Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gwamnonin da ba za su je majalisar dattawa ba bayan kammala mulki a 2027
A yayin da zaɓen shekarar 2027 ke ƙara matsowa, siyasar Najeriya na shiga wani sabon salo, musamman a jihohin da gwamnoni masu ci ke kammala wa'adinsu na biyu.
Bayan shafe shekaru takwas a kan karagar mulki, wasu daga cikin waɗannan gwamnoni suna fuskantar barazanar makomar siyasar su bayan barin ofis.
A al'adance, yawancin gwamnoni da ke kammala wa'adinsu kan karkata zuwa neman kujerar Majalisar Dattawa domin ci gaba da kasancewa cikin harkokin siyasa a matakin ƙasa.
Wannan mataki ya zama tamkar wata hanya da ƴan siyasa ke bi domin ci gaba da tasiri da kuma kare muradunsu bayan sauka daga mulki.
Sai dai a wannan karon, akwai wasu gwamnoni da wa'adinsu zai ƙare a 2027 waɗanda ba su nuna sha'awar neman kujerar sanata ba.
Matakin nasu ya janyo ce-ce-ku-ce da hasashe dangane da makomarsu bayan kammala wa'adinsu, ko dai a cikin jam'iyyunsu ko harkokin kasuwanci, ko kuma a wasu muƙaman gwamnati na gaba.
A wannan muƙala, za mu duba jerin gwamnonin Najeriya da ke kammala wa'adinsu a 2027 amma ba su nemi takarar Majalisar Dattawa ba.
Babagana Umara Zulum
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ne gwamnan ɗaya tilo daga yankin arewa maso gabashin Najeriya da bai nemi kowace irin takara ba a zaɓen 2027.
A wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar a cikin watan Mayu, Gwamna zulum ya ce ya sha matsin lamba daga magoya bayansa kan ya fito takarar majalisar dattawa, amma ya ƙi amincewa saboda fifita haɗin kan jam'iyyar kamar yadda ya bayyana.
Gwamna Zulum dai ya fito ne daga yankin Borno ta Tsakiya, wadda Sanata Kaka Shehu Lawan ke wakilta, kuma ya sake samun tikitin takarar ƙarƙashin jam'iyyar APC.
Babajide Sanwo-Olu
Gwamnan jihar Legas din wanda ke kammala wa'adin mulkinsa na biyu, bai nemi takarar komai da a zaɓen 2027 da ke tafe.
Tuni dai ya tsayar da mataimakinsa, Dr Obafemi Hamzat a matsayin ɗantakarar gwamnan jihar a zaɓen da ke tafe.
Sonwo-Olu ya fito ne daga yankin Legas ta Tsakiya, wadda Sanni Eshilokun Wasiu Olatunji ke wakilta a majalisar dattawan, kuma yanzu haka ma yake takarar a APC.
A tarihin jihar Legas tun bayan komawar Najeriyar mulkin dimokraɗiyya a 1999, babu gwamnan jihar ko ɗaya daga jihar da ya zama ɗanmajalisar dattawan.
Oluseyi Makinde
Gwamna Oluseyi Abiodun Makinde na jihar Oyo ne cikon gwamna na uku da bai nemi takarar majalisar dattawa ba a 2027.
A maimakon haka gwamnan bai barin gado ya tsaya ne takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ke tafen ƙarƙashin jam'iyyar APM, mai alamar rogo.
Masu sa ido na kallon takararsa a matsayin wani yunƙuri na faɗaɗa tasirinsa daga matakin jiha zuwa siyasar ƙasa baki ɗaya.
Wasu masu lura da al'amuran siyasa na ganin cewa rashin neman kujerar Majalisar Dattawa na iya nuna cewa waɗannan gwamnoni suna da wasu manyan tsare-tsaren siyasa na gaba, yayin da wasu kuma ke cewa hakan wata alama ce ta sauya salo a siyasar Najeriya, inda ba kowane mai barin gwamnati ne zai nemi wata kujera ta zaɓe nan take ba.