KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 03/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 03/11/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Shugaba Tinubu
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Ƴar Arewan da ke buga wa Najeriya ƙwallo
  • waya
  • Gwamna Adeleke na Accord
  • Jihohi masu talauci
  • Buba Galadima
  • Dattijuwa

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. An ceto wasu mutum takwas da aka yi garkuwa da su a Kaduna

    Ƴansandan Najeriya

    Jami'an tsaro sun tabbatar da ceto wata mata mai juna biyu, Jamila Muhammad da wasu mutum bakwai da 'yan bindiga suka sace a jihar Kaduna bayan shafe makonni a hannun masu garkuwar.

    An kuɓutar da mutanen ne a wani samame na haɗin gwiwa da ya haɗa da Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS da rundunar ƴansandan Najeriya da sojoji tare kuma da haɗin gwiwar gwamnatin Kaduna.

    Kwamishinan ƴansanda a jihar, Muhammad Rabiu shi ya tabbatar da ceto mutanen a wani taron manema labarai a hedkwatar DSS da ke Kaduna.

    Rabiu ya ce samamen na cikin wani ɓangare na ƙoƙari da jami'an tsaro ke yi wajen kakkaɓe ayyukan masu garkuwa a anguwar Millenium City da ƙewaye.

    Ya ce anguwar ta fuskanci ayyukan masu garkuwa a baya-bayan nan, abin da ya saka fargaba tsakanin mazauna yankin da kuma masu ruwa da tsaki kan tsaron lafiyar mutane.

    An sace Jamila mai shekara 27 ranar 6 ga Oktoba lokacin da ƴanbindiga suka kai hari anguwar Millenium City da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna, inda kuma a lokacin ne aka yi garkuwa da Ahmad Zakka da matarsa da kuma ƴarsu ƴar kimanin watanni shida.

    Sai dai an saki Zakka da matarsa ranar 15 ga Oktoba, kwanaki kaɗan bayan bidiyonsu ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka ci gaba da riƙe Jamila har sai da jami'an tsaro suka kai farmaki.

    Rahotanni sun bayyana cewa ta yi ɓarin cikinta lokacin da take hannun ƴanbindigar.

  2. Amurka za ta daina bai wa Isra'ila tallafin kuɗi

    Trump

    Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta daina bai wa Isra’ila tallafin kusan dala biliyan huɗu a kowace shekara, bayan sun cimma yarjejeniya da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu watanni da suka gabata” domin kawo ƙarshen tsarin.

    A watan Yuni, Mista Netanyahu ya ce lokaci ya yi da ƙasarsa za ta daina kasancewa mai karɓar tallafi, ta koma abokiyar hulɗa.

    Yarjejeniyar fahimtar juna ta tsawon shekara goma, wadda ta tanadi Amurka na ba wa Isra’ila kusan dala biliyan huɗu a kowace shekara a matsayin tallafin soji, za ta ƙare a shekarar 2028.

    Ana kyautata zaton cewa Amurka ta bai wa Isra’ila fiye da dala biliyan 21 a tallafin soji cikin shekaru biyu bayan hare-haren da Hamas ta kaddamar a ranar 7 ga Oktoba, a cewar wata cibiyar bincike da ke birnin Washington.

    Tun bayan ƙarshen yaƙin duniya na biyu, Isra’ila ce ta fi karɓar tallafin ƙasashen waje daga Amurka.

  3. EFCC ta bankaɗo haramtaccen matatar fetur na ƴan China a Ogun

    Matatar mai a Ogun

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC), ta ce ta gano wata haramtacciyar matatar man fetur da ake zargin wasu ƴan China na gudanarwa a yankin Ogere da ke jihar Ogun.

    Wata sanarwa da EFCCn ta fitar a shafinta na X, ta ce an kai samame a matatar ranar Asabar, 31 ga Oktoba, bayan samun bayanan sirri na yadda ake tafiyar da matatar..

    Hukumar ta ce jami’anta sun samu babu kowa a wurin lokacin da suka kai samame.

    Har ila yau, ta ce an gano sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen tace man fetur da kuma wasu tankunan da aka binne a ƙarƙashin ƙasa.

