Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kuskuren VAR: Me ya sa ba a soke ƙwallon Haaland ba?
Manchester City ta doke Manchester United da ci 1-0 a Old Trafford ranar Lahadi a Premier League, amma abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne ƙwallon da Haaland ya ci, wadda ta bai wa City damar haɗa maki uku.
Kuskuren ya faru ne, bayan da na'urar da take taimaka wa alƙalin wasa wajen yanke hukunci, VAR ta tabbatar da cewar ƙwallon da Haaland ya buga ta shiga raga.
Sai kwamitin kula da yadda alƙalan gasar Premier League suka sanar an samu kuskuren hukunci kan ƙwallon da Haaland ya zura a ragar Manchester United a wasan hamayya.
Hakan ne ya sake buɗe cece-kuce musamman tsakanin masu bibiyar tamaula da kuma a kafafen sada zumunta kan me ya sa idan aka samu yin kuskure a wasan tamaula ba a soke sakamakon ko a sake buga karawar?
Tun farko mataimakin alƙalin wasa ya ɗaga tuta mai ruwan ɗorawa da cewar an yi satar gida, amma sai VAR ta shiga tsakani sannan aka sauya hukuncin, aka amince da ƙwallon.
Ƙwamitin ya ce ya kamata VAR ta bai wa Michael Oliver shawarar ya sake duba abin da ya faru, musamman saboda gurbin da Enzo Fernández yake da yadda ya yi ƙoƙarin taɓa ƙwallon, sannan da gurbin da Haaland ya ke shi kansa.
To me ya sa, duk da sanarwar cewa an samu kuskuren yanke hukunci, amma ba za a sake wasan ba ko soke ƙwallon da aka ci?
Ga abubuwan da ya kamata ku sanu kan irin wannan lamarin.
Me ya faru kan ƙwallon da Haaland ya ci?
A minti na 60, Josko Gvardiol ya buga ƙwallo zuwa cikin yankin gidan Manchester United, inda Haaland ya samu damar buga kwallon cikin daga.
Tun farko mataimakin alkalin wasa daga daga gefen fili ya ɗaga tuta, saboda cewar an yi satar gida.
Daga nan sakamakon ya zama takaddama, sai da aka je duba, VAR, wadda ta ce Haaland baya gurbin satar gida - sai dai wata tambayar ita ce wane wuri Enzo Fernandez yake kafin a zura ƙwallon a raga?
Kamar yadda aka nuna bidiyon abin da ya faru, ɗan wasan City, Enzo Fernandez na gurbin satar gida, harma ya yi ƙoƙarin taɓa ƙwallon da kai a lokacin yana kwance a ƙasa, amma bai samu ba, amma gurbin da yake da yunƙurin da ya yi suna da muhimmaci da ya kamata a duba ba na Haaland ba - abubuwan da suka jawo cece-kucen kenan.
Kuma VAR ta yanke hukuncin Fernández bai yi katsalandan ba, don haka ƙwallon ta halas ce.
Daga baya kwamitin kula da aikin da alƙalan wasan Premier League suka gudanar ya ce wannan shi ne kuskuren da ya kamata a sake dubawa a karawar.
Me ya sa kwamitin raflin ya ce an yi kuskure?
Matsalar ba ita ce Haaland yana gurbin satar gida ba, ɗan wasan Norway yana mataki mai ƙyau.
Laifin da ake gani shi ne Fernandez yana gurbin satar gida da kuma yadda ya yi ƙoƙarin saka wa ƙwallon da tazararsa da mai tsaron bayan United, Lisandro Martínez.
Ƙwamintin ya ce VAR ba ta yi la'akari yadda ya kamata kan tasirin Fernández a wannan yanayin, sai ta tsaya kan gurbin da Haaland ya ke.
Saboda haka, maimakon a tabbatar da hukuncin, ya kamata ta bai wa raflin shawarar ya je ya sake duba lamarin a bidiyo.
