Hanyoyi uku da masu tsattsauran ra'ayi ke bi wajen jan hankalin matasa a Najeriya

Yanar gizo
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A cikin shekarun baya-bayan nan, yanar gizo ta zama wani muhimmin ɓangare na rayuwar matasa a Najeriya, musamman wajen neman ilimi da sana'a zuwa sadarwa da nishaɗi.

A Najeriya, miliyoyin matasa ne ke amfani da kafafen sada zumunta da sauran ɓangarorin intanet a kullum.

Sai dai yayin da yanar gizo ke samar da damarmaki masu yawa, masana tsaro na gargaɗin cewa ta zama wata muhimmiyar hanya da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi ke amfani da ita wajen yaɗa manufofinsu da kuma jan hankalin sababbin mambobi.

Masana sun ce sauyin fasahar sadarwa ya sauya yadda ake yada ra'ayoyin tsattsauran ra'ayi. Idan a baya irin waɗannan ƙungiyoyi suna dogaro ne da ganawa kai tsaye ko kuma wa'azi a wajen jama'a, yanzu suna iya isa ga dubban matasa ta hanyar waya ko kwamfuta daga ko'ina cikin duniya.

A daidai lokacin da Najeriya ke fama da ƙalubalen rashin aikin yi, talauci da matsin tattalin arziki, wasu masana na ganin cewa waɗannan matsaloli na ƙara sa wasu matasa su kasance cikin haɗarin karɓar saƙonnin masu tsattsauran ra'ayi cikin sauƙi.

Shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, Kabiru Adamu, ya bayyanawa BBC hanyoyi uku da ake amfani da su wajen jan hankalin matasa, da kuma matakin da ya dace a ɗauka.

Yanar gizo

Masanin ya ce yawanci ta hanyar amfani da yanar gizo suke fara isa ga matasa. "Wani lokaci sukan shiga shafukan sada zumunta ko zauruka ko kuma su wallafa abubuwan da za su ja hankalin matasa saboda sun riga sun fahimci abubuwan da ke damunsu," in ji shi.

A cewarsa, waɗannan ƙungiyoyi suna nazarin halin da matasa ke ciki, sannan su tsara saƙonninsu ta hanyar da za ta sa su ji ana fahimtar matsalolinsu.

"Da zarar sun gano abin da matashi yake fuskanta, ko rashin aikin yi ne, ko matsalar tattalin arziki, ko kuma rashin jin cewa yana da muhimmanci a cikin al'umma, sai su fara amfani da waɗannan abubuwa wajen jan hankalinsa," in ji Kabiru.

Masanin ya ce kafafen sada zumunta da sauran dandamalin intanet sun ba masu tsattsauran ra'ayi damar samun damar da ba su taɓa samu ba a baya.

Ya ƙara a cewa yanar gizo ita ce hanya ta farko. A can ne suke gano matasa, su fahimci abubuwan da suke tattaunawa akai da kuma damuwarsu, inda ya ce daga nan ne kuma suke fara gina dangantaka da su.

Masana sun bayyana cewa a wasu lokuta ba sa bayyana kansu kai tsaye a matsayin masu tsattsauran ra'ayi. Maimakon haka, suna shiga tattaunawa kan batutuwan da suka shafi rayuwar matasa kafin daga bisani su fara gabatar da ra'ayoyinsu.

Tattalin arziki

Baya ga yanar gizo, Kabiru Adamu ya ce matsin tattalin arziki na daga cikin manyan abubuwan da masu tsattsauran ra'ayi ke amfani da su wajen jan hankalin matasa su shiga cikin su.

"A irin yanayin da ake ciki na ƙuncin rayuwa da talauci da rashin aikin yi, wasu daga cikin waɗannan ƙungiyoyi kan ba wa matasa kuɗi ko kuma su yi musu alƙawarin samun wata dama da za ta rage musu raɗaɗin rayuwa."

Ya ce irin waɗannan alƙawura na iya zama masu jan hankali musamman ga matasan da suka daɗe suna fama da rashin aikin yi ko kuma waɗanda ke cikin matsanancin hali.

Najeriya dai ta yi suna a cikin ƙasashen da ke da arzikin ɗimbin matasa, kuma da yawa daga cikinsu ba su da aikin yi, wanda hakan ya sa ƙasar takan zama ɗaya daga cikin waɗanda ake saurin jan ra'ayin matasanta da kuɗi.

Karkatar da koyarwar addini

A cewar Kabiru Adamu, hanya ta uku ita ce amfani da addini ta hanyar juyawa da kaucewa daga asalin koyarwarsa.