    Hukumar ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin gano waɗanda ke da hannu a tafiyar da matatar domin kama waɗanda suke da laifi.

  4. Mutum biyu sun mutu, 20 sun jikkata a harin Rasha a Ukraine

    Rasha

    Akalla mutum 2 ne suka mutu wasu sama da 20 sun jikkata sakamakon harin makami mai linzami da Rasha ta kai birnin Dnipro na Ukraine.

    Magajin garin birnin, Dmytro Filatov, ya ce ana kwashe marasa lafiya daga cibiyar kula da marasa lafiya masu fama da cututtuka masu tsanani da harin ya lalata.

    Tun da fari, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce manyan hare-haren da Rasha ta kai cikin dare sun jikkata sama da mutum 70 a wani asibiti da ke Kharkiv, tare da katse wutar lantarki a birane da dama.

    Hare-haren na cikin dare sun biyo bayan ɗaya daga cikin munanan hare-haren da Rasha ta kai a 'yan makonnin nan, wanda ya afkawa wata cibiyar bayar da agajin jin ƙai a yankin Zaporizhzhia a daren Litinin.

    Yanzu an tabbatar da mutuwar mutum 31, yayin da ake neman sama da mutum 40.

  5. Ƴan bindiga sun sace ɗaliban Islamiyya 14 a Neja

    Ƴan bindiga

    Aƙalla ɗaliban makarantar Islamiyya 14 ne aka yi garkuwa da su a yankin Pandogan na karamar hukumar Rafi a jihar Neja.

    Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar, Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Litinin.

    A cewarsa, lamarin ya faru ne ranar Lahadi lokacin da ɗaliban ke girbe masara a gonar malaminsu a ƙauyen Tungan-Bako lokacin da ƴan bindiga suka afka musu.

    Kakakin ƴan sandan ya ce ana can ana ƙoƙarin ganin an ceto ɗaliban.

  6. An aika jami'an tsaro don kwantar da zanga-zanga a Bangladesh

    Bangladesh

    An tura jami'an tsaro babban birnin Bangladesh, Dhaka, yayin da zanga-zangar ma’aikatan masana’antar tufafi ta shiga rana ta huɗu, lamarin da ya tilasta rufe daruruwan masana’antu.

    Akwai ɗimbin jami’an ’yan sanda a yankunan masana’antu a yankunan Gazipur da Narayanganj.

    ’Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zangar da suka yi ƙoƙarin toshe manyan hanyoyi. Suna neman a ƙara masu albashi saboda tsadar rayuwa da ke ƙaruwa.

    Wata mai zanga-zanga kenan ke cewa komai ya yi tsada a kasar nan, kama daga kayan amfanin yau da kullum, da hayar gidaje da wutar lantarki da Ma’aikatan sun yi watsi da kiran da aka yi musu na komawa bakin aiki duk da matakin da gwamnati ta ɗauka na kafa wani kwamiti domin duba albashinsu.

    Masana’antar tufafi na daga cikin manyan ginshiƙan tattalin arzikin Bangladesh, inda take samar da kusan dala biliyan 40 a duk shekara.

  7. Shugabannin adawar Isra'ila na ƙoƙarin kafa gwamnati

    Gadi Eisenkot

    Shugabannin jam’iyyun adawa a Isra’ila sun yi wata ganawa a karon farko tun bayan babban zaɓen da aka gudanar a makon da ya gabata, wanda babu wata jam'iyyar da ta yi nasara a zaɓen.

    Jam’iyyun adawar sun nuna goyon bayansu ga tsohon babban kwamandan sojin Isra’ila Gadi Eisenkot, amma har yanzu suna da saɓanin ra’ayi kan yadda za a kafa gwamnati.

    Shugaban jam’iyyar Democrats, Yair Golan, ya yi kiran a kafa gwamnatin haɗaka.

    Sai dai wasu daga cikin ’yan adawar sun ba da shawarar ƙulla ƙawance da jam’iyyun Yahudawa masu ra’ayin mazan jiya na ultra-Orthodox.

    Ana sa ran Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, zai fara tsarin zaɓen ɗan takarar da zai yi ƙoƙarin kafa gwamnati a ranar Laraba, wanda dokar ƙasar ta ba shi wa'adin kwanaki 7 domin hakan.

