Wane giɓi ficewar UAE daga Opec za ta haifar?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Faisal Islam
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Economics editor
- Lokacin karatu: Minti 3
Wani babban al'amari ne cewa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sanar da cewa za ta fice daga ƙungiyar Ƙasashe Masu Arzikin man Fetur ta Opec baga-tatan.
UAE ta kasance mamba a ƙungiyar tun kafin ta zama ƙasa a shekara ta 1971.
Opec dai ta ƙunshi yawancin ƙasashe daga yankin Gulf masu fitar da man fetur, waɗanda suka shafe tsawon shekaru suna daidaita farashin man fetur ta hanyar ƙara wa ko kuma rage samar da shi. Ta taka rawa sosai a rikicin mai da aka shiga a shekarun 1970.
Yayin da Saudiyya ta mamaye ƙungiyar wajen samar da mai, UAE ita ce ta biyu wajen samar da mai. Hakan na nufin cewa ƙasar na da muhimmanci a ƙungiyar, saboda tana da ƙarfin iya ƙara samar da mai don rage farashi.
Opec na samar da ganga miliyan 3-3.5 a kowace rana.
Sai dai, sanar da ficewa a wannan lokaci na nuna irin sakamakon da yaƙin Iran ya janyo. Matsin lamba da yankin ya shiga ya yi tasiri kan yanayin dangantaka tsakanin UAE da Iran, kuma zai shafi dangantakar ƙasar da Saudiyya wadda ta riga ta lalace.
Ga Opec, wannan babban giɓi ne a daidai lokacin da tambayoyi ke fita na ganin haɗin kan ƙungiyar na tsawon lokaci.
Lokacin da UAE za ta fitar da mai ɗinta a kasuwa ta hanyar ruwa ko kuma bututai, zai iya yiwuwa ya kai ganga miliyan biyar a rana. Saudiyya kuwa za ta mayar da martani ta hanyar tsauwala farashin da tattalin arzikin UAE zai iya jure wa, amma ban da sauran mambobin Opec.
Komai ya ta'allaka kan martanin Saudiyya.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Manyan jami'an masarautar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun bayyana batun samar da sabbin bututai a rijiyoyin mai da ke Abu Dhabi, inda suka ketare mashigar Hormuz - da ya dangana zuwa tashar jiragen ruwa na Fujairah da ba a amfani da shi.
Akwai wani babban bututu da ake amfani da shi a yau, sai dai ana buƙatar ƙara girmansa domin ya yi daidai karin buƙatar samar da mai.
A halin yanzu, yayin da aka toshe mashigar Hormuz, wannan ba shi ne kaɗai abin da ke faruwa a ɓangaren kasuwar mai ba, wanda kuma ke shafar farashin mai da gas da robobi da kuma sauran kayan abinci.
Opec ba ta da muhimmanci sosai a kasuwar mai a duniya kamar yanda take da shi a shekarun 1970, inda kusan kashi 85 na mai da ake hada-hada a duniya ke fitowa daga wajen.
Haka-nan mai ba shi da muhimmanci ga tattalin arzikin duniya fiye da yadda yake a shekarun 1970. Ƙungiyar ba za ta iya janyo wa duniya tsaiko wajen mai ba, kamar yadda yake a baya.
Na tuna maganar da wani jami'i a Opec ya faɗa min, kuma tsohon ministan mai a Saudiyya Sheikh Yamani: "Zamanin mai ba zai kare ba saboda duniya ta rasa mai.
Hanya ɗaya ta fahimtar matakin UAE shi ne, alamar cewa duniya ta rage dogaro da mai, kuma akwai alamomi da suka nuna haka: Zuba hannun jarin da China ta yi a ɓangaren lantarki ya taimaka wajen dakile taɓarɓarewar tattalin arziki daga hauhawar farashin man fetur da iskar gas.
Ta hanyar samar da motoci masu aiki da lantarki, manyan motoci da kuma jiragen ƙasa sun rage amfani da mai da ganga miliyan ɗaya a rana, a ƙasar da ta kasance ta biyu mafi girman tattalin arziki a duniya.
Buƙatar mai a duniya zai daidaita yayin da wannan lamari ke ci gaba da karaɗe faɗin duniya.
Wannan na nufin cewa yana da kyau a samar da kuɗaɗe da yawa daga ɓangaren mai kafin bukata ya karu. UAE na da karfin tattalin arziki da kuma tattalin arziki mai kyau, musamman ma ɓangarenta na yawon buɗe ido.
Komai zai dogara kan lafawar rikicin yankin na Gulf.
Ficewar UAE daga Opec zai kara janyo matsin lamba ga Saudiyya.
Lokacin da tankokin dakon man suka sake bi ta mashigin, ko kuma idan har UAE ta sake karfafa batun gina sabbin bututan mai, ƙasar za ta samar da mai ɗin da ba ta taɓa yi ba a baya, ba tare da shamaki ba daga kungiyar Opec.










