Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya janyo rashin jituwa tsakanin Wike da gwamnonin APC?
- Marubuci, Bashir Zubairu Ahamd
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC News Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Wani kwantaccen rikicin siyasa tsakanin ministan Abuja, Nyesom Wike da gwamnonin jam'iyyar APC ya fito fili a ranar Litinin bayan da Wike ya bayyana damuwarsa dangane da abin da ya bayyana da ƙoƙarin taɗe shi da gwamnonin ke yi.
Gwamnonin sun zargi Wike da yi wa jam'iyyarsu ta APC shiga hanci da ƙudundune duk da cewa shi ɗan jam'iyyar PDP ne, inda suke tuhumar sa da sauya baki bayan ya yi alƙawarin cewa zai taimaka wa APC daga sama har ƙasa.
Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Nyesom Wike dai ya sake jaddada goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa bai taɓa yin alkawarin cewa Jam'iyyar PDP ba za ta tsayar da 'yan takara a zaɓen gwamna da Majalisar Dokoki ta Ƙasa da Majalisun Dokokin Jihohi ba.
Babbar fargabar da gwamonin jam'iyyar ke yi ita ce wannan raba ƙafa da Wike ke yi na iya zama naƙasu ga makomar jam'iyyar a lokacin zaɓe.
Masu sharhi na ganin shi kansa shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu, na yi wa Wike kallon ƙadangaren bakin tulu.
Musayar yawu tsakanin Wike da Hope Uzodinma
A cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Kafofin Sadarwa na Zamani, Lere Olayinka, ya fitar, Nyesom Wike ya ce ba zai zama wanda zai taimaka wa gwamnoni su ci zaɓe a jihohinsu ba.
Ya ce, "siyasa ta fi karkata ne ga gida, don haka waɗanda ke da matsaloli a jihohinsu su warware su, maimakon amfani da sake zaɓen Shugaban Ƙasa wajen tayar da ƙura ko neman tausayin jama'a."
Wike ya bayyana cewa bai taɓa ganawa da APC ba kafin shi da sauran mambobin G5 su goyi bayan Shugaba Tinubu a zaɓen 2023. Ya ce a zaɓen 2027 ma, goyon bayansa ya ta'allaka ne kan Shugaban Ƙasa kawai.
Wani abu ma shi ne ya mayarwa gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma martani, inda shi Ministan ya ce siyasa a yanzu ba ta tsaya ga mutum ya taso daga matsayi na huɗu ya zama gwamna ba, sai dai ta shafi samun sahihin goyon bayan jama'a da kuma lashe zaɓe tun daga matakin rumfunan zaɓe.
A cewar Wike "Ina Jihar Imo a ƙarƙashin Gwamna Hope Uzodinma, ta yaya APC ta samu nasarar lashe kujerun Majalisar Dattawa guda biyu a 2023, a zaɓen da aka gudanar a rana guda da na Shugaban Ƙasa, alhali APC ta samu ƙasa da kashi 15 cikin 100 na ƙuri'un shugaban ƙasa? Shin Rainbow Coalition ne ya sa haka? Ko kuwa masu zaɓen sun rikice ne?"
Rawar da Wike ke takawa a jihohi
Masana sun bayyana matsayar ta Wike a matsayin abin da aka jima ana hasashen faruwar sa, kasancewar ɗan siyasa ne mai alƙibla biyu, kuma rikicinsa da gwamnonin APC ya daɗe da nuna haka.
Farfesa Abubakar Kari, malami a sashen nazarin kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja a Najeriya ya ce, ''ko ba daɗe ko ba jima za a kai wani mataki da Wike zai samu matsala da 'yan jam'iyyar APC, saboda mutum ne da zaɓi tsarin ungulu da kan zabo a siyasarsa''.
Shi ɗan jam'iyyar PDP ne amma ana amfani da shi ana ɓalɓalta jam'iyar gaba ɗaya ana rushe ta, saboda yana goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu'', in ji shi.
To amma a cewar Farfesa Kari, gwamnonin jam'iyyar APC na zargin Wike da shirya musu zagon ƙasa inda yake tsayar da 'yan takara a ƙarƙashin PDP masu ƙarfi domin su kara da su a matakin zaɓen gwamnoni da 'yan majalisar tarayya.
"Hakan ya sa gwamnonin ke ma sa kallon mai aƙida biyu, akwai misalai a jahohi da dama, alal misali a jihar Kwara ɗan takarar gwamnan jihar shi kansa akwai wata yarjejeniya tsakaninsa da Wike, hatta a jihar Gombe da ma Imo da sauran jihohi duka yana da 'yan takara da ya tsayar masu. Wato a gefe ɗaya yana yiwa Tinubu aiki a gefe ɗaya kuma yana yi wa APC zagon ƙasa", in ji Farfesa Kari.