  8. Wani jirgi da ya taso daga Isra'ila ya yi saukar gaggawa a Bulgaria

    Kafafen yaɗa labarai a Bulgaria sun rawaito cewa wani jirgin sama da ya taso daga Isra’ila ya sauka a filin jirgin sama na Sofia bayan an samu barazanar cewa an sa bam a cikin jirgin ta hanyar saƙon imel.

    Lamarin ya biyo bayan saukar gaggawa da wasu jirage biyu da ke kan hanyarsu ta zuwa Warsaw suka yi, waɗanda rahotanni suka ce su ma sun sauka saboda irin wannan barazanar bam.

    Filin jirgin sama na Modlin da ke Warsaw ya dakatar da ayyukansa na ɗan lokaci yayin da ake binciken ɗaya daga cikin jiragen.

    A ranar Litinin kuma, wani jirgin kamfanin Wizz Air da ya taso daga Landan zuwa Sofia an karkatar da shi zuwa Budapest a Hungary shi ma kan barazanar an dasa bam a cikinsa, yayin da yake sararin samaniya.

  9. Amurkawa na kaɗa ƙuri'a a zaɓen tsakiyar wa'adi

    ..

    Miliyoyin Amurkawa na kaɗa ƙuri’a a zaɓukan tsakiyar wa’adi, waɗanda za su tantance ko Donald Trump zai ci gaba da riƙe ikon Majalisa a shekaru biyu na ƙarshe na wa’adin mulkinsa.

    A tarihi, jam’iyyar da ke mulki kan sha kaye a irin waɗannan zaɓuka na tsakiyar wa’adi, kuma ƙuri’un jin ra’ayin jama’a na nuna cewa jam’iyyar Democrat na da damar lashe Majalisar Wakilai kuma wataƙila har da Majalisar Dattawa.

    Ana hasashen za a yi fafatawa mai zafi a kujerun Majalisar Dattawa a wasu jihohin da a baya aka ɗauka a matsayin sansanonin Republican, ciki har da Texas, Alaska, Kansas da Ohio.

    ’Yan Democrat na fatan yin amfani da damuwar da jama’a ke nunawa kan tsadar rayuwa, wadda suka ce ta ƙara tsananta sakamakon yaƙin da Shugaba Donald Trump ya shiga da Iran don cimma muradi.

  10. 'Iran ta kakkaɓo jiragen Amurka biyu marasa matuƙa'

    ..

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce ta lalata jirage marasa matuƙa guda biyu na Amurka a lardin Hormozgan a daren jiya.

    A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce ta jirage marasa matuƙa ne a sararin samaniyar Bandar Khamir “ta hanyar haɗaɗɗen harbin kariyar sararin samaniya”.

    Amurka ba ta mayar da martani ba.

    Kafofin watsa labaran Amurka sun ambato wasu majiyoyin soji na cewa a safiyar yau Amurka ta kai hari kan wurare a tsibirin Qeshm bayan da IRGC ta yi harbi kan wani jirgin yaƙin Amurka.

    Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya ce a yau: “Ya kamata ƙasashen yankin su sani cewa kamar yadda Jamhuriyar Musulunci ta Iran take a shirye domin yin karya duk yatsar da aka nuna mata, Amurka za ta gaskata wannan.

  11. Ba mu da hannu a sabon harin Amurka kan Iran - Isra'ila

    ..

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ba ta da hannu a hare-haren da aka ruwaito Amurka ta kai a wani tsibiri da ke Iran.

    Wannan na zuwa ne bayan da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, a baya-bayan nan, ya yi barazanar dawo da yaƙi da Tehran.

    Da yake amsa tambayar kamfanin dillancin labarai na AFP, kakakin rundunar sojin Isra'ila ya ce Isra'ila ba ta da wata alaƙa da hare-haren da Amurka ta kai a tsibirin Qeshm a daren jiya.

    Harin ya zo ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki a Amurka, yayin da kuma ake ci gaba da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu, wadda ta sake nuna akwai yiwuwar har yanzu a iya cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe watanni tara ana yi.

