KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 28 ga watan Yulin 2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Za mu yi amfani da kuɗin Iran da muke riƙe da su wajen biyan kuɗin yaƙi - Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da kuɗaɗen Iran da ke ƙarƙashin ikon Amurka wajen biyan kuɗin ɓarnar da yaƙin baya-bayan nan ya haddasa.

    Da yake magana da manema labarai a cikin jirgin shugaban ƙasa na Air Force One, Trump ya kuma yi watsi da rahotannin da ke nuna damuwa kan ƙarancin makamai a hannun Amurka bayan watanni ana kai hare-hare kan Iran.

    Ya ƙara da cewa tsohon shugaban ƙasar Joe Biden ya aika makamai masu yawa zuwa Ukraine, lamarin da ya sa Amurka ke ƙoƙarin sake cike ma'ajiyarta a yanzu.

    "Duk da haka, har yanzu muna da makamai masu yawa. A gaskiya muna da tarin makamai fiye da yadda za mu iya amfani da su," in ji Trump.

  2. An ji ƙarar fashewa da dama kusa da ofishin jakadancin Amurka a Iraq

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    An ji ƙarar fashe-fashe da dama a yankunan da ke kusa da ofishin jakadancin Amurka a birnin Erbil na yankin Kurdistan da ke arewacin Iraq, a cewar rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na yankin.

    Tashar Al Jazeera ta ruwaito cewa an samu aƙalla fashewa bakwai a yankunan da ke kusa da ofishin jakadancin Amurka da wasu muhimman gine-ginen diflomasiyya a birnin.

    Sai dai kamfanin dillancin labaran Tasnim, wanda ake alaƙanta shi da dakarun kare juyin juya halin Iran, ya wallafa hotunan da ke nuna harin da aka kai kan sansanonin ƙungiyoyin Kurdawa masu adawa da gwamnatin Iran.

    Kamar yadda Al Jazeera ta ruwaito, Tasnim ma ta ce an samu fashewa bakwai, amma ta bayyana wuraren da hare-haren suka auku da Khalifan da Soran, waɗanda ke yankin Erbil a Iraq.

    Har zuwa yanzu, babu wani bayani a hukumance kan yawan asarar da aka yi ko irin ɓarnar da hare-haren suka haddasa.

  3. Iran ta ce duk wani yunƙurin toshe tashoshin jiragen ruwanta zai haifar da ƙazancewar yaƙi

    ....

    Asalin hoton, IRNA

    Iran ta yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na sake toshe tashoshin jiragen ruwanta ko hana zirga-zirgar jiragen ruwa zai haifar da ƙazancewar yaƙi ne tare da jaddada cewa za ta mayar da martani kan duk wata barazana da ta fuskanta.

    A cikin wata sanarwa da Hedikwatar Khatam al-Anbiya, wadda ke jagorantar ayyukan yaƙin Iran, ta fitar a daren Litinin, ta ce Amurka ta yi barazana ga jiragen ruwan Iran da jiragen kasuwanci da tankokin mai a cikin ruwan ƙasar cikin kwanaki uku da suka gabata.

    Sanarwar ta ce: "Muna gargadin cewa wannan mataki na Amurka ana kallonsa a matsayin faɗaɗa yaƙi a yankin ne, kuma kamar yadda rundunonin sojin Iran suka nuna a aikace, ba za su bar wata barazana ko ta'addanci daga rundunar Amurka ba tare da mayar da martani ba."

    Wannan sabon gargaɗi na zuwa ne yayin da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ke ci gaba da ƙamari, inda hare-haren ramuwar gayya tsakanin ɓangarorin biyu suka shafe kusan makonni biyu ba tare da tsaiko ba.

    Rikicin ya ƙara zafafa ne kwanaki uku da suka gabata, a daidai lokacin da ake nuna kyakkyawan fata kan yiwuwar samun ci gaba a tattaunawar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

    Sai dai tattaunawar ta tsaya cik, yayin da Donald Trump ke ci gaba da jaddada cewa idan ba a samu sakamako mai gamsarwa ba, zai iya la'akari da ɗaukar matakin soja kan Iran.

  4. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za ta kasance da ku a wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.