Wannan shi ne abin da ƙwamitin ya tabbatar da kuskuren da aka yi.
Me ya sa idan an yi kuskure, ba a soke wasan?
Wannan shi ne abin da mutane da dama ke neman samun amsa.
Amincewa da cewar alkalin wasa ya yi kuskure ba yana nufin za a soke karawar ba, ko kuma sakamakon wasan ba shi da inganci.
A ƙwallon ƙafa, akwai bambanci tsakanin, kuskuren da aka yi yayin wasa da kuskuren da aka gano bayan an kammala wasa da kuma yanayin da dokokin gasar suka tanadi sake buga wasa.
Idan aka kammala wasa bisa tsarin gasar, kuskuren alƙalin wasa ko na VAR da aka gano daga baya, baya nufin kai tsaye za a soke sakamakon ko sake karawar.
Saboda haka, sakamakon wasan da Manchester City ta yi nasara 1-0 a Old Trafford yana nan yadda yake.
Ƙwamitin da ke ƙarƙashin Fifa, da ke tsara dokokin ƙwallon ƙafa, IFAB ya bayyana cewa alƙalin wasa shi ne ke da ikon yanke hukunci na ƙarshe, yayin da VAR ke taimaka masa kan dokokin da aka tanadarwa na'urar.
Shin za a iya hukunta rafli ko mai kula da VAR kan yin kuskure?
Wannan shi ne inda tsarin ya fi bambanta da abin da wasu magoya baya ke tunani.
Ba lallai ne a hukunta kuskuren da rafli ya yi, musamman idan aka gano hakan bayan da aka kammala fafatawa.
Ga jerin abubuwan da za a yi masa:
- Za a iya cire jami'in daga wasu wasanni
- Za a iya hana shi aikin VAR na wani lokaci
- Za a iya sake duba yadda ya gudanar da aikinsa cikin natsuwa
- Za kuma a iya tura shi ya je ya ƙara samun horo
- Ko kuma a ɗauki wasu matakan kan ayyukansa na gaba
Irin haka ta taɓa faruwa a karawar Manchester United da Wolves a 2023, inda aka hana Wolves bugun fenarit, sakamakon taho mu gama da mai tsaron ragar United, André Onana ya yi da ɗan wasan Wolves, Sasa Kalajdzic.
Daga baya kwamitin ya amince cewa hukuncin fenariti ya kamata a bayar.
Hakan ya sa alƙalin wasa, Simon Hooper da mai kula da VAR, Michael Salisbury da Richard West ba a ba su aikin jan ragamar wasan Premier League a karshen makon gaba ba.
Wannan yana nuna cewa ana iya samun kuskuren alƙalanci, amma ba lallai ne sakamakon wasan ya canza ba.
Ga misalin abin da ya faru a baya irin haka
Luis Díaz da Tottenham
Idan ana neman misalin da ya fi nuna wannan matsalar, to lamarin Luis Díaz lokacin yana Liverpool shi ne ɗaya daga cikin hukuncin da aka yi kuskure da ya shahara.
A wasan da Tottenham da karɓi baƙuncin Liverpool a watan Satumba a 2023, Díaz ya zura ƙwallo cikin ragar masu masaukin baƙi, amma sai aka daga tuta da cewar an yi catar gida. Kuma VAR ta kasa gyara hukuncin.
Daga baya kwamitin da yake kula da yadda alkalan Premier Leagye suke gudanar da aikin, ya sake bibiyar karawar gabakin ɗayanta, daga nan ne suka sanar da cewar an yi babban kuskure da aka hana ƙwallon.
An kuma fitar da tattaunawar da aka yi tsakanin alkalin wasa da mai kula da na'urar, VAR domin a tantance yadda aka yi kuskuren.
Haka kuma lamarin ya yi tasiri sosai a wasan da ta kai Liverpool ta yi rashin nasara da ci 2-1, amma ba a sake wasan ko soke sakamakon ba.