  12. China ta gargaɗi Amurka game da kai wa Iran hari

    Shugaba Trump da Xi

    Ministan Harkokin Wajen China ya ce ƙasarsa na goyon bayan Iran wajen kare ikon mulkinta da kuma tsaronta.

    A wata ganawa da Ali Bagherikani, mataimakin sakataren majalisar tsaron Iran, Wang Yi ya ce ƙasarsa na kira ga dukkan ɓangarorin da ke cikin rikicin Gabas ta Tsakiya su mayar da hankali kan hanyoyin warware shi ta siyasa.

    A halin da ake ciki kuma, Rasha ta ce alamun yiwuwar ɗaukar sabbin matakan soji a kan Iran na haifar da damuwa.

    A nata ɓangaren, China ta yi gargaɗi ga Amurka kan kai wa Iran hari.

    Shugaban China Xi Jinping ya gana da Sarkin Oman, Haitham bin Tariq Al Said, a ranar Lahadi, inda ya ce bai kamata Gabas ta Tsakiya da yankin Tekun Fasha su zama wurin da manyan ƙasashen duniya ke fafatawa ba.

    A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da aka fitar bayan taron, Oman ta bayyana goyon bayanta ga shirin zaman lafiya na China a Gabas ta Tsakiya, tare da nuna fatan cewa Beijing za ta taka rawa mai ƙarfi wajen tabbatar da dawwamammen zaman lafiya a yankin.

    China ce babbar mai sayen man fetur daga Iran, kuma ita ce ta biyu mafi girman ƙawar tattalin arzikin ƙasar.

    Beijing ta yi Allah wadai da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran, da kuma takunkuman da Washington ta kakaba wa Tehran.

    China ta jaddada muhimmancin buɗe ƙofofin diflomasiyya a mashigar Hormuz, tare da yin kira da a tsagaita wuta.

  13. NLC da TUC sun samu saɓani kan tallafin 70,000 na ma'aikata

    NLC/UC

    Manyan ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya, NLC da TUC sun samu saɓani kan tallafin sufuri na naira 70, da gwamnatin ƙasar za ta bai wa ma'aikatan ƙasar tsawon wata shida.

    A makon da ya gabata ne wakilan NLC da na gwamnatin tarayya suka cimma wata yarjejeniya da ta ƙunshi bai wa ma'aikatan ƙasar tallafin sufuri na naira 70,000 a kowane wata har tsawon wata shida.

    To sai kwanaki bayan hakan ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta nuna rashin amincewa da matakin, tana mai watsi da shi.

    Cikin wata sanarwar da shugaba da sakataren ƙungiyar na ƙasa, festus Osifo da Nuhu Toro suka sanya wa hannu, TUC ta ce gwamnatin tarayya na da damar da za ta iya ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 300,000 maimakon 70,000.

    To sai dai cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels, shugaban ƙungiyar NLC, Joe Ajaero ya ce ƙungiyarsa na da ikon yin shawarwari ita kaɗai kan batutuwan da suka shafi ƙwadago, bisa ƙa’idar Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya (ILO).

    Ya ƙara da cewa saɓanin haka ƙungiyar TUC ba za ta iya cimma yarjejeniya da gwamnati ita kaɗai ba, dole sai da NLC.

  14. Amurka ta sake kai wa Iran hari

    Rahotanni na cewa Amurka ta kai wasu hare-hare a tsibirin Qeshm na Iran, a wani mataki da aka bayyana a matsayin da ta bayyana da kariyar kai.

    Harin ya zo ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki a Amurka, yayin da kuma ake ci gaba da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu, wadda ta sake nuna akwai yiwuwar har yanzu a iya cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe watanni tara ana yi.

    Kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Iran sun ruwaito cewa an ji ƙarar fashe-fashe a yankin, kodayake Ma’aikatar Tsaron Amurka, ba ta tabbatar da alhakin kai harin ba, sai dai wasu jami’an Amurka sun ce an kai farmakin ne bayan da Iran ta harba makamai kan wani jirgin saman Amurka.

