Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Litinin 14/09/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. A gargaɗi ƴan Zambiya kan cin mushen dabbobi sakamakon cutar anthrax

    Hukumomi a Zambiya sun gargaɗi ƴan ƙasar da su guji cin naman dabbobin daji bayan da dabbobi da dama suka mutu sakamakon cutar anthrax.

    Wani jami'i na hukumar kare afkuwar bala'i ya ce a ƙarshen makon da ya gabata, mutum 12 ne suka kamu da cutar bayan da suka ci naman dabbobin a yankin kogin Munyamadzi.

    Jami'in ya yi kira ga jama'a da su guji cin naman dabbobin da ba a tantance dalilin mutuwarsu ba.

    Zuwa yanzu jami'ai ba su tantance girman ɓarkewar cutar a baya-bayan nan ba inda ake ci gaba da sa ido da kuma gwaji a ɗakin gwaje-gwaje.

    A shekarar 2023, ƙasar ta yi fama da ɓarkewar cutar da ba a yi tunani ba, har ta kai mutum huɗu sun mutu sannan kuma ta bazu zuwa larduna tara cikin 10.

  2. Sojoji sun gano lita 10,000 na mai da aka 'tace ta haramtacciyar hanya' a Rivers

    Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta ce ta bankaɗo wani wajen ajiyar albarkatun mai ɗauke da lita 10,000 na man da ake zargin an tace ta haramtacciyar hanya.

    Cikin wata sanarwa ta Daraktan Yada labarai na rundunar, Abiodun Folorunsho, an yi bankaɗar ce a samamen da dakaru suka kai a ranar Asabar don daƙile satar ɗanyen mai a yankin Eleme Express na jihar Rivers.

    Ana zargin an samo man ne daga wani waje nesa da yankin wanda kuma aka ajiye domin sayarwa mutane.

    Rundunar ta ce an gano man cikin jarkoki 400 wadda kowace jarka ke ɗauke da mai lita 25 a ciki sai dai kuma babu wata haramtacciyar matata da aka gano a wajen.

    A cewar rundunar, baya ga bankaɗar, dakaru sun yi nasarar tarwatsa wata muhimmiyar cibiya ta samar da mai ta ɓarauniyar hanya.

    Sanarwar ta ƙara da cewa jami'an ba su samu cafke kowa ba kasacewar masu hada-hada a cibiyar sun tsere a lokacin da sojoji suka yi dirar mikiya a wajen.

  3. Yadda za ku sayi hannun jari

    A ranar Litinin ɗin nan ne matatar Ɗangote ta fara sayar da hannun jarin da ta ce za ta sayar ga al'ummar Najeriya domin bai wa duk wani ɗan ƙasar damar mallakar wani kaso a kamfanin.

    Kamfanin wanda zai sayar da hannayen jari guda biliyan 4.1 a kan farashin naira 525 kowane hannu, za a rufe sayarwar ne a ranar 13 ga watan Oktoban 2026.

    Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya sanar da cewa matatar man fetur ɗin nasa za ta fara sayar da hannayen jari ga jama'a ta hanyar Initial Public Offering (IPO), inda aka tsara bai wa kowa damar mallakar kaso a cikin kamfanin ko da da ƙaramin jari ne.

    Wannan cigaba ne da ya buɗe sabuwar tattaunawa kan muhimmancin kasuwar hannun jari da kuma damar da take samarwa ga matasa masu son gina makoma mai ɗorewa.

    Hakan ya sa ƴan Najeriya ke yin tambayoyi dangane da hanyoyin da ya kamata su bi domin sayen hannun jari a duk lokacin da irin wannan dama ta bujuro musu ba ma lallai a matatar Ɗangote kaɗai ba.

    Da yake sharhi kan wannan dama, Dr Salihu Lukman, Mataimakin Farfesa a University of Hafr Al Batin da ke ƙasar Saudiyya, ya ce kasuwar hannun jari na daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen tara dukiya cikin tsari da kuma dogon lokaci.

    Ku latsa nan domin samun bayani kan hanyoyin da ake bi don sayen hannun jari da ma samun ƙarin bayani.

  4. Hatsarin mota ya halaka aƙalla mutum 21 a Afirka ta Kudu

    Wani hatsarin mota ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 21 a Lardin Western Cape da ke Afirka ta Kudu.

    Jami'ai sun ce mutane da dama sun ji rauni a hatsarin da ya afku kusa da garin Prince Albert mai nisan kusan kilomita 300 daga Cape Town.

