'Yadda yunwa ke tursasa wa mutane zuwa tsibiran mayaƙan Boko Haram'

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Kimanin shekara 15 kenan Boko Haram na abu ɗaya: kisa da tarwatsa al'umma a yankin tafkin Chadi da sunan jihadi.

Dubun-dubatar rayukan mutane sun salwanta, sannan miliyoyin mutane sun tarwatse, a cewar ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights International.

Har yanzu ƙungiyar na ci gaba da ƙaddamar da hare-hare kan jami'an tsaron Najeriya da wuraren ibada da kasuwanni da kuma ƙauyuka, akasari kan fararen hula.

Sai dai yayin da hukumomi da ƙasashen duniya ke ta ƙara ɗamarar yaƙi da abubuwan da ke faruwa a yankin, bayanai na cewa yankin na tafkin Chadi wata duniya ce ta daban, inda ake hada-hada ta tattalin arziƙi har ma mutane da dama ke dogaro da yankin - mai matuƙar hadari - wajen ci gaba da rayuwa.

"Mutane ne rububin zuwa wurin," a cewar Abubakar Gamandi, wani ɗan asalin yankin kuma shugaban masunta na yankintafkin Chadi.

Tamkar hawa siraɗi ne, akwai yiwuwar a mutu ko kuma a dawo a raye.

Me ya haifar da hakan?

Matsalar rikicin Boko Haram a tafkin Chadi ya haifar da matsalar jin-ƙai mai girman gaske a Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

Lamarin ya jefa mutane da dama cikin ƙangi, inda mutane suka rasa hanyar samun abin rayuwa.

Sai dai bayan sama da shekara 10 ana abu ɗaya, yanzu alaƙa ta sauya, inda mayaƙan Boko Haram da kuma mutanen da rikicin ya tarwasta tun farko suka fahimci cewa za su iya ci gaba da rayuwa da juna, a wani yanayi na cuɗanni-in-cuɗe-ka.

Hakan na faruwa ne saboda rayuwa ta yi ƙunci ga mazauna yankin sanadiyyar taɓarɓarewa tattalin arziƙi.

"Akwai mutanen da za ku ji ana cewa an mayar da su ƙauyukansu bayan, to amma mutane sun tara iyali, wasu suna da mata hudu da yara, amma babu aikin yi, babu abin da za su ciyar da iyalinsu, saboda haka sai su koma cikin daji inda ke ƙarƙashin Boko Haram suna kamun kifi ko kiwo domin samun abin rayuwa," in ji Gamandi.

Mutumin ya ƙara da cewa abin da ya sa kenan aka kashe mutane irin waɗannan da yawa lokacin da sojojin Chadin suka kai hari a kan irin wadannan tsibirai a farkon watan Mayu.

Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin harin an kashe gomman masunta sannan wasu kuma sun nutse a cikin ruwa yayin da suke ƙoƙarin tserewa.

Ta yaya alaƙar ta fara?

Gamandi ya ce "mutane sun koma yankin ne sanadiyyar yunwa".

Ya ƙara da cewa "tun mayaƙan Boko Haram na kashe su har suka dawo suka amince da su amma suka sanya musu sharaɗi".

A cewarsa mutane da suka yi sulhu da mayaƙan domin gudanar da sana'o'insu sun hada da masunta da manoma da kuma makiyaya.

Sukan ƙyale masunta su gudanar da kamun kifi, makiyaya kuma su yi kiwon dabbobi sannan manoma su noma gonakinsu matuƙar suka amince da sharaɗin da mayaƙan suka gindaya musu.

Ya bayyana cewa wannan al'amari na faruwa ne a wasu yankunan ƙasashen Chadi da Jamhuriyar Nijar da Kamaru, amma a Najeriya akwai irin wadannan tsibirai a ƙananan hukumomin Abadam da Kukawa da Monguno da Marte da kuma Ngala.

Sharadin da mayaƙan kan kafa wa mutanen sun haɗa da:

  • Haramta amfani da wayar hannu
  • Kada mutum ya yi magana da asalin mazauna tsibirin
  • Kada a kai musu labarin abin da ke faruwa a birni
  • Kada a ɗauki labarin abin da ke faruwa a tsibirin a kai cikin birni

Gamandi ya ce akan hukunta duk wanda aka samu da saɓa irin waɗannan ƙa'idoji ta hanyar gargadi ko bulala ko kuma idan abin ya yi tsanani kisa.

"Babu mai yin sulhu a wadannan tsibirai sai su (mayaƙan Iswap)".

Me ya sa Boko Haram ta ƙyale mutane shiga yankinta?

Abubakar Gamandi ya ce a wasu lokuta mayaƙan Iswap ko Boko Haram ne ke safarar mutane zuwa wadannan tsibirai domin gudanar da harkokin kamun kifi.

"Ko ba ka da kudi, za su iya ɗaukar ka a kwale-kwale ko ba ka da kuɗi, idan ka kama kifi ka sayar sai ka biya su".

To amma me ya sa mayaƙan suke nuna wannan zalama?

Mayaƙan na neman hanyoyin samun kuɗi da kuma hanyoyin da za su riƙa samun kayan masarufi.

Kasancewar suna karɓar haraji daga masu kamun kifi, wannan wata babbar hanya ce ta kudin shiga.

Haka nan kuma sukan bai wa masunta saƙo domin sayo musu abubuwan buƙatu na yau da kullum idan za su je cin kasuwa na mako-mako.

Idan babu irin wadannan masunta za su iya shan wahala wajen samun hakan.

Gamandi ya ce akasarin mutanen da ke zuwa yankunan kan yi biyayya ga dukkanin sharuɗɗan da Boko Haram ɗin ta gindaya musu.

Ko gwamnati na da masaniya?

Rahotanni sun nuna cewa yankin da mayaƙan Boko Haram da kuma masuntan ke haduwa wuri ne da ya zarce inda sojoji ke zuwa.

"Sojoji ba su zuwa bakin ruwan da Boko Haram ke zuwa su kwashi mutane domin zuwa kamun kifi, tafiya ce ta kimanin awa biyu kuma a kan amalanke, wurare irin su kwatan kirikiri, kwatan barwa, Gigime da kuma Barwa a Jamhuriyar Nijar".

Kwamishin sadarwa na jihar Borno Farfesa Usman Tar ya ce: "Gwamnati ta san mutanen suna zuwa irin wannan wuri amma gwamnati ta hana zuwa duk inda gwamnati ba ta tabbatar da amincinsa ba.

"Abin da ya sa aka hana shi ne idan sojojin sun kai farmaki, bai kamata abin ya shafi talakaba.

"To amma idan mutum ne ya kai kansa, wurin ƴan ta'adda, kuma aka kai hari, abin zai iya taba su".

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta sha yin faɗakarwa ta amfani da harsuna daban-daban, kan cewa mutane su daina zuwa irin waɗannan yankuna.

A tattaunawarsa da BBC, Tar ya ce akwai wasu yankuna na tafkin Chadi da sojoji suka kori mayaƙan Boko Haram daga cikinsu, kuma aka amince wa mutane su kama kifi a cikinsu.

"Ai shi kifi ba sai ka je wurin ƴan ta'adda za ka same shi ba," a cewar kwamishinan.

Ya ƙara da cewa akwai yankunan Baga da sojojin Najeriya suka kori mayaƙa, kuma yanzu haka akwai mutane da ke hada-hadarsu a wurin.

Ya bayyana doka ta haramta irin harajin da mutanen ke biyan mayaƙa, kuma "duk wanda aka kama tare da ƴan ta'adda, shi ma ɗan ta'adda ne".