ta yanzu.
Wasan da suka yi nasara a kan Kamaru a farkon watan nan da wanda suka yi da Senegal a watan Yuni da kuma wanda suka samu nasara kan Tanzania a makon jiya.
Matashiyar 'yar wasan nan mai shekara 21 mai tsaron raga Comfort Erhabor, da kuma wadda aka ɗauka a matsayin ko ta kwana Nnadozie, suna cikin sabbin fuskokin da Madugu ya gabatar.
Matashiyar da aka haifa a Netherlands ta kuma tashi a England ta fara wasanta ne a wasan Kamaru.
"Yadda Madugu yake yarda da matasan 'yan wasa ya sa inda mutum ta shi sosai,"inji Ta.
"Ban yi tsammanin shiga cikin tawaga ba haka cikin ƙanƙanin lokaci, amma haka 'yan wasan suka karɓe ni da kyakkywar fuska."
Erhabor na wasa ne a Portsmouth da ke buga mataki na uku a Ingila, wata dama da ta bata ikon zama ydda take a yau.
Yayin da Madugu yake son cakuɗa matasan 'yan wasa da kwararru, Omewa ta bayyana Stellar da suka atisaye tare a matsayin wata "zinariya".
"Ba don su ba da yau ba za mu zo nan mu taka leda ba.
"Yayin da muke atisaye tare, suna koya mana yadda za mu riƙa wasa tare mu samu kwarewa daga wurinsu cikin ƙanƙanin lokaci."
Abokiyar wasanta ta gaba Oshoala wadda ke fatan cin kofin karo na biyar, tana cikin waɗanda Omewa ke yi wa godiya.
"Babbar 'yar wasa ce. tana cikin mutanen da za ka iya tattaunawa da su ba tare da wani jin ɗar ba, tana koya mana abubuwa sannan kuma tana ba mu labaran rayuwarta ta kwallo.
"Gaskiya babbar abar koyi ce."
Ba duka kwararrun 'yan wasan Najeriya ba ne ke cikin tawagarsu, saboda yar wasansu ta baya Ashleigh Plumptre wadda na cikin 'yan wasa ma su muhimmanci a tawagar take fama da jinya a ƙafarta.
Tawagar ba ta da nutsuwa bayan rikicin sata da aka zargi tawagar da ita daga isarsu Morocco, yayin da 'yar wasan gabansu Esther Okoronkwo ta yi asarar dalar Amurka mai yawa.
A ranar Litinin ne Hukumar Kwallon Ƙafa ta Najeriya ta fitar da sanarwa inda ta yi Allah wadai da nuna wari da zagin da aka rika yi wa Okoronkwo a kafafen sada zumunta.
Idan aka zo maganar kyautar kuɗi ga wadanda suka lashe gasar an ninka kuɗin, wanda ya lashe gasar zai samu kimanin dalar Amurka miliyan 2 - wani ƙari da yake nuna haɓɓakar kwallon ƙafar mata a Afrika.
Duk da ƙara faɗaɗa gasar, amma Najeriya ita ce tawagar da har yanzu kowa yake son ya samu nasara a kanta.