Wannan shi ne babban misalin da ke nuna cewa koda ana samu kuskure wajen alkalanci wasa babu batun soke sakamako, ko a sanar da cewar a sake fafatawar.
Wasan Arsenal da Brentford
A watan Fabrairun 2023, Arsenal ta tashi 1-1 da Brentford.
Brentford ta ci ƙwallon da karawar ta tashi kunnen doki 1-1, amma daga baya aka gano cewa Christian Nørgaard yana satar gida, kafin Ivan Toney ya ci ƙwallon.
Kuma VAR ta kasa yin cikakken binciken lamarin.
Howard Webb, shugaban kwamitin alkalan na Premier League a lokacin, ya tuntubi Arsenal ya sanar da ita an yi kuskuren alkalanci a karawar, sannan ya yi mata bayani kan abin da ya faru.
Amma kuma Arsenal ba ta samu maki uku ba, kuma ba a sake wasan ba, sakamakon ya ci gaba da zama 1-1.
Hakan ya sa Mikel Arteta ya nuna cewa irin waɗannan kuskuren na iya yin tasiri sosai wajen neman lashe babban gasar.
Brighton ma ta fuskanci irin wannan lamarin
Brighton ma ta samu kanta a irin wannan yanayi.
An yi kuskure wajen zana layin offside a wasan Brighton da Crystal Palace, abin da ya sa aka soke ƙwallon da Brighton ta zura a raga.
Daga baya Howard Webb ya nemi afuwar Brighton.
Jami'in da ya kula da VAR a karawar, John Brooks ba a saka shi cikin wasau wasannin Premier League ba, saboda abinda ya faru.
Don haka abin da ya faru da Haaland ba sabon abu ba ne.
Abin da ya bambanta shi shi ne cewa yanzu ana amfani da fasahar VAR da ƙarin bayanin jama'a game da yadda aka yi alkalancin wasanni.
Me ya sa ake neman afuwa bayan an yi kuskuren alkalancin wasa?
Wannan ya shafi yadda kwamitin alkalan wasannin ya canza tsarin sadarwa ga ungiyoyi da kuma jama'a.
A ƙarƙashin mulkin Howard Webb, ana bayar da mahimmacin kan bayyana wa ungiyoyi da magoya baya dalilin da ya sa aka yanke wasu hukunci.
Akwai kuma shirin da bayanai da ake kira Match Officials: Mic'd Up, inda Webb ke nazarin wasu muhimman abubuwan da suka faru da kuma tattaunawa kan hukuncin da VAR ta gudanar. Premier League ma ta wallafa irin waɗannan bayanai domin ƙara fahimtar aikin jami'an alkalancin tamaula.
Saboda haka wannan bayanai kan fito ne daga kwamitin da yakan ce:
- Mun yi kuskure.
Abinda suke nufi:
- Bayan nazari, mun gano cewa hukuncin da aka yanke bai dace da abin da ya kamata a yanke ba.
Shin a Premier League kaɗai ake samun irin wannan kuskuren?
Kuskuren alkalanci abu ne da ke faruwa a ƙwallon ƙafa a faɗin duniya.
Amma Premier League na daga cikin gasar da ake bayar da cikakken bayani kan irin waɗannan abubuwa saboda yawan amfani da VAR, yawan kyamarori, girman gasar da kuma matsin lambar kafafen yaɗa labarai.
Musammaan a Ingila, ana ƙara ƙoƙarin bayyana kurakuran rafli ga jama'a, ciki har da nazarin VAR da fitar da wasu bayanan tattaunawa tsakanin Alkalan da suka busa karawar.
Saboda haka ba wai a Ingila kaɗai ake samun kuskure ba, kawai a can ake bitar aikin aikin da rafli suka gudanar, sannan a sanar da ƙungiyoyi da jama'a kan ingancinsu.