Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fitattun Sanatoci 10 da ba za su koma majalisar dattawan Najeriya a 2027 ba
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 8
Aƙalla ƴan majalisar dattawan Najeriya 35 ne suka rasa damar sake tsayawa takara a zaɓen 2027 da ke tafe a ƙasar.
Wasu daga cikinsu sun samu tikitin takarar gwamna ne, yayin da wasu suka samu saɓani da jam'iyyunsu har ta kai ga an hana su tikitin takara ko kuma suka fice daga jam'iyyar.
Wasu kuma sun janye daga takarar ne da raɗin kansu.
Majalisar Dattawa ta Najeriya na da sanatoci 109, uku daga kowace jiha 36 da ke ƙasar, da kuma ɗaya da ke wakiltar Babban Birnin Tarayya Abuja.
Yayin da za a shiga Majalisa ta 11 bayan wa'adin Majalisa ta 10 ya ƙare, ana sa ran ganin sabbin fuskoki da kuma wasu tsoffin gwamnonin jihohi a Majalisar Dattawar.
Hukumar zaɓe ta ƙasar, INEC, ta fitar da sunayen ƴan takarar kujerun Sanata a dukkan mazaɓun Sanata 109 na ƙasar a makon da ya gabata, kamar yadda jam'iyyun siyasa suka gabatar mata.
Hakan ya sa BBC ta yi nazari kan wasu fitattun Sanatocin da ba za su sake neman lashe kujerunsu ba a zaɓen 2027.
1. Aminu Tambuwal
Sanata Aminu Waziri Tambuwal, wanda ke wakiltar mazabar Sokoto ta Kudu tun daga 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, ya fice daga jam'iyyar ya koma ADC a farkon shekarar 2026.
Ya sanar da cewa ya janye daga neman sake takarar kujerar Sanata ne yayin wani taron da jam'iyyar ADC ta gudanar domin sasanta rikicin fitar da ƴan takararta a jihar Sokoto.
A yanzu Faruk Malami Yabo ne zai yi wa ADC takarar kujerar Sanatan Sokoto ta Kudu a zaɓen 2027.
Tambuwal tsohon gwamnan jihar Sokoto ne, kuma ya taɓa riƙe muƙamin Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya.
2. Danjuma Goje
Tsohon gwamnan jihar Gombe kuma Sanatan da ke wakiltar Gombe ta Tsakiya, Muhammad Ɗanjuma Goje, ya ce ya ɗauki rashin samun tikitin sake takarar Sanata a ƙarƙashin jam'iyyar APC a matsayin ƙaddarar rayuwa.
APC ba ta ba shi tikitin takara a zaɓen 2027 ba, a wani mataki da aka danganta da saɓanin da ke tsakaninsa da Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya. A yanzu Mohammed Ahmed ne zai yi wa jam'iyyar takarar kujerar da Goje ke kai.
A wata hira da BBC, Sanata Goje ya ce Gwamna Inuwa Yahaya ba shi da ikon yin masa ritaya daga siyasa.
Bayan rashin samun tikitin, an yi ta hasashen cewa Goje, wanda yana daga cikin jiga-jigan siyasar Gombe, zai iya sauya sheƙa zuwa wata jam'iyya domin ci gaba da fafutukar siyasarsa.
Sai dai duk da rashin samun tikitin APC, tsohon gwamnan ya ce zai ci gaba da mara wa jam'iyyar baya domin ganin ta samu nasara a zaɓen 2027.
3. Rufai Sani Hanga
Sanata Rufai Sani Hanga na ɗaya daga cikin makusantan jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kuma yana wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya.
Hanga ya lashe zaɓen Sanata na 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, kafin daga bisani su samu saɓani da jam'iyyar ya bi Kwankwaso zuwa ADC. Daga nan ne suka koma sabuwar jam'iyyar NDC, wadda ta haɗa wasu daga cikin manyan ƴan siyasar adawa, ciki har da Peter Obi, wanda ake sa ran zai yi wa jam'iyyar takarar shugaban ƙasa.
Sai dai dangantakarsa da NDC ta yi tsami bayan da bai samu tikitin sake takarar kujerar Sanata ba, lamarin da ya haifar da cece-ku-ce.
