Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ina makaman da ake safara zuwa Najeriya ke shigewa?
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
A cikin watanni shida na farkon shekarar 2026, an shiga da da makamai da alburusai da darajarsu ta kai naira biliyan 55.06 cikin Najeriya, kamar yadda sabbin bayanan da hukumar ƙididdiga ta ƙasar, NBS, ta fitar.
Waɗannan alƙaluma na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro, da hare-haren ƴanbindiga da sauran ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, yayin da ake ƙara nuna damuwa kan yaɗuwar bindigogi da sauran makamai ba bisa ƙa'ida ba a sassan ƙasar.
Haka kuma, ƙarin shigo da makaman ya zo ne yayin da Najeriya ke gab da shiga shekarar zaɓen 2027, abin da ya sake nuna damuwa kan yadda makamai ke shiga ƙasar da kuma inda suke zuwa.
Ko da yake waɗannan alkaluma, ba su bayyana cewa ko akwai wasu adadin makaman da ke hannun hukumomin tsaro ko kuma waɗanda ke hannun ƴanbindiga da sauran ƙungiyoyi ba
Sai dai babban abin tambaya shi ne: ina waɗannan makaman suke shigowa Najeriya, ta waɗanne hanyoyi suke shiga, kuma me ƙarin shigo da su ke nufi ga tsaron ƙasar?
Wannan ne abin da BBC za ta duba a cikin wannan labari.
Abin da alƙaluman ke nufi
Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin da ke nazari kan harkokin tsaro a nahiyar Afrika na Beacon Security and Intelligence Limited ya ce duk da cewa alƙaluman ba su fayyace komai a fili ba amma ba abin mamaki ba ne idan an ga cewa an kashe waɗannan kuɗaɗe kan makamai a Najeriya.
Ya ce a yadda bayanai suka nuna gwamnatin ta ware kusan naira tiriliyan biyar a kasafinta kan tsaro a 2026, wanda babu wani fanni da ya samu irin wannan tagomashi.
"Idan ka duba matsalar da ake da shi a Najeriya ba za a ce wannan abin damuwa ba ne," in ji shi.
Saboda haka Dr Kabiru ya ce akwai buƙatar hukumomi su riƙa bibiya su gano diddigin inda makaman da ba na hukumomi ba suke fitowa.
Ya kuma ce dole ne a magance matsalar tsaron kafin lokacin zaɓe saboda gudun barazanar da hakan zai iya yi idan kaso mai yawa na makaman suna hannun masu tayar da ƙayar baya.
Shin an gano daga inda makaman ke fitowa?
Kabiru Adamu ya ce binciken hukumar ta NBS ya tsaya ne kawai kan nazari game da abubuwan da aka yi shige da fice da su a Najeriya, kuma babu wani bayani dalla-dalla kan inda suka fito.
A taƙaice a cewarsa babu wasu sahihan bayanai game da waɗanda ke shigo da makaman da inda suka tafi.
Sai dai ya ce idan aka kalli ɓangarorin hukumomin da abin da suke yi, za a iya cewa makaman na hannunsu.
Masanin ya ce kai tsaye ba za a danganta dukkan makaman da rahoton ya ambata ba da ƴanbindiga saboda ba lallai a iya tabbatar da hakan.
Me ya kamata gwamnati ta yi?
Dakta Kabiru Adamu ya ce ya zama wajibi a irin wannan lokaci gwamnati ta yi amfani da irin waɗannan alƙaluma domin gano inda kowane makami yake tare da sa ido wajen bibiya yadda ya kamata.
"Kamata ya yi gwamnati ta ɗauki wannan bayanan, ta tabbatar da cewa duk wani abu da ke da nasaba da makami, hukuma ne ke riƙe da shi," in ji shi.
Ya ƙara da cewa tunda hukumar gwamnati ce ta fitar da makaman, to za ta iya amfani da dabarun da ta bi wajen gano su wajen tantance tushensu.
Shin hukumomi sun san da wannan?
Ko da yake ba a san ainihin adadin makaman da ke shigowa Najeriya ba, hukumomin ƙasar sun sha kama makamai da ake ƙoƙarin shigo da su ta hanyoyin daban-daban.
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce ta kama bindigogi kusan 603 da ake ƙoƙarin shigo da su ƙasar tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2026. An ce an miƙa makaman da aka kama ga Cibiyar Kula da Ƙananan Makamai ta ƙasar.
Wannan ba sabon batu ba ne ga hukumomin tsaron Najeriya.
A watan Yulin 2025, tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, wanda shi ne ministan tsaro na yanzu ya nuna damuwa kan yawaitar makamai ba bisa ƙa'ida ba a ƙasar.
Ya ce akwai kimanin kashi 40 cikin 100 na makamai ba bisa ƙa'ida ba da ke yawo a ƙasashen Yammacin Afirka a Najeriya.
Ya kuma yi gargadin cewa rashin zaman lafiya da rikice-rikicen da ke faruwa a sassan duniya na ci gaba da yin tasiri kan yanayin tsaron cikin gida na Najeriya.
Sai dai idan hukumomi suna kama wasu daga cikin makaman da ake ƙoƙarin shigowa da su, kuma hukumomin tsaro sun daɗe suna bayyana damuwa kan yawaitar makamai a ƙasar, tambayar da ta rage ita ce: ta ina sauran makaman suke shigowa, kuma ina suke ƙarewa?