Amurka ta sanar da taƙaita biza ga jami'an Afirka ta Kudu
Amurka ta sanar da taƙaita bayar da takardun biza ga mutanen da ake zargi da nuna wariyar launin fata ga tsirarun farar fata a Afirka ta Kudu.
Wannan ce taƙaddama ta baya-bayan nan tsakanin ƙasashen biyu.
Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta soki Afirka ta Kudu kan batutuwa da dama da suka haɗa da manufofi da aka bijiro da su don magancenuna wariya.
Trump ya ce manufofin suna nuna wariya ga farar fata ƴan Afirka ta Kudu. Tuni dai Afirka ta Kudun ta musanta waɗannan zarge-zargen.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce gwamnatin Afirka ta Kudu ba ta warware matsalolin da ta bayyana ba, kamar yadda ya faɗa cikin wata sanarwa da ke ƙunshe da matakin.
Ya ce taƙaita bayar da bizar za ta shafi waɗanda ke tunzura wariyar launin fata.
Sai dai Rubio bai fito ya bayyana sunan waɗanda matakin ya shafa ba.