Daga bisani Hanga ya koma jam'iyyar APC mai mulki, amma ba zai sake neman kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya a zaɓen 2027 ba.
A jerin ƴan takarar da INEC ta fitar, Nasiru Yusuf Gawuna ne zai nemi kujerar da Hanga ke kai a yanzu a NDC yayin da Sanata Ibrahim Shekarau zai nemi kujerar a APC.
4. Ned Nwoko
Sanata Chinedu Munir Nwoko, wanda aka fi sani da Ned Nwoko, na daga cikin sanatocin da ba za su koma Majalisar Dattawa a 2027 ba, bayan da ya rasa tikitin jam'iyyar APC na sake neman kujerar Delta ta Arewa.
Nwoko ya lashe kujerar a zaɓen 2023 ne a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, kafin ya fice daga jam'iyyar ya koma APC, gabanin zaɓen fidda gwani na jam'iyyar.
Sai dai duk da komawarsa APC ba ta ba shi tikitin ba. A zaɓen fidda gwani na jam'iyyar da aka gudanar a watan Mayun 2026, tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya doke Nwoko, inda ya samu tikitin APC na takarar Sanatan Delta ta Arewa a zaɓen 2027.
Nwoko na daga cikin fitattun ƴan siyasar Najeriya da ake yawan magana a kansu, kuma ya shahara a siyasa saboda yana auren fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Regina Daniels.
5. Ahmed Aliyu Wadada
Sanata Ahmed Aliyu Wadada, wanda ke wakiltar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Dattawa, yana daga cikin sanatocin da ba za su sake neman kujerarsu ba a zaɓen 2027, bayan ya samu tikitin jam'iyyar APC na takarar gwamnan jihar Nasarawa.
Wadada, wanda ya lashe kujerar Sanata a 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar SDP, ya koma APC, inda Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana shi a matsayin wanda yake son ya gaje shi a matsayin gwamna.
Matakin na gwamna Sule ya haifar da ce-ce-ku-ce a jihar, musamman saboda ya sanar da matakin tun kafin Wadada ya kammala komawa APC, lamarin da ya sa wasu ke kallon abin a matsayin wata yarjejeniya ta siyasa tsakanin gwamnan da sanatan saboda sun fito ne daga mazaɓa ɗaya.
A cewar masu irin wannan fahimta, yayin da Sule ke kammala wa'adinsa na biyu kuma ba zai sake tsayawa takarar gwamna ba, Wadada zai gaje shi a takarar APC, yayin da Sule zai yi takarar Majalisar Dattawa bayan barin kujerar gwamna.
6. Umar Shehu Buba
Sanata Shehu Buba Umar, wanda ke wakiltar Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya, na daga cikin sanatocin da ba za su nemi kujerarsu ba a zaɓen 2027, bayan da ya koma takarar gwamnan jihar Bauchi.
Buba ya lashe kujerar Sanata ne a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar APC, amma ya rasa tikitin jam'iyyar na zaɓen 2027 bayan rikici da ya biyo bayan zaɓen fidda gwani na APC a jihar.
Bayan rashin samun tikitin, Buba ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PRP a watan Mayun 2026, inda daga bisani aka tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar jam'iyyar na gwamnan Bauchi a 2027.
7. Ibrahim Lamido
Sanata Ibrahim Lamido, wanda ke wakiltar Sokoto ta Gabas a Majalisar Dattawan Najeriya, na daga cikin sanatocin da ba za su sake neman kujerarsu ba a zaɓen 2027.
Lamido ya lashe kujerar ne a ƙarƙashin jam'iyyar APC a zaɓen 2023, kafin ya fice daga jam'iyyar a watan Afrilun 2026 ya koma jam'iyyar ADC. Ya ce rashin jituwa da rikice-rikicen cikin gida a APC na daga cikin dalilan da suka sa ya bar jam'iyyar.
Bayan komawarsa ADC, Lamido ya nemi tikitin jam'iyyar na takarar gwamnan jihar Sokoto a 2027.
Sai dai bai samu tikitin ba, bayan da ADC ta cimma matsaya ta goyon bayan tsohon mataimakin gwamnan Sokoto, Mannir Dan'iya. Duk da rashin samun tikitin, Lamido ya ce zai ci gaba da kasancewa a ADC tare da mara wa ɗan takarar jam'iyyar baya.