    Hukumomin Lardin sun rufe babbar hanyar lamarin da ya janyo cunkoson ababen hawa.

  5. Saudiyya ce ta nemi a soke tattaunawar Oman - Iran

    Kakakin ma'aikatar harkokin Iran Esmail Baghaei ya ce an soke tattaunawar a aka tsara yi a Oman tsakanin Iran ɗin da wasu ƙasashen Gulf bisa buƙatar da Saudiyya ta nema.

    Wannan wata dama ce da aka bai wa Iran da Oman kuma ana sa rai cewa ƙasashen yankin za su ci moriya da kuma una godiya ga hakan, kamar yadda Baghaei ya shaida.

    Ministocin harkokin wajen Iran da Oman sun sanar da soke tattaunawar a daren jiya kuma zuwa yanzu ba a sanar da ranar da za a yi tattaunawar ba.

    Sanarwar soke taron dai ta sa farashin ɗanyen mai ya zarce dala 108 kan kowace ganga guda.

  6. Iran ta kakkaɓo jirgi mara matuƙi a Mashigar Hormuz

    Rundunar Juyin juya halin Iran ta ce ta harbo wani jirgi mara matuƙi a Mashigar Hormuz.

    Kamfanin dillancin labarai na IRIB ya ruwaito cewa dakarun IRGC ne suka kakkaɓo jirgin na MQ-1 a Mashigar ta Hormuz.

    Kakakin rundunar ya ce sabon makaman tsaron sararin samaniyar IRGC ne suka harbo jirgin ruwan tare da lalata shi.

    Zuwa yanzu IRGC ba ta yi ƙarin bayani game da batun ba.

  7. Boko Haram ta lalata aƙalla makarantu 5000 a Borno - Zulum

    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce Boko Haram ta lalata gine-ginen makarantu aƙalla 5,000, lamarin da ya sa yara miliyan 2.2 ba sa zuwa makaranta a lokacin da rikicin ta'addanci ya yi ƙamari.

    Gwamna Zulum ya bayyana waɗannan alƙaluma ne a lokacin ƙaddamar da wasu ayyuka a Maiduguri, jiya Lahadi.

    Kakakin gwamnan, Malam Dauda Iliya, ya shaida wa BBC cewa gwamna Zulum ya duƙufa wajen ganin an shawo kan matsalar tsaron tare da inganta fannin ilimi ganin irin girman ɓarnar da Boko Haram ta yi wa ɓangaren.

    A cewar kakakin, gwamnan ya gina azuzuwa kusan 5000 da gina wasu makarantu 129 sannan kuma ana sa ran kammala wasu 140 daga nan zuwa ƙarshen mulkinsa.

    Ya ce akwai yara sama da miliyan ɗaya da dubu 800 da suke makaranta saɓanin lokacin da gwamna Zulum ya karɓi mulki inda a lokacin yara dubu 800 ne kaɗai suke zuwa makaranta.

    Gwamna Zulum ya bayyana cewa Boko Haram ta kashe malamai da jami'an kula da makarantu da dama musamman a lokacin da yaƙin ya yi ƙamari.

    Zulum ya ce gwamnatinsa ta ware dala miliyan 35 a tsakanin shekarar 2025 da 2026 don inganta ilimin pramare da sakandare.

  8. 'Za a yi makonni kafin tantance waɗanda gobarar jirgin ruwan Philippine ta shafa'

    Hukumomi a Philippine sun ce za a iya ɗaukan makonni ko ma watanni kafin tantance mutanen da gobarar jirgin ruwa ta shafa a makon da ya gabata.

    Lamarin dai ya yi sanadin mutuwar mutum 76.

    "Akasarinsu sun ƙone sosai," in ji Richard Allan Mangalip, wani ƙwararren jami'in bincike a hukumar ƴansandan Philippine.

    An nemi iyalan mutanen da su taimaka wajen tantance su ta hanyar gwajin DNA da kuma wasu kayayyaki da suka mallaka.

    Jirgin ruwan ƙirar MV June Aster ya nufi Coron ne daga Manila a Lardin Palawan, wani fitaccen wajen zuwa hutu, a lokacin da gobarar ta tashi ta inda ake ajiye kaya sannan kuma ta yaɗu zuwa sassan jirgin.

    Mutum 43 ne suka tsira yayin da wasu 13 kuma har yanzu ba a san inda suke ba, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

    Jami'in ya ce suna ta ƙoƙarin abubuwan da za su taya su tantance mutanen sai dai a cewar shi zai yi wuya a iya bayar da wa'adi na tsawon lokacin da za a ɗauka na tantancewar - "zai iya kai wa makonni, ko ma watanni".

    Wani jami'in tsaron teku, a ranar Asabar, ya ce abin da suka bai wa muhimmanci a yanzu shi ne tantance mutanen da kuma gano musabbabin gobarar.

  9. Farashin mai ya ɗaga a duniya bayan soke tattaunawar Iran da wasu ƙasashen Gulf

    Farashin man fetur ya sake tashi a kasuwannin duniya bayan rufe wani bututun mai mai muhimmanci a Saudiyya, da gazawar tattaunawar diflomasiyya da kuma hare-haren da ake kai wa jiragen ruwa a yankin Gulf.

    Farashin ɗanyen man Brent ya kai dala 108 kan kowacce ganga.

    A ranar Juma'ar da ta gabata, Saudiyya ta sanar da cewa ta rufe bututun man, bayan wasu hare-hare da Iraqi ta kai da jiragen marasa matuƙa, sun yi masa ɓarna.

    Tun da farko masarautar Saudiyya ta zargi mayaƙan ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran da kai irin waɗannan hare-hare.

    A ɓangare guda kuma, ƙasar Oman ta ɗage wani taro da aka shirya yi a ranar Litinin tsakanin Iran da ƙasashen Larabawan da ke yankin Gulf domin tattauna batun mashigar Hormuz. Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur a duniya.

  10. An fara sayar da hannun jari mafi girma na matatar Dangote

    An buɗe hannun jari mafi girma a Afirka ga jama'ar da ke da sha'awar siyan hannun jari a matatar mai ta Dangote.

    Matatar ta Ɗangote tana tayin sama da hannun jari biliyan huɗu a ƙarƙashin wata yarjejeniya da ake sa ran za ta samar da kusan dala biliyan 1.6.

    Matatar ta ƙara da cewa tana son bai wa jama'a damar kasancewa masu hannun jari a matatarsa da ta soma aiki shekaru biyu da suka gabata kuma tuni ta kasance matata mafi girma a nahiyar Afirka.

    Dangote ya bayyana cewa yana shirye-shiryen faɗaɗa aiki a matatar da za a kashe dala biliyan 14 wanda zai ruɓanya ayyukan matatar nan da shekarar 2029.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da farashin fetur ya kusa kaiwa naira 1,400 kan kowace lita zuwa ƙarshen watan Agusta a Najeriya.

  11. 'Ya kamata NATO ta kakkaɓo jiragen Rasha a sararin samaniyar Ukraine'

    Wata cibiyar bincike da ke Amurka ta ce ya kamata ƙungiyar tsaro ta NATO ta yi la'akari da fara kakkaɓo jiragen yaƙi marasa matuƙi na Rasha a sararin samaniyar Ukraine.

    Cibiyar Institute for the Study of War, ce ta bayar da wannan shawara bayan da Rasha ta kai hari a ranar Lahadi kan wata tashar jirgin ƙasa da ke kusa da iyakar Poland.

    Wani jirgin ƙasa da ke ɗauke da manyan jami'an Turai ya wuce wannan yankin jim kaɗan kafin afkuwar lamarin.

    Ukraine ta ce akwai yiwuwar Rasha ta kai harin ne da nufin tarwatsa jirgin.

    A halin yanzu, ƙasashen NATO na kakkaɓo jiragen yaƙi marasa matuƙa na Rasha ne kawai idan sun shiga sararin samaniyar ƙasashen ƙungiyar.

    Sai dai yanzu ana tattauna yiwuwar ɗaukar irin wannan mataki a sararin samaniyar Ukraine, domin kariya da kuma daƙile ƙkaruwar matakan da Rasha ke ɗauka a rikicin da ƙasashen biyu ke yi da juna.

  12. Barka da Safiya!

    Masu bibiyar wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke gabatarwa a kowacce rana, barka da warhaka.

    Da fatan an wayi gari lafiya. Kamar kullum, a yau ma shafin zai ci gaba da kawo muku rahotanni da labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

    Nabeela Mukhtar Uba tare da abokin aiki Usman Minjibir za mu kasance tare da ku zuwa anjima da za mu miƙa ragama ga sauran abokan aiki.

    Sai ku ci gaba da bibiyarmu sannan za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk, X da kuma Instagram domin karanta ƙarin labarai da ma kallon bidiyo.