Ganduje ya mayar wa Abba Kabir martani

Lokacin da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Abdullahi Ganduje ba ya da ikon ba shi umarni, mutane da dama sun yi mamaki.
Wasu masu sharhi kan siyasa sun yi tunanin cewa hakan ya fara nuna cewa za a iya samun ɓaraka a jam'iyyar, watanni ƙalilan bayan gwamnan na Kano ya yi sauyin sheƙar da ya girgiza siyasar Kano, jiha mafi yawan al'umma a arewacin Najeriya.
Ganduje ya yi mataimakin gwamnan Kano sau biyu, ya yi gwamnan jihar wa'adi biyu a jere sannan ya yi shugaban jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar.
Wannan ya sanya ake kallon sa a matsayin mai matuƙar tasiri a siyasar jihar ta Kano.
Bugu da ƙari shi ne wanda ya karɓi Gwamna Abba Kabir daga jam'iyyar NNPP a watan Janairu.
A hirarsa da BBC, Abdullahi Ganduje ya ce kalaman na Abba Kabir ba su saɓa wa ɗa'ar jam'iyyar APC ba.
'Abin da Abba ya ce ba laifi ba ne'
Tsohon shugaban jam'iyyar na APC ya ce a ɗa'ar jam'iyyar tasu kowane gwamna shi ne jagoran jam'iyyar a jiharsa, don haka wannan ba wani abu ba ne.
''Ai ni