Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Champions League: Damar da PSG ke da ita a kan Arsenal
Da alama babu wani abu da ya fi ƙayatarwa a ƙarshen wannan kakar kamar karawar da za a yi tsakanin ƙungiyoyin Ingila da Faransa a wasan ƙarshe na gasar Champions League, bayan shafe tsawon kakar ana gwagwagwa.
Ƙayataccen wasan da zai gudana a filin wasa na Puskas Arena da ke birnin Budapest na ƙasar Hungary, shi ne karawa ta 63 da Arsenal za ta yi a wannan kaka, wadda ta fara kakar da nufin lashe kofuna huɗu rigis, har sai zuwa farkon watan Afrilu inda ta tabbatar hakan ba zai yiwu ba.
Ita kuwa Paris St-Germain wannan zai kasance wasanta na 56, idan aka cire wasa bakwai da ta buga a gasar cin kofin ƙungiyoyin ƙasashen duniya (Club World Cup) kafin fara kakar wasan bana.
Yayin da Gasar Kofin Duniya ke gab da isowa, za a iya cewa babu hutu ga ƴan wasan duka ɓangarorin biyu. To amma idan aka yi la'akari da wani abu ɗaya, ƴan wasan PSG ne suka fi samun hutu gabanin karawar ƙarshen ta Champions League.
Kocin PSG, Luis Enrique, ya rika hutar da dama daga cikin manyan ƴan wasansa a gasar Ligue 1 a wannan kakar. Wannan dama ta samu ne saboda saukin hamayya a gasar cikin gida da matasan ƴan wasan da aka gina da taimakon ɗimbin dukiyar da mamallakr ƙungiyar ƴan Qatar suka zuba.
Saboda PSG ta kare a matsayi na 11 a matakin teburi a Champions League, ƙungiyar ta buga wasa 16 kafin kaiwa zagayen karshe, ciki har da nasarar da ta samu kan Monaco a zagayen cike gurbi. Arsenal kuwa ta buga wasa 14 kacal kafin kaiwa wannan mataki na karshe.
Idan aka yi la'akari da ƴan wasan ƙungiyoyin biyu da suka kara a falle na biyu na matakin kusa da karshe na gasar, ƴan wasan Mikel Arteta sun buga ƙarin mintuna idan aka kwatanta da ƴan wasan ƙungiyar PSG — jimillar mintuna 6,726 kenan.
Wasu daga cikin alkaluman kokarin ƴan wasa daban-daban sun ɗauki hankali sosai kafin karawar karshe a UEFA Champions League, tsakanin Arsenal da Paris Saint-Germain.
Ƙyaftin din PSG, Marquinhos, ya yi karawa 14 a Champions League — adadin da ya yi daidai da yawan fitowarsa gaba daya a Ligue 1, inda ya buga wasa 11 sannan aka saka shi cikin fili daga benci sau uku.
Daga 13 ga Fabrairu zuwa 19 ga Afrilu, tsohon ɗan bayan Brazil din bai taka ko minti ɗaya ba a gasar lig, inda ya kasance a benci ba tare da an saka shi ba a wasa bakwai a jere. Sai dai ya buga dukkan mintunan wasanni shida a Champions League a wannan lokaci.
Mai rike da ƙyautar Ballon d'Or, Ousmane Dembele, ya kammala mintuna 90 cikakku sau daya kacal cikin wasa 22 da ya buga a lig. Shi ma ɗan wasa, Khvicha Kvaratskhelia ya kammala cikakken wasa sau biyu ne kawai daga karawa 28.
A ranar 12 ga watan Mayu, Dembele ya sake lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasa na Ligue 1 a karo na biyu a jere, duk da cece-kuce da aka sha fama kan lamarin. Ya ci kwallo 10 tare da bayar da bakwai aka zura a raga.
Sai dai ya yi fafatawa 11 kacal a lig, kuma ya buga wasa 22 daga cikin 34 da PSG ta yi gaba ɗaya, yayin da matsalolin rauni suka sa ya rasa wasa 10.
Salon sauya ƴan wasa da koci, Luis Enrique ke amfani da shi ya ba PSG damar hutar da taurarinta da yawa. Ya yi amfani da ƴan wasa 28 a lig idan aka kwatanta da 25 da Mikel Arteta ya yi amfani da su a Arsenal.
Sai dai wannan tsarin ya jawo wasu matsaloli, duk da cewa ba masu yawa ba ne. Uku daga cikin rashin nasarar PSG shida a lig — da Olympique Marseille da AS Monaco da Olympique Lyonnais — sun zo ne bayan wasannin Champions League.
Warren Zaire-Emery shi ne ya fi kowa buga mintuna da yawa a PSG da jimillar mintuna 2,453. Amma ƴan wasan Arsenal shida sun zarce wannan adadi.
Ana kallon Premier League a matsayin gasa mafi karfi a Turai, ba wai kawai saboda son kai na Ingila ba idan ta zo kwarzanta abu, domin ma'aunin UEFA na association coefficients ya sanya Premier League a matakin farko a Turai, yayin da Ligue 1 ke matsayi na biyar.
Duk da haka, ya kamata a tuna cewa PSG ta buga wasa 58 a kakar bara lokacin da ta lashe kofuna hudu, ciki har da Champions League na farko a tarihinta, bayan da ta doke Arsenal da jimillar 3-1 a wasan kusa da na karshe.
Haka kuma, Ligue 1 tana da wasa huɗu kasa da Premier League saboda tsarin kungiyoyi 18 da take amfani da shi.
Ko ta yaya, babu shakka manyan ƴan wasan Arsenal sun yi aiki tukuru a wannan kakar. Mai tsaron gida David Raya ya buga dukkan mintunan kakar har sai da aka hutar da shi a wasan karshe da Crystal Palace, bayan sun riga sun lashe kofin.
Declan Rice, William Saliba, Gabriel Magalhaes da Martin Zubimendi duk sun fara a wasa aƙall 30 na lig a Arsenal — abin da Warren Zaire-Emery kadai zai iya fada a bangaren PSG.
Har ma Jurrien Timber, wanda ya ji rauni tun tsakiyar watan Maris kuma har yanzu ana shakkar ko zai buga wasan karshe, ya yi mintuna fiye da na yawan Zaire-Emery.
Daga cikin ƴan wasa 10 da suka fi kowa buga mintuna a lig tsakanin ƙungiyoyin biyu a wannan kakar, biyu kacal ne daga PSG — Warren Zaire-Emery da Illia Zabarnyi.
Yadda Arsenal za ta tunkari wasan karshe zai kasance abin sha'awa sosai, musamman bayan ta lashe kofin Premier League, saura karawa ɗaya a kammala kakar bana, lokacin da Manchester City ta yi canjaras da Bournemouth a ranar Talatar da ta gabata.
Da dama daga cikin fitattun ƴan wasan Arsenal an hutar da su a karawar karshe ta kakar, inda suka doke Crystal Palace da ci 2-1.
A bangaren Paris Saint-Germain kuwa, ƙungiyar ta tabbatar da lashe Ligue 1 tun ranar 13 ga Mayu, bayan nasarar 2-0 a wajen RC Lens, ƙungiyar da ta zo ta biyu da maki shida a baya.
PSG ta sha kashi 2-1 a wasan karshe a lig da Paris FC, bayan an ba su kofin kafin. Wannan wasa ya gudana ne a ranar 17 ga Mayu, wanda ke nufin PSG za ta samu hutun kwanaki 13 kafin wasan karshe, yayin da Arsenal za ta samu kwanaki shida kacal.
A watan Maris, ƙungiyar ta koci Luis Enrique ta samu amincewar ɗage wasan lig da Lens, domin ba su damar mayar da hankali kan zagayen kwata fainal a karawarta ta Champions League da Liverpool.
Luis Enrique ya ce: "Kowane wasa daban yake kuma yana da kalubalensa. Dole ne mu yi la'akari da komai."
Ya kara da cewa: "Ina bukatar magana da ƴan wasa ɗaya bayan ɗaya. Ba abu ne mai sauki ba, kamar wasan Tetris ne. Dole ne mu samu maki uku sannan kuma mu tabbatar ƴan wasan sun dawo cikin koshin lafiya, domin buga karawa mafi muhimmanci a kakar."
PSG ta lashe Ligue 1 sau 12 cikin shekaru 14 da suka gabata, bayan da ta ɗauki kofin sau biyu kacal kafin kamfanin Qatar Sports Investments ya mallaki ƙungiyar ɗin gaba ɗaya a 2012.
A daya bangaren, Arsenal ta kawo karshen jiran shekaru 22 kafin sake lashe kofin Premier League, wanda ya sa kungiyoyin biyu yanzu suke da kofunan lig guda 14 kowacce.
Sai dai PSG ce ke da rinjaye idan aka zo batun yawan lashe Champions League mai ɗaya a tarihi. Amma komai na iya canzawa a wasan ranar Asabar.