Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa ministocin Tinubu suka kasa samun takara a zaɓukan fitar da gwani?
Ƴan Najeriya na ci gaba da dora ayar tambaya kan abin da ya hana ministocin Tinubu da suka ajiye aiki don neman takara cimma burinsu.
Aƙalla ministocin gwamnatin Tinubu biyar ne suka ajiye aiki da nufin tsayawa takarar kujeru daban-daban a zaɓen 2027 da ke tafe.
A makon da ya gabata ne jam'iyyar APC mai mulki ta gudanar da zaɓukan fitar da gwani a kujeru daban-daban, a shirye-shiryen zaɓukan 2027.
Sai dai wani abu da ya ɗauki hankali shi ne daga cikin mutanen biyar, ɗaya ne kawai ya samu kujerar da ya je nema kai tsaye, yayin da uku suka rasa, ɗaya kuma aka sauya masa kujerar da ya je nema daga sanata zuwa ɗan majalisar wakilai.
Su wane ne ministocin Tinubun da suka sauka daga muƙamansu don tsayawa takarar 2027?
Yusuf Maitama Tuggar
Shi ne tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, da ya shafe shekara uku a kan kujerar.
A ƙarshen watan Maris ne ya sanar da ajiye muƙaminsa domin tsayawa takarar gwamnan jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Tuggar ya shiga fafatawar neman yi wa APC takarar gwamnan Bauchi, ɗaya daga cikin jihohin da zaɓukan fitar da gwanin jam'iyyar suka fi ɗauki hankali.
Sai dai bayan fafatawa a zaɓen fitar da gwani, tsohon ministan bai samu nasara ba, bayan da ya sha kaye a hannun tsohon gwamnan jihar, Mohammed Abubakar.
Sa'id Ahmed Alƙali
Tsohon ministan sufurin ƙasar, na daga cikin sahun farko na ministocin Tinubu da suka ajiye aiki da nufn tsayawa takarar 2027.
Sa'idu Alƙali ya nemi takarar gwamnan Gombe, jihar da takarar APC ta fi ɗaukar zafi a Najeriya.
Tsohon ministan na daga cikin ƴantakarar da suka yi watsi da maslaha a jihar, inda ya buƙaci a yi zaɓen ƴartinƙe.
Bayan gudanar da zaɓen, tsohon ministan ya sha kaye a hannun ɗantakarar da gwamnan jihar ya goya wa baya.
Adebayo Adelabu
Tsohon ministan lantarkin shi ne mutum na ƙashe da ya sauka daga muƙaminsa domin tsayawa takarar gwamnan jihar Oyo d ake kudu maso yammacin ƙasar.
Sai dai shi ma bai yi nasara ba a zaɓen fitar da gwanin da aka gudanar ta hanyar ƴartinƙe.
Adebayo Adelabu ya yi zargin tafka maguɗi a zaɓen da Sanata Sarafadeen Alli ya yi nasara.
Yusuf Tanko Sununu
A ƙarshen watan Maris ne Yusuf Tanko Sununu ya sauka daga muƙaminsa na ministan ayyukan jin-kai na ƙasar, domin tsayawa takarar Sanata a jihar Kebbi.
Sai dai bayan tutuɓa mai yawa, tsohon ministan ya janye tare da samun takarar majalisar wakilai ta tarayya don wakiltar mazaɓar Yauri/Shanga/Ngaski.
Tun kafin Tinubu ya naɗa shi minista a 2023, Tanko Sunusu ke matsayin ɗan majalisar wakilan ƙasar.
Nkeiruka Onyejeocha
Tsohuwar ƙaramar ministar ƙwadagon ta Najeriya ta ajiye muƙaminta domin tsayawa takarar ƴarmajalisar wakilai da tarayya dmin wakiltar mazaɓar Isuikwuato/Umunneochi da ke jihar Abia a kudu maso gabashin ƙasar.
Ms Onyejeocha ta yi nasarar samun takarar a jam'iyyar APC, lamarin da ya sa ta kasance minista ɗaya tilo da ta cimma burinta bayan ajiye aiki.
Me ya hana su samun takarar?
Babban abin da ya ɗauki hankali shi ne yadda ake ganin ministocin na da kusanci da shugaba Tinubu a sama, amma suka kasa samun tikitin takara a APC.
To sai Dr Kabiru Sa'id Sufi, malami a Ƙwalejin Share Fagen shiga Jami'a da ke Kano a Najeriya ya ce dalilai biyu ne suka hana ministocin samun nasara.
Hanya ta farko ita ce akwai yiwuwar ba su nemi shawarar shugaban ƙasa kafin ajiye aikin nasu don tsayawa takarar ba, kamar yadda Dr Sufi ya bayyana.
''Abu na farko da ya janyo musu hakan shi ne kila ba su nemi shawarar shugaban ƙasa kafin neman takarar ba, kawai sun sanar masa za su yi takara ne, amma ba su nemi amincewarsa ba'', in ji shi.
''Wasu waɗanda ba ministocin ba, ana cewa sun samu takarar ne saboda sanya bakin fadar shugaban ƙasar'', in ji shi.
Masanin siyasar ya ƙara da cewa abu na biyu da ya janyo wa ministocin rashin nasara shi ne rashin samun goyon bayan gwamnoninsu.
"Gwamnoni ne suka nuna musu tasiri a jihohin nasu, kasancewar ba su samu goyon bayan Shugaba Tinubu ba ya sa gwamnonin suka yi amfani da damarsu wajen saka mutanen da suke ganin za su iya tanƙwarawa, maimako sun ministocin da suka dawo daga sama'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ko tsoffin ministocin za su iya barin APC
Dr Sufi ya ce zuwa yanzu babu alamun da ke cewa tsoffin ministocin za su fice daga APC.
''Babu wata alamar bijirewa a gare su ba zuwa yanzu, saɓanin wasu da ba su samu takarar ba'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa babu wasu kalaman tunzuri daga gare su da ke nuna cewa za su fice daga APC.
''Wataƙila abin da za su yi shi ne kame hannayensu su koma gefe'', in ji masanin siyasar.