KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa na 27 Yuli - 2 Agusta 2026

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 27 ga watan Yuli, zuwa 2 ga watan Agusta 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Diomande ya amince da sharuɗan Real Madrid

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    RB Leipzig winger Yan Diomande has agreed personal terms with Real Madrid after Paris St-Germain withdrew their interest.

    Dan wasan gefe na kungiyar RB Leipzig Yan Diomande ya amince da sharudan Real Madrid kan komawar kungiyar.

    Wannan na zuwa ne bayan da Paris St-Germain ta fita daga cinikin ɗan wasan na Ivoru Coast.

    A baya Liverpool ce ta matsa ƙaimi kan ɗan gaban mai shekara 19, wanda tun farko aka yi masa kuɗi £69m kuma ƙungiyarsa ta ki amincewa da tayin na Liverpool kuma PSG ma da ta taya aka ƙi amincewa da ita.

    Daga nan sai Liverpool ta koma kan wani ɗan wasan, PSG kuma ta zaɓi ta goga kafaɗa da Madrid.

    PSG ta yi tayin kan kuɗi £102.5m amma ba a sayar mata ba.

    Yayin da Real Madrid da ɗan wasanta na Brazil Vinicius suka gaza cimma matsaya, ana tsammanin Yan zai iya maye gurbin Jr Vinicius.

    Arsenal dai ta mayar da hankali kan ɗan wasan wanda rahotanni suka ce yaƙi tsawaita kwantaraginsa ya zuwa yanzu.

  2. Kalli yadda matan Nigeria suka chaɓa kwalliya lokacin isarsu Morocco

    Yayin da aka fara gasar cin kofin nahiyar Afrika ta Mata Wafcon a Morocco ƙasashe da dama sun isa Rabat babban birnin ƙasar cikin kwalliya da ƙayatarwa.

    Mafi yawan ƙasashen sun isa ne cikin tsarin al'adunsu da suke nuna ƙasashen da suka fito.

    Tawagar Super Falcons ta Najeriya ma ta isa Morocco da ta ta kwalliyar, ga wasu hotuna na yadda 'yan wasan suka isa kasar.

    ,

    Asalin hoton, NGSuper_Falcons

    a

    Asalin hoton, NGSuper_Falcons

    a

    Asalin hoton, NGSuper_Falcons

    ,

    Asalin hoton, NGSuper_Falcons

    a

    Asalin hoton, NGSuper_Falcons

    a

    Asalin hoton, NGSuper_Falcons

    ,

    Asalin hoton, NGSuper_Falcons

    h

    Asalin hoton, NGSuper_Falcons

    a

    Asalin hoton, NGSuper_Falcons

  3. Pirlo ba zai zama kocin Italiya ba kan alaƙa da kamfanin cacar Rasha

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Andrea Pirlo ya ce ba shi ne zaɓin da ya fi dacewa da ya zama kocin Italiya ba, biyo bayan kwanakin da aka shafe ana taƙaddama kan alaƙarsa da wani kamfanin caca na ƙasar Rasha.

    Hukumar kwallon ƙafa ta Italiya dai ba ta tabbatar da naɗa shi a matsayin sabon kocin ƙasar ba, sai dai an kusa kaiwa ga hakan.

    Amma a ƙarshen mako ne wasu manyan 'yan siaysa na ƙasar suka riƙa sukar Hukumar kwallon ƙafar kan zaɓar Pirlo, suna cewa kocin mai shekara 47 yana matsayin jakadan kamfanin caca na Rasha Fonteb tun watan Oktobar bara.

    Kamfanin ya ɗauki nauyin wasu tarukan wasanni da suka haɗa da tsofaffin mayakan da suka yi yaƙin Rasha da Ukraine kuma Pirlo ya halarci gasar tare da wasu masu goyawa fadar Kremlin baya.

    "Duk wanda yake goyon bayan Rasha daga 2022 bai kamata ya riƙe matsayi ba a matsaki na ƙasa" in ji Carlo Calenda na jam'iyyar Azione.

    "Bayan ganin muhawarar da ake ta tafkawa a kai na cewa ba ni ne na dace da aikin kocin Italiya ba, Ina ganin ya dace na fito na yi ƙarin haske kan wasu bangarori na mahawarar," in ji tsohon kocin na Juventus da AC Milan.

    "A 'yan kwanakin nan na ga abubuwan da suka ɓatan tai kan muhawarar, duk wata yarjejeniya da na sa wa hannu tana da alaƙa ne kawai da abin da ya shafi kwallon ƙafa babu wani abu na siyasa ciki," kamar yadda Pirlo ya rubuta a shafinsa na Istagram.

