Man Utd na son Leao, Madrid na shirin sake dawo da Mourinho

Asalin hoton, Getty Images
Mai yuwuwa Manchester United ta karkata ga dan wasan gaba na gefe Rafael Leao, mai shekara 26, dan Portugal a bazara, inda AC Milan take a shirye a yi maganar musaya da ita ta karbi Marcus Rashford, ko dan wasan tsakiya na Uruguay Manuel Ugarte mai shekara 25, ko Joshua Zirkzee, mai shekara 24, dan Netherlands. (La Gazzetta dello Sport)
Crystal Palace ta fitar da jeri masu horad da 'yan wasa shida da za ta zaba domin maye gurbin Oliver Glasner a karshen kaka, kuma kocin Coventry Frank Lampard da na Ipswich Kieran McKenna na cikin wadanda take nazari. (Independent)
Benfica ta sanya sunan kociyan Fulham Marco Silva, na Portugal mai shekara 48, a matsayin na gaba da zai maye gurbin Jose Mourinho, wanda shi kuma ake alakanta shi da sake komawa Real Madrid a kaka ta gaba. (Record)
Manchester United ba ta son ta jefa kanta cikin dambarwar sayen dan wasan Nottingham Forest na tsakiya da Ingila, Elliot Anderson, mai shekara 23, wanda Manchester City, ma na sonshi kuma za ta iya karkata ga wasu 'yan wasan kamar su Carlos Baleba na Brighton da tawagar Kamaru Carlos Baleba. (ESPN)
Newcastle na shirin yin garambawul a bazara, inda take duba yuwuwar sayen golan Faransa Robin Risser da golan Manchester City da Ingila James Trafford, mai shekara 23. (i paper)
Kyaftin din Manchester United Bruno Fernandes, mai shekara 31, yana da damar a saye shi a kan fam miliyan 57 a kwantiraginsa, amma kuma kungiyar na da kwarin guiwa cewa idan har ta samnu tikitin buga gasar Zakarun Turai (Champions League), hakan zai iya sa ta shawo kan dan wasan na Portugal ya tsaya. (Mirror)
Barcelona na ci gaba da kokarin ganin ta sayi dan wasan gaba na Atletico Madrid da Argentina Julian Alvarez, mai shekara 26, amma kuma Arsenal da Paris St-Germain sun ki su hakura da neman sayen tsohon dan wasan na Manchester City. (Teamtalk)
Leeds United ta sake sabunta sha'awar da take yi wa dan wasan tsakiya na Sporting Hidemasa Morita, kuma ana ganin dan wasan na tawagar Japan mai shekara 30 zai iya yarda idan har kungiyar ta yi nasarar komawa gasar Firmiya. (Mail)
Kila matsalar kudi ta sa Marseille sayar da dan wasanta na gaba na Ingila Mason Greenwood, mai shekara 24, - kuma Juventus a shirye take ta zare dan wasan duk da cewa Marseille na son akalla Yuro miliyan 50ne a kn dan wasan. (La Gazzetta dello Sport)
Tuni Everton ta mika wa PSV tayin cewa tana son dan wasanta na gaba dan Bosnia da Herzegovina Esmir Bajraktarevic, mai shekara 21, a bazara. (SportSport )









