Mutum 12 sun mutu bayan ruftawar ginin a yaƙi ya shafa a Gaza
Aƙalla mutum 12 aka kashe har da ƙananan yara sannan wasu gommai sun yi ɓatan dabo bayan da wani rukunin gidaje ya rufa a zirin Gaza.
Jami'an ceto sun duƙufa wajen zaƙulo gawarwaki da kuma mutanen da ke da sauran numfashi waɗanda suka maƙale ƙarƙashin ɓuraguzai.
Rahotanni sun ce mutanen da yaƙin Isra'ila ya shafa ne ke zama a gidan mai hawa shida da ke yankin Tal al-Hawa, a kudu maso yammacin Gaza.
Hukumar tsaro ta bayyana cewa ta samu damar aro wasu manyan kayan aiki don taimakawa a ayyukan ceto.
Isra’ila ta ƙaƙaba takunkumi masu tsauri kan kayan aikin da za a iya shigar da su Gaza.
