  4. Rogers da Palmer za su samar da sauyi a Chelsea - Alonso

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Chelsea Xabi Alonso ya ce shirinsa na haɗa ɗan wasan da suka saya £117m Morgan Rogers tare da Cole Palmer a cikin fili zani abu ne da zai samarwa ƙungiyar sakamakon da take so.

    Dan wasan tsakiyar shi ne wanda ya fi duk wani dan wasan Burtaniya tsada a tarihi, bayan sayen shi da Chelsea ta yi daga Aston Villa zuwa Stamford Bridge a makon jiya.

    Yanzu ɗan wasan na hutu ne bayan kammala gasar Kofin Duniya da ƙasarsa ta yi, kuma a gefe guda Chelsea sabuwar ƙungiyarsa ta fara wasannin share fagen kaka a Sydney.

    "A wannan hannun muna buƙatar gogaggun 'yan wasa kuma na yi imanin irin shi ba su da yawa a yanzu haka," in ji Alonso.

    Morgan Rogers ya sanya hannu kwantaragin shekara shida ne tare da Chelsea, kuma akwai zaɓin tsawaita kwantaragin idan ta ƙare.

  5. Chiesa na farin cikin da zamannsa a Liverpool amma yana buƙatar dama

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan gaban Italiya Federico Chiesa ya dage kan cewa shi Liverpool ce kawai a gabansa yayin da ake ci gaba da yaɗa jita-jita kan makomarsa a kwallon ƙafa.

    A kaka biyu da ya buga a ƙarƙashin kulawar Arne Slota a Anfield, wasa biyu kacal ɗan wasan gaban ya fara a Premier ya kuma ci kwallo biyar ne kawai a wasanni 50 da ya buga a duka gasanni.

    Dan wasan mai shekara 28 ya koma Anfield ne daga Juventus ne kan kuɗi £12.5m a 2024 kuma kwantaraginsa zai ƙare ne a 2028, ya shaida wa jaridar La Gazzetta a watan Yuni cewa : " Idan ban samu damar buga wasa a kai a kai ba, zai nemi wani wurin na tafi."

    Amma bayan cin kwallo ɗaya da ya yi a wasan da suka yi na sada zumunta ranar Asabar da Sunderland ƙarkashin Araola ya shaida wa manema labarai cewa "Lokaci ya yi yanzu, ina farin ciki a Liverpool, ina son ƙungiyar da komai nata da magoya baya".

  6. Ina Vinicius ya nufa Arsenal ko Real Madrid ?

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ko shakka babu akwai sauran taƙaddama a makomar ɗan wasan gaban Real Madrid Vinicius Jr.

    Dan wasan wanda babu ja yana cikin 'yan wasan kwallon ƙafa na duniya mafiya shahara gobensa ba ta bayyana ba ya zuwa yanzu.

    Dan Brazil ɗin zai shiga shekaarsa ta ƙarshe ne a kwantaraginsa da ƙungiyar ta Sifaniya, kuma irin waɗannan 'yan wasa ba a barin kwantaraginsu ta kai irin wannan lokaci ba tare da tsawaita ta ba.

    Ya koma Madrid ne yana da shekara 18 a 2018, ya ci kwafuna 14 ya zura kwallo 128 a wasa 375 da ya yi a ƙungiyar tasa.

    Rahotanni daga kasuwar saye da sayerwar 'yan wasan Turai na cewa darajar ɗan wasan za ta kai £200m.

    Madrid ta yi yunƙurin sabunta kwantaragin ɗan wasan ko kuma fara magana kan makomarsa ranar Litinin ɗin nan, sai dai har yanzu babu wata magana mai kwari kan hakan.

    Tuni Arsenal suka nuna muradinsu kan ɗan wasan, wanda wasu ƙungiyoyin Saudiyya suka riƙa nuna muradinsu kan shi.

    Kocin Gunners Mikel Arteta ya jima na son ɗaukar ɗan wasan da zai buga masa ɓangaren hagu wanda ya nuna kansa, kuma Vinicius ya nuna cancantarsa kan zaɓin.

    Tun bayan da ta rasa ɗan wasan da ta so ɗauka Morgan Rogers da Chelsea ta saya, Arsenal ta ƙara matsa ƙaimi kan ɗaukar ɗan wasan.

  7. Barkanmu da rana

    Masu bibiyar wannan shafi Muhammad Buhari Fagge ne ke fatan an tashi lashi, da fatan mun shiga sabon mako kalau.

    Za mu kawo muku rahotannin labaran wasanni da abubuwan da ke faruwa a kasuwar 'yan wasan nahiyar Turai.

    Me ake ciki tsakanin Real Madrid da Vinicius. Yaya batun Rashford kan komawar shi Manchester United. Me aka cimma tsakanin Madrid da Yan Diamonde. Barcelona ta hakura da Julian Alvarez kenan.

    Ku biyo mu domin samun cikakkun labaran.