Kafin hakan ma, Lamido ya sanar da cewa ba zai nemi sake komawa Majalisar Dattawa ba, inda ya ce kujerar Sanata ba ta da ikon zartarwa da ake buƙata wajen magance matsalar tsaro da ke addabar al'ummarsa.
8. Nasiru Sani Zangon Daura
Sanata Nasiru Sani Zangon Daura, wanda ke wakiltar Katsina ta Arewa a Majalisar Dattawan Najeriya, ya rasa tikitin takara a jam'iyyar APC na sake neman kujerar.
Zangon Daura ya lashe kujerar ne a zaɓen 2023, bayan ya doke Sanata Ahmad Babba Kaita, wanda yake kan kujerar a lokacin.
Sai dai a zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar a watan Mayun 2026, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Nasir Yahaya-Daura, ya lashe tikitin jam'iyyar na takarar Sanatan Katsina ta Arewa
Hakan na nufin Zangon Daura ba zai sake neman kujerar da yake kai ba a zaɓen 2027.
9. Mohammed Ogoshi Onawo
Sanata Mohammed Ogoshi Onawo, wanda ke wakiltar Nasarawa ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya, zai yi takarar gwamnan jihar Nasarawa a jam'iyyar APM a 2027.
Onawo ya lashe kujerar Sanatan Nasarawa ta Kudu a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, inda ya doke tsohon gwamnan jihar, Tanko Al-Makura, na APC.
Daga baya ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar ADC, kafin kuma ya koma APM, da a yanzu zai mata takarar gwamnan jihar.
10. Sharafadeen Alli
Sanata Sharafadeen Abiodun Alli, wanda ke wakiltar Oyo ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya, na daga cikin sanatocin da ba za su sake neman kujerarsu ba a zaɓen 2027, bayan ya samu tikitin jam'iyyar APC na takarar gwamnan jihar Oyo.
A watan Afrilun 2026 ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan Oyo, kafin daga bisani ya samu goyon bayan shugabannin jam'iyyar a jihar. A watan Mayu kuma ya samu tikitin APC bayan ya yi nasara a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar.
APC ta bayyana Alli a hukumance a matsayin ɗan takararta na gwamna a zaɓen 2027, yayin da Aderemi Oseni ya samu tikitin jam'iyyar na neman kujerar Sanatan Oyo ta Kudu da Alli zai bari.
Saura Sanatocin da suka rasa tikitin takara a 2027
- Aminu Iya Abbas — Adamawa ta Tsakiya — zai yi takarar gwamna a Adamawa
- Amos Yohanna — Adamawa ta Arewa
- Samaila Dahuwa Kaila — Bauchi ta Arewa
- Benson Agadaga — Bayelsa ta Gabas
- Eteng Jonah Williams — Cross River ta Tsakiya
- Neda Bernards Imasuen — Edo ta Kudu
- Cyril Fasuyi — Ekiti ta Arewa
- Ezenwa Francis Onyewuchi — Imo ta Gabas
- Osita Izunaso — Imo ta Yamma
- Khabeeb Mustapha — Jigawa ta Kudu maso Yamma
- Yahaya Abubakar Abdullahi — Kebbi ta Arewa
- Jibrin Isah (Echocho) — Kogi ta Gabas
- Sadiq Suleiman Umar — Kwara ta Arewa
- Lola Ashiru — Kwara ta Kudu
- Godiya Akwashiki — Nasarawa ta Arewa
- Gbenga Daniel — Ogun ta Gabas
- Solomon Olamilekan Adeola (Yayi) — Ogun ta Yamma — zai yi takarar gwamna a Ogun
- Francis Adedayo Faduyile — Ondo ta Kudu
- Olubiyi Fadeyi — Osun ta Tsakiya
- Lere Oyewumi — Osun ta Yamma
- Abdulfatai Buhari — Oyo ta Arewa — zai yi takarar gwamna a Oyo
- Diket Plang — Plateau ta Tsakiya
- Pam Dachungyang — Plateau ta Arewa
- Ipalibo Gogo Banigo — Rivers ta Yamma
- Emmanuel Nwachukwu — Anambra ta Kudu