'Tinubu ne ya ƙaƙaba mana ɗan takara a Bauchi'

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Siyasar jihar Bauchi daga arewa maso gabashin Najeriya, wata siyasa ce da ke bai wa gwamnoni kunya, a irin siyasar ruwa na cinye gwanaye sosai, don haka da wuya wani ya daki kirji yace kai tsaye ga abin da zai faru.

Siyasar ubangida ba ta fiye tasiri ba a jihar, shi yasa a wannan karon manyan wadanda suka yi takarar neman kujerar gwamna a jihar suka kadu da sakamakon zaben fidda gwamanin da aka yi.

Cikin wadanda suka shiga neman tikitin takarar akwai ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tugga, da Sanata mai ci Sanata Umaru Shehu Buba, da agoran yakin neman zaben shugaba Tinubu a Jihar Bauchi a 2023,Nuru Mani Soro, sai kuma Bala Mai Jama'a Wunti, wanda tsohon shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC ne.

Amma a karshe tsohon gwamnan jihar da ya yi jagoranci tsakanin 2015 zuwa 2019 Barista Muhammed Abdullahi Abubakar, ne ya samu, wanda ya yi shekara hudu a baya ya fadi zabe yanzu kuma ya samu tikitin takarar domin kammala shekara hudun da suka rage masa.

Wannan abu dai bai yi wa abokan burmin Baristan dadi ba.

Yusuf maitama Tugga, tsohon ministan harkokin wajn Najeriya, na daga cikin wadanda wannan mataki na tsayar da Barista bai yi wa dadi ba, ya shaida wa BBC cewa, gaskiya wannan mataki bai yi masa dadi ba.

Ya ce,"Mu da a son a ranmu ne mun so ayi zabe wabda ya ci ya ci, wanda ya fadi kuma shi ke nan, to amma sai shugaban jam'iyyarmu ta APC na kasa ya kira mu y ace an zabi M.A Abubakar, a matsayin dan takarar gwamna."

" Wannan zalunci ne wanda kuma ya fara tun lokacin da ministan lafiya na Najeriya ya tunbuke sakataren jam'iyyarmu na jiha inda ya sa ma'aikacinsa."In ji shi.

Honorabil Nuru, shi ma ya bayyana rashin jin dadinsa da zaben a fili, yana mai cewa makomarsa a APC babu tabbas.

" Tun lokacin da aka yi zaben shugabannnin jam'iyya aka samu kura-kurai da Rashin fahimta, kuma mu Bauchi a zaben fidda gwani ba, an dai kira mu mu da muke neman kujerar aka sanar damu cewa akwai sakon shugaban kasa akan wanda zai yi wa APC takarar gwamna." In ji Hon Nuru.

Ya ce, "Mu dai an zabo mana dan takarar ne kamar shugaban jam'iyya ya ce, kuma shugaban kasa ma ya fada.Shi wanda aka fi magana akansa wato ministan lafiya Muhammad Ali Pate daga Bauchi, ba zai fita daga zargi ba."

Hon Nuru, ya ce " Yanzu ni a yau, dan APC ne amma zuwa anjima ko zuwa gobe ban san me zai faru ba."

A cewar Sanata Umaru Shehu Buba, tun gabanin ranar Laraba ya gano Juma'arsa a APC ba za ta yi kyau ba shi yasa ya koma PRP kuma ya samu tikitin takarar gwamnan.

Ya ce," Shekara uku ko hudu mu ke jigilar jam'iyyar APC a Bauchi, to an zo zabe, amma wasu bata gari da bas a iya cin zabe ko a akwatinsu sun samu dama a gwamnati suka yi abin da suke so, domin an zo ranar da za ayi zaben fidda gwamni ba a ga kowa ba hatta jami'an zaben."

" Wannan ai ba dimokradiyya ba ne, shugaban kasa shi ne zai zabawa mutanen Bauchi wanda zai shugabance su?" in ji shi.

BBC dai yi yunkurin ji daga Shugaban Jam'iyyar APC na jihar Bauchi Muhammad Tilde, amma baya daukar waya, kazalika an tuntubi ministan lafiyar da aka yi wa wadannan zarge-zarge shi ma ba a same shi ba.

Jihar Bauchi dai na daga cikin jihohin da za a samu sabon gwamna a babban zaben 2027, sai dai tun daga gudanar da zabukan fidda gwani da aka gudanar rikici ya dabaibaye jam'iyyun siyasa a jihar.

Zabukan fidda gwani a kusan duka jam'iyyun Najeriya na barin baya da kura tamkar dai wannan, wasu masana na ganin tsarin sulhu da jam'iyyar APC ta runguma, na daya daga cikin matakan da suke yi wa dimokradiyya dabai-bayi.