"Sukan karkatar da wasu fassarorin addini domin su dace da ra'ayinsu. Daga nan su riƙa nuna wa matasa cewa idan suka bi tafarkinsu, za su samu ɗaukaka a duniya da kuma matsayi mai girma a lahira."

Ya ce sau da yawa irin waɗannan ƙungiyoyi kan yi amfani da hujjoji da suka cire daga mahallinsu domin gina akidun da suke son matasa su runguma.

An dai sha samun waɗanda suka yi amfani da sunan addini wajen isar da saƙonnin da suke son yaɗawa ga mutane, musamman matasa, wanda kuma a lokuta da dama sukan samu mabiya.

Ƙalubalen sa ido a yanar gizo

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani abu da aka daɗe ana tattaunawa a Najeriya shi ne yadda ba a iya daƙile shafukan da ake zargin masu tsauraran ra'ayi tare da kamawa da hukunta masu gudanar da su.

A game da wannan, Kabiru Adamu ya ce gwamnati na fuskantar manyan ƙalubale wajen sa ido kan irin waɗannan ayyuka.

"A nan ne gwamnati ke da babban gibi ta fuskar tsaro. Har yanzu ba mu da cikakken tsarin gano ainihin mutanen da ke amfani da yanar gizo, wato abin da ake kira digital identity."

A cewarsa, hakan na sa bincike kan masu amfani da shafukan intanet wajen aikata laifuka ya kasance mai wahala.

"Na biyu kuma, ba mu da isassun ƙwararrun hukumomi da aikinsu kawai shi ne kula da yadda ake gudanar da harkokin yanar gizo. Yawancin manyan kamfanonin da ke gudanar da waɗannan dandamali suna ƙasashen waje kuma suna bin dokokinsu wajen bayar da bayanai."

Ya ce a mafi yawan lokuta jami'an tsaro ba sa samun damar wasu bayanai sai ta hanyar bin matakan doka ko samun umarnin kotu.

Matakan kariya

A ra'ayinsa, mataki na farko da gwamnati ya kamata ta ɗauka shi ne ƙarfafa tsarin tantance ainihin masu amfani da yanar gizo.

"Ya kamata a samar da ingantaccen tsarin 'digital identity' domin sanin masu amfani da intanet tare da tabbatar da cewa ana amfani da shi yadda ya kamata."

Sai dai ya jaddada cewa tsaro kaɗai ba zai wadatar ba. "Akwai buƙatar abin da ake kira 'digital literacy' wato wayar da kan mutane da ilimantar da su game da yanar gizo," in ji shi.

Ya ƙara da cewa dole mutane su fahimci yadda yanar gizo ke aiki, abin da ya kamata su yi da kuma abin da bai kamata su yi ba.

Ya ce ya kamata a fara koyar da irin wannan ilimi tun daga matakin firamare har zuwa jami'a tare da ci gaba da wayar da kan jama'a, musamman matasa domin guje wa shiga ƙungiyoyin nan.

"Ya kamata matasa su san yadda za su gane waɗanda ke ƙoƙarin jan ra'ayinsu da kuma dabarun da irin waɗannan ƙungiyoyi ke amfani da su."

Daidaita tsaro da ƴancin jama'a

Kabiru Adamu ya ce duk wani ƙoƙari na ƙarfafa sa ido kan yanar gizo ya kamata ya kasance cikin iyakokin doka ba tare da take ƴancin faɗin albarkacin baki da dokar ƙasa ta tanada ba.

"Abin da ake buƙata shi ne a tabbatar da cewa idan wani ya karya doka a yanar gizo, an gano shi kuma an hukunta shi bisa doka. Amma ba wai a tauye ƴancin jama'a na bayyana ra'ayinsu ba."

A cewarsa, yaƙi da yaɗuwar tsattsauran ra'ayi a yanar gizo ba aikin gwamnati kaɗai ba ne.

"Wannan ya shafi iyaye, malamai, shugabannin al'umma, kafafen yaɗa labarai da kamfanonin fasaha. Sai an haɗa kai ne za a iya kare matasa daga masu amfani da matsalolinsu wajen yaɗa tsattsauran ra'ayi."

Ya ƙara da cewa, yayin da fasaha ke ci gaba da sauya rayuwa, wajibi ne a tabbatar cewa matasa suna amfani da ita wajen gina makomarsu, ba tare da fadawa tarkon waɗanda ke son amfani da ita wajen jefa su cikin hatsari ba.