Karatu don nishaɗi na da alaƙa da ingantacciyar lafiyar ƙwaƙwalwa - Bincike

Asalin hoton, Getty Images
Masu bincike a Birtaniya sun gano cewa yin karatu don nishaɗi na da alaƙa da samun ingantacciyar lafiyar ƙwaƙwalwa, da rage damuwa da kuma rage yiwuwar kamuwa da cutar mantuwa.
A cikin wani sabon nazari da suka yi bayan tattara hujjoji da dama ciki har da takardun bincike, da sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a da kuma hotunan binciken ƙwaƙwalwa, masana kimiyyar daga Jami’ar Cambridge sun bayyana cewa yin karatu akai-akai, ko da kuwa wane irin littafi ne, na iya samar da fa’idojin lafiya a kowanne mataki na rayuwa.
Ɗaya daga cikin sakamakon binciken, wanda ya shafi matasa sama da dubu goma, ya nuna cewa waɗanda suka fara karatu don nishaɗi tun suna ƙanana, sun fi kwakwalwa sosai da mayar da hankali a kan karatu.
Binciken ya kuma nuna cewa irin waɗannan matasa sun fi samun nasara a makaranta, idan aka kwatanta da takwarorinsu da ba sa yawan karatu don nishaɗi.

