Mene ne "Rainbow Coalition" da Wike ya kafa?
Rainbow Coalition wani sabon tsarin haɗin gwiwar siyasa ne da ake dangantawa da Ministan Abuja (FCT), Nyesom Wike, domin tattara magoya baya daga jam'iyyu daban-daban su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027.
An kira shi Rainbow Coalition ne saboda yana ƙoƙarin haɗa 'yan siyasa daga jam'iyyu masu launuka da manufofi daban-daban, ba tare da tilasta musu su bar jam'iyyunsu ba. A cewar Wike, mutum na iya kasancewa a PDP, APGA, LP ko wata jam'iyya, amma ya goyi bayan sake zaɓen Tinubu a matakin shugaban ƙasa.
Dangane da ƙawancen Rainbow Coalition ya ce hakan ba shi da wata alaƙa da Jam'iyyar APC, yana mai bayyana ƙawancen a matsayin wata kafa da jam'iyyun siyasa daban-daban da ke jin daɗin "kyawawan ayyukan" Shugaban Ƙasa suka haɗa kai a ƙarƙashinta domin mara masa baya wajen neman wa'adi na biyu.
Sai dai wannan yunƙuri ya haifar da muhawara saboda wasu shugabannin APC suna ganin tsarin zai iya:
- Haifar da rikicewa ga masu kaɗa ƙuri'a.
- Sa mutane su zaɓi Tinubu amma su ƙi zaɓen 'yan takarar APC a sauran mukamai.
- Ƙirƙirar wata kafa ta siyasa da za ta yi gogayya da tsarin APC a jihohi.
A saboda haka, gwamnonin APC ƙarƙashin jagorancin Hope Uzodimma sun bayyana cewa ba za su goyi bayan kowace haɗaka da za ta iya raunana APC ko 'yan takararta ba.
Me wannan ke nufi ga makomar Wike da jam'iyyun biyu?
Kasancewar Ministan na Abuja ya bayyana cewa jam'iyyarsa ta PDP za ta shiga zaɓuka ne kawai ba wai don ta yi nasara ba, kuma alamu sun nuna yadda a matakin tarayya jam'iyyar ta samu tasgaro saboda tarin rikice-rikicen da take fama da su, amma a matakin jihohi akwai saɓanin haka.
Farfesa Kari ya ce, "wannan wani lamari ne da ba za ta saɓu ba ga jam'iyyun na PDP da kuma APC ɗin".
Masana dai na ganin babu wata alama ta warware wannan taƙƙadama kasancewar shugaba Tinubu na kallon Wike a matsayin wanda zai taka gagarumar rawa wajen taimaka masa samun magoya baya da ɗimbin ƙuri'u a shiyar kudu maso kudancin ƙasar, inda ya ke ganin ci gaba da tafiya da shi zai haifar da alfanu a zaɓen 2027 mai zuwa.
Kazalika, a cewar masanin "idan aka kammala zaɓen 2027 muddin jam'iyyar APC ta samu nasara to akwai yiwuwar shugaba Tinubu zai watsar da Wike, domin ya riga ya biya buƙatarsa".
Me jam'iyyar APC ke cewa game da wannan lamari?
Gwamnonin da ke ƙarƙashin jam'iyyar APC sun nesanta kansu da ƙawancen siyasa na "Rainbow Coalition" da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ke jagoranta da zimmar goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Shugaban gwamnonin jam'iyyar kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana matsayar gwamnonin ne bayan wani taron sirri da gwamnonin APC suka gudanar a Abuja ranar Litinin.
Gwamnonin sun ce ba za su shiga ko su goyi baya ko su amince da duk wata ƙawance ko tsarin siyasa da zai iya raunana APC da yin illa ga 'yan takarar jam'iyyar ko kuma kawo cikas ga sake zaɓen Shugaba Tinubu ba.
Uzodimma ya ce gwamnonin APC za su mayar da hankali ne wajen tallafa wa 'yan takarar jam'iyyar a dukkan matakan zaɓen 2027.
Malam Bala Ibrahim shi ne Daraktan watsa labarai na jam'iyyar APC, ya shaidawa BBC cewa, "gwamnonin sun ce aje a yi duk mai yuwa domin a samu nasara, amma a ce za a ƙulla ƙawance a ci amanar 'ya'yan jam'iyya ba daidai ba ne, ita jam'iyya ba za ta yarda da wannan ba, su gwamnonin APC ba za su goyi bayan hakan ba" in ji shi.
Jam'iyyar dai ta kai matsayar cewa kowa ya je ya yi nasa ƙoƙari duk wanda ya samu nasara to shi ne zakara ba wai yin ungulu da kan zabo ba.