Atletico da Juventus na harin Madueke, Liverpool na son Wanner

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Atletico Madrid da Juventus na duba yiwuwar ɗaukar ɗan ɗan wasan Arsenal Noni Madueke matsayin ɗan wasan Aro. (Caught Offside)

Liverpool, da Bayern Munich da Real Madrid na son ɗan wasan PSV Eindhoven Paul Wanner. (Teamtalk)

Lazio ta koma teburin tattaunawa da dan wasan Ajantina Mauro Icardi, da ke zaman kansa bayan ya bar Galatasaray, sannan ƙofar sa a buɗe take ga sabbin damarmaki. (Sky Sports Italia)

Ana danganta Everton da Icardi, amma shugaban Toffees David Moyes , na janƙafa wajen shiga tattaunawa a matsayin ɗan wasan mai zaman kansa. (Football Insider)

Crystal Palace na son sabuntawa mai tsaron ragar Ingila Dean Henderson, kwantaraginsa, don tsawaita zamansa a ƙungiyar. (The Athletic - subscription required)

Nottingham Forest ta kammala shirye-shiryen ɗaukar ɗan wasan gaba na Shamrock Rovers, Michael Noonan, inda za ta biya kuɗin horon da aka ba shi, kafin komawarsa ƙungiyar a watan Janairu. (Irish Mirror)

Inter Milan na tattaunawa kan yiwuwar tsawaita kwanataragin ɗan wasan Italiya Federico Dimarco, da ɗan wasan Turkey Hakan Calhanoglu. (Football Italia)

Tsohon dan wasan gaban Faransa Karim Benzema, ya tattauna da ƴan wasan Bayer Leverkusen inda ya ke neman sabuwar ƙungiyar da zai koma taka leda bayan ya bar Al-Hilal a kakar wassani. (Fichajes - in Spanish)