    Tun da farko dai, farashin mai a kasuwannin duniya ya faɗi sosai bayan kalamai masu cike da kwarin gwiwa daga Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, da kuma Shugaban Amurka, Donald Trump.

  15. Ana taƙaddama kan zaɓen fitar da gwanin sanatan Zamfara ta Arewa

    Sahabi

    Wata sabuwar taƙaddama ta ɓarke a jihar siyasar jihar Zamfara kan zaɓen fitar da gwanin sanatan Zamfara ta Arewa a jam'iyyar APC.

    A ranar Litinin ne jam'iyyar ta gudanar da zaɓen fitar da gwani tsakanin ƴantakara uku, amma fafatwar ta fi zafi ne tsakanin sanata mai ci Sahabi Yau Kaura da wanda ke neman kujerar kuma tsohon Sanatan yankin, Sanata Tijjani Yahaya Kaura.

    Sai dai bayan kammala zaɓen shugaban kwamitin zaɓen Dr Auwal Abdullahi Aliyu ya bayyana Sanata Sahabi Yau Kaura a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri'a 49,176.

    Yayin da Sanata Tijjani Yahaya Kaura ya samu ƙuri'a 9,628.

    To sai wani abu da ya ɗauki hankali shi ne jim kaɗan bayan shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwanin ya bayyana wanda ya yi nasara, sai aka ga wasu ƴan kwamitinsa cikin wani bidiyo na bayyana Sanata Tijjani Yahaya a matsayin wanda ya yi nasara.

    Lamarin da ya sa kowane ɓangare ke iƙirarin nasara a zaɓen.

    Bayanai na cewa an gwabza zaɓen ne tsakanin magiya bayan manyan jiga-jigan siyasar jihar, Sanata Abdul'aziz Yari da ke goyon bayan Sanata Tijjani Yahaya, da kuma Ƙaramin Ministan tsaron Najeriya, Muhammad Bello Matawalle da ke goyon bayan Sanata Sahabi.

    Zuwa yanzu dai uwar jam'iyyar APC ta ƙasa ba ta ce komai ba game da lamarin.

  16. Na yi wa duka ƴan Najeriya addu'a a lokacin Umarata - Tinubu

    Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya kammala ziyarar ibadar Umarah da yake yi zuwa Saudiyya, inda ya bayyana cewa ya yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da wadata ga dukkan ’yan Najeriya.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

    “Na kammala ziyarar ibada ta a Saudiyya, tare da membobin tawagata, muka samu wata gagarumar karramawa ta shiga cikin Ka’aba Mai Tsarki domin yin addu’a, tare da gudanar da Umrah,” in ji shi.

    Ya kuma bayyana ziyarar da abubuwan da ya gani a can a matsayin wata shaida ta ɗorewar alaƙar addini, abota da mutunta juna tsakanin Najeriya da ƙasar Saudiyya.

    A makon da ya gabata ne shugaban na Najeriya ta tafi Saudiyya domin halartar ibadar Umarah.

  17. Amurkawa na shirin fita zaɓen tsakiyar wa'adi

    zaɓen

    A yau ne Amurkawa za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen rabin wa’adi wanda zai taka muhimmiyar rawa wajen tsara shekaru biyun ƙarshe na mulkin Shugaba Donald Trump.

    Jam’iyyarsa ta Republican na ƙoƙarin ci gaba da rike rinjaye a majalisun dokokin ƙasar guda biyu, amma mafi yawan masu sharhi na hasashen cewa jam’iyyar Democrat za ta sake karɓe iko da aƙalla a Majalisar Wakilai.

    Ana ci gaba da fafatawa sosai a kan kujeru da dama na Majalisar Dattawa, inda har yanzu ba a iya hasashen waɗanda za su yi nasara.

    Masu kaɗa ƙuri’a da dama na ɗora alhakin tsadar rayuwa a kan gwamnatin Trump.

    Yawanci jam'iyyar shugaban ƙasa mai ci a zaɓen ta kan rasa rinjaye a kujerun majalisun dokokin inda a bana halin tsadar rayuwar da ake fama da ita a ƙasar wadda aka ɗora alhaki akan Donald Trump, jam'iyyar Republican za ta iya rasa rinjye.

  18. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku kasance da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa