Garin da mutane ke girmama kaji

Asalin hoton, Mel Christian
A ƙasashe irin Najeriya da sauran ƙasashen Afirka ba baƙon abu ba ne ka ga kaji suna yawo a kan hanya ko cikin unguwanni.
Sai dai wani lokaci gara ka yi kaffa-kaffa da kajinka, domin gudun kada wata rana ka neme su ka rasa.
To amma a tsibirin Kauai da ke yankin Hawaii na Amurka, lamarin ya sha bamban.
A wannan yankin kajin daji ne ke watayawa yadda suka ga dama. Kaji ne suke yadda suka ga dama a garin.
Dubun-dubatar irin waɗannan kaji za a iya ganin su a bakin gine-gine kamar bankuna da wuraren ajiye motoci.
Babu mai su, kuma babu mai tsare su a keji, sannan wani abin mamaki shi ne da wuya ka gan su a cikin miya.
To amma ta yaya waɗannan tsuntsaye waɗanda a waus ƙasashen ke tsintar kansu a cikin tukunya, amma suke yin abin da suka ga dama ba tare da wata hantara ba a wannan tsibiri?
Amasar wannan tambaya sai an bincika tarihin yadda wannan tsibiri ke fama da manyan guguwa da kuma yadda wadannan kaji ke iya jurewa da kuma iya haihuwa cikin sauri.
Daga ina kajin suka samo asali?

Asalin hoton, GETTY
Tarihin waɗannan kajin ya samo asali ne shekara 800 da suka gabata lokacin da fataken yankin Polynesia da ke yawo a jiragen ruwa suka kawo irin waɗannan kaji a ƙasar.
A tsawon ƙarnuka da suka gabata, wadannan kaji sun riƙa rayuwa a cikin dazuka, nesa da matsugunan al'umma.
Sai dai a shekara ta 1992 lamarin ya sauya, lokacin da guguwar da aka yi wa laƙabi da Hurricane Iniki ta faɗa kan tsibirin na Kauai.
Guguwar ta fada wa yankin tana gudun kilomita 225 a awa ɗaya, lamarin da ya sanya ta lalata gonaki ta tarwatsa sheƙar kajin.
Sai kajin dajin suka fantsama zuwa cikin garuruwa, suka cakuɗu da na gida, suka hayayyafa.
Daga nan ne aka samu kaji masu juriya, bayan da suka gaji irin juriyar kajin daji, sannan suka gaji hayayyafa cikin sauri daga kajin gida da suka cakuɗa da su.
Kada a takura masu

A ƙasashen Afirka da dama kaji na fuskantar barazana daga kyanwa da shaho da kuma macizai.
Amma a wannan tsibiri an yi yunƙurin hana wasu daga cikin irin waɗannan namun daji rayuwa a cikinsa domin gudun kada su cutar da kajin.
Rashin wanzuwar irin wadannan dabbobi da kuma yanayi mai ɗumi da ake da shi a yankin ya sanya kajin ke iya hayayyafa cikin hanzari.
Sai dai a halin yanzu rayuwa da irin waɗannan kaji na zama wani ƙalubale ga mutanen yankin.
Zakaru a cikinsu za su iya yin cara tun a farkon dare idan suka ga dama.
Haka nan kuma suna yi wa mutane ɓarna.
Dandazon waɗannan kaji za su iya lalata lambuna da mafnin gona, a wasu lokutan kuma sukan haddas cunkoson ababen hawa a kan tituna.
Me ya sa ba a cin su kamar kajin gida?

Asalin hoton, GETTY
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan ce tambayar da kowa yake son yi: me ya sa mazauna wannan tsibiri ba za su riƙa yanka waɗannan kaji suna yinfarfesu da su ba?
Ɗaya daga cikin dalilan shi ne waɗannan kaji suna da gudu sosai, haka nan suna tashi sama zuwa kan bishiyoyi suna neman abinci, ciki har da ƙwari.
Hakan ya sanya namansu yake da tauri kuma ba su da kitse sosai idan aka kwatanta da kajin gida waɗanda ake kiwo domin ci.
Akwai wata karin magana da ta shahawraa a yankin Hawaii da ke cewa: 'Idan kan son dafa kazar Hawaii to ka hada ta da dutse, idan ya yi taushi to kazar ta dahu'.
A maimakon ƙoƙarin korar waɗannan kaji, a yanzu al'ummar yankin sun rungume su a matsayin wani tambari na yankin.
A yanzu waɗannan kaji na daga cikin abubuwan da ke janyo masu yawo shaƙatawa zuwa tsibirin, inda ake buga rigunan sawa da kofuna da kuma kayan tsaraba ɗauke da hotunan kajin, inda ake sayar wa baƙin da suka ziyarci tsibirin.
Saboda haka, a wannan tsibirin da ke yankin Hawaii, yayin da kaji a wasu sassan duniya ke ƙarewa a cikin tukunya, a nan kuwa sun zama tamkar tambarin yankin ne, kuma abokan zaman al'ummar.


























