Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gwamnonin Najeriya da ke neman wa'adi na biyu a zaɓen 2027
A shekarar 2027 ne al'ummar Najeriya za su sake zaɓen shugabanni a matakai daban-daban, ciki har da gwamnoni a wasu jihohin ƙasar.
Yayin da wasu jihohi za su fuskanci sauyin shugabanci, akwai waɗanda gwamnoninsu ke neman wa'adin mulki na biyu bisa tanadin kundin tsarin mulkin ƙasar.
Tun kafin fara gangamin yaƙin neman zaɓen gwamnonin a hukumance, alamun fafatawar neman kujerun gwamnoni suka fara bayyana a wasu jihohi, inda masu neman ƙalubalantar gwamnonin da ke kan mulki ke ƙoƙarin ƙarfafa tasirinsu a tsakanin masu zaɓe.
Masu nazarin harkokin siyasa na ganin cewa irin waɗannan zaɓuka kan zama wata dama ga masu zaɓe domin tantance ayyukan da gwamnatin da ke kan mulki ta gudanar a wa'adinta na farko, tare da yanke shawarar ko ta cancanci ci gaba ko a'a.
A gefe guda kuma, gwamnonin da ke neman sake komawa kan kujerunsu na bayyana nasarorin da suka ce sun samu a fannoni daban-daban domin neman amincewar jama'a a karo na biyu.
A wannan muƙala, za mu yi nazari kan gwamnonin Najeriya da ke neman wa'adin mulki na biyu a zaɓen 2027, da kuma yanayin siyasar jihohinsu gabanin fara fafatawar neman ƙuri'un masu zaɓe.
Uba Sani - Kaduna
Shi ne gwamna na shida cikin jerin gwamnonin Kaduna tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokradiyya a 1999.
Ya gina kansa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan APC a Arewacin Najeriya.
Yana fuskantar zazzafar mahayya daga tsohon abokin adawarsa Isah Ashiru Kudan na jam'iyyar ADC.
Masu sharhi na ganin cewa zaɓen gwamnan Kaduna na 2027 na cikin zaɓukan gwamnoni da za su ɗauki hankali a 2027.
Batutuwan tsaro da tattalin arziki ne muhimman abubuwan da masu kaɗa ƙuri'a za su mayar da hankali a jihar.
Abba Kabir Yusuf - Kano
Gwamnan jihar Kanon na neman wa'adin mulkinsa na biyu ne bayan da ya koma APC a farkon wannan shekara daga NNP da aka zaɓe shi a 2023.
A iya cewa jihar Kano ce kan gaba a yawan masu kaɗa ƙuri'a a Najeriya.
Yana da goyon bayan manyan jiga-jigan APC na jihar, lamarin da ya sa magoya bayansa ke ganin zai sake lashe zaɓensa cikin sauƙi.
To amma masu sharhi na ganin cewa zai fuskanci babban kalubale daga tsohon mataimakinsa Comrd Aminu Abdusslam na NDC Kwankwasiyya da ake ganin na da ƙarfi a jihar.
Masu bibiyar harkokin siyasa a Najeriya na sanya Kano cikin jihohin da zaɓen gwamnansu zai yi zafi ƙwarai.
Caleb Mutfwang - Plateau
Gwamna Mutfwang ya samu karɓuwa a jihar bayan ƙoƙarin shawo kan rikice-rikicen shari'ar zaɓen 2023.
Shi ma a farkon wannan shekarar ne ya koma jam'iyyar APC bayan ficewa daga jam'iyyarsa ta PDP da ake zaɓe shi cikinta.
Tsaro da zaman lafiya ne manyan batutuwan da jama'ar jihar za su mayar da hankali wajen zaɓen gwamnan jihar mai yawan fama da rikice-rkicen addini da ƙabilanci.
Ahmad Aliyu -Sokoto
Gwamna Ahmad Aliyu na APC ya karɓi mulkin jihar a hannun PDP a 2023.
Yana d agoyon bayan tsohon gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wamako, wanda ke zama ubagidan siyasar jihar.
Gwamnan na neman wa'adin mulki na biyu ne a fafatawa da jam'iyyun ADC , wadda tsohon gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ke zama jagoranta a jihar, da sauran jam'iyyu.
Agbu Kefas - Taraba
A 2023 ne aka zaɓe shi gwamnan Taraba karƙashin jam'iyyar PDP, kodayake daga baya ya koma APC.
Ya samu karɓuwa tsakanin al'ummar jihar ta hanyar shirye-shiryen ilimi da ci gaban al'umma.
Sai dai yana fuskantar ƙalubale daga ɗantakarar jam'iyyar NDC, Farfesa Yahaya Sani wanda a zaɓen 2023 ya zo na biyu lokavcin yana jam'iyyar NNPP.
Dikko Umar Radda - Katsina
Gwamna Radda na da goyon bayan APC mai ƙarfi a jihar Katsina, mai jiga-jigan ƴansiyasa.
Kodayake bayanai na cewa jam'iyyar ta APC na fuskantar matsaloli a jihar da ke arewa maso yammcin ƙasar.
Tsaro, musamman matsalar 'yan bindiga, zai kasance babban abin da masu zaɓe za su yi la'akari da shi.
Sai dai jam'iyyun hamayya irinsu ADC da PDP ka iya zama babban ƙalubale gare shi.
Umar Namadi - Jigawa
Gwamna Namadi ya gaji tsarin APC mai ƙarfi da aka daɗe ana ginawa a jihar.
Masu lura da al'amuramn siyasar jihar sun ce gwamnan na da kyakkyawar alaƙa da shugabannin siyasar jihar.
Babban ƙalubalensa shi ne kula da matsalolin tattalin arziki da walwalar al'ummar jihar.
Dauda Lawal - Zamfara
A shekarar 2023 ne Dauda Lawal ya ƙwace mulkin Zamfara daga jam'iyyar APC, kodayake daga baya ya koma APCn.
Babban ƙalubalensa shi ne magance matsalar tsaro da tattalin arziki, waɗanda suka daɗe suna addabar jihar.
Jam'iyyun ADC da PDP za su yi ƙoƙarin ƙwace mulkin jihar.
Sauran gwamnonin da ke neman wa'adi na biyu
- Alex Otti - Abia
- Umo Eno - Akwa Ibom
- Hyacinth Alia - Benue
- Bassey Otu - Cross River
- Sheriff Oborevwori - Delta
- Francis Nwifuru - Ebonyi
- Peter Mbah - Enugu