Gwamnatin Sokoto ta rufe masallacin Sheikh Musa Lukuwa
Gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da rufe masallacin Juma’a na Musa Lukuwa har sai yadda hali ya yi bayan tashin hankalin da ya faru a makon da ya gabata inda wani matashi ya daɓawa malamin wuƙa.
Cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar, gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne domin bayar da damar yin bincike kan harin da aka kai tare da kisa.
Sanarwar ta kuma ce gwamnati ta kafa kwamitin malamai domin gudanar da bincike kan musabbabin rikicin inda kuma ake sa ran kwamitin zai bai wa gwamnati shawarwari kan matakan da suka dace a ɗauka.
Gwamnatin ta kuma nesata kanta daga duk wani al'amari na fakewa da addini don yin ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.
Sanarwar ta yi kira ga al’ummar jihar da su guji furta kalamai masu tayar da hankali da ka iya tunzura jama’a da kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan al'ummar jihar.
Malam Musa Ayuba Lukuwa malamin addinin Musulunci ne a jihar Sokoto da ke bin fahimtar Ahlussunnah Wal Jama'a.
Yana daga cikin malamai masu yawan janyo taƙaddama musamman dangane da al'amura masu sarƙaƙiya.