Me ya sa Amurka ke goyon bayan ƙasashen da ke ficewa daga Kotun ICC?

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta yaba da matakin da Chadi ta ɗauka na ficewa daga Kotun Hukuman Manyan Laifuka ta ICC.
Chadi ta zama ƙasa ta biyar da ta sanar da matakin ficewa daga Kotun a baya-bayana nan.
Ko a makon da ya gabata ma ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun ɗauki irin wannan mataki.
Gwamnatin Chadi ta ce ta ɗauki matakin ne bayan da ta zargi zargi kotun da nuna bambanci a aikinta da mayar da hankali kan ƙasashen Afrika kawai.
Kotun ta daɗe tana fuskantar ƙalubalen ficewar wasu daga cikin mambobinta kuma yanzu tana cikin wani rikici na neman sabon babban mai gabatar da kara, bayan korar Karim Khan.
A kwanakin baya ne aka tsige Karim Khan a matsayin babban mai gabatar da ƙara, sakamakon zarge-zargen rashin da'a.
Khan wanda ya taba gabatar da sammacin kama Netanyahu— ya ce siyasa ce ta yi tasiri wajen tsige shi daga mukaminsa.

Asalin hoton, Getty Images
Me ya sa Amurka ke goyon bayan ficewa daga kotun?
Gwamnatin Amurka ta ce yi maraba da matakin Chadin na ficewa daga Kotun, inda ta bayyana kotun a matsayin "wata cibiya mai matsaloli da kura-kurai."
A cikin wata sanarwa da Ofishin Harkokin Afirka na Amurka ya wallafa a shafin X ya ce matakin da ƙasar ta ɗauka na nuna yunƙurin cin gashin kanta, kamar yadda wasu ƙasashe suka yi.
"Amurka ba za ta taɓa miƙa ikon cin gashin kanta ga wata kotun duniya da ba ta da cikakken alhakin bayyanawa ko amsa wa kowa ba," in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce hukumomin Amurka za su fara wani babban yunƙuri domin daƙile abin da ta kira wuce gona da iri da kuma amfani da ikon da ba ta da hurumin yi na Kotun ICC.
Amurka ta nuna damuwa kan yadda Kotun ICC ke gudanar da ayyukanta, tare da neman Chadi ta sake tunani kan ci gaba da kasancewa mamba a kotun.

Asalin hoton, Getty Images
'Zargin Chadi da hannu a rikicin Sudan'
Matakin Chadi na ficewa daga ICC ba ya rasa nasaba da zargin da ake yi wa gwamnatin Ndjamena da hannu a yaƙin makwabciyarta Sudan.
Dakarun Sojin Sudan da ƙungiyoyin agaji sun zargi Chadi da taimaka wa mayaƙan RSF na Sudan da makamai da aka shigo da su daga ƙasar Haɗɗiɗiyar Daular Larabawa.
Kodayake dukkanin ɓangarorin da ke yaƙi a Sudan ana zarginsu da aikata laifukan yaƙi, musamman kai wa fararen hula hari.
An kafa kotun duniya ta ICC a 2002 domin hukunta mutanen da suka aikata laifukan yaƙi.
Kotun mai kasashe mambobi 125, kuma 34 daga Afrika, tana fuskantar matsi da suka daga wasu manyan ƙasashe kamar Amurka da ba ta da wakilci.
Karkashin tsarin kotun mambobinta suna da haƙƙin kama duk wani da take zargi wanda kotun ta bayar da sammacen kama shi.
Ƙasashen da suka fice da masu shirin ficewa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Burundi ce ƙasa ta farko da ta fice daga kotun hukunta manyan laifuka da duniya ICC.
Burundi ta fice ne a hukumance a 2017 bayan ta zargi kotun da farautar yan ƙasashen Afrika.
Kotun ta zargi gwamnatin Burundi da aikata laifukan yaƙi da suka haɗa da aikata kisa da kuma azabtarwa.
A 2015 Burundi ta fuskanci zanga-zanga da tashin hankali inda aka zargi jami'an tsaro da murƙushe masu zanga-zanga ƙarƙashin jagorancin shugaba Pierre Nkurunziza bayan ya yanke shawarar neman wa'adi na uku.
Philippines ma a 2019 ta fice daga kotun bayan ta ƙaddamar da bincike kan shugaba Rodrigo Duterte kan kisan mutane a yakin da ya ƙaddamar kan masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Shugaba Duterte ya zargi kotun da nuna bambanci wadda ya ce ana amfani da ita a matsayin wani makami wajen ƙoƙarin karya gwamnatinsa.
Ƙasashen ƙungiyar AES - Nijar da Mali da Burkina Faso waɗanda dukkaninsu sojoji ne ke mulki a ƙarshen watan Yunin 2026 suka sanar ficewa daga kotun ta ICC a wani mataki na ƙara nesanta kansu da ƙasashen yammaci.
Kasar Venezuela ma ta ce tana shirin ficewa daga kotun ta ICC kan binciken da ta take yi na zargin aikata laifukan yaƙi zamanin gwamnatin hamɓararren shugaban ƙasa Nicolas Maduro.
Kenya da Afrika ta Kudu ma sun taba yin barazanar ficewa daga kotun ta ICC.
Manyan ƙasashe ba su da wakilci a ICC
Aikin Kotun ICC, ya shafi ƙoƙarin gurfanar da mutanen da ke da alhakin aikata manyan laifuka a duniya a lokacin da kasashe suka gaza aiwatar da hukunci kan hakan.
Sai babban ƙalubalen kotun shi ne rashin ikon tilasta aiwatar da hukuncinta, kuma manyan ƙasashe da dama irinsu Amurka da Isra'ila da China da Rasha ba su amince da ikon kotun ba, lamarin da ke kawo cikas ga yiwuwar gudanar da bincike kan ƙasashen.
Rashin manyan ƙasashen ya sa mambobinta da dama ke ficewa idan har ta nemi shiga ƙasar domin bincike da kuma gudanar da aikinta na gano laifukan yaƙi.
Tsohon babban mai gabatar da ƙara a ICC ya sha fuskantar barazanar takunkumin Amurka neman sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaron kasar Yoav Gallant kan laifukan yaƙi da aka aikata a yakin Isra'ila da Hamas a Gaza.
Gwamnatin Chadi ta ce daga cikin ayyukan bincike na kotun 13 da ta gudanar tun kafa ta, tara daga ciki sun shafi Afrika, sauran huɗu kuma na wasu sassa ne na duniya.
Wannan na iya zama dalilin da ya sa ƙasashe da dama na Afrika ke ficewa daga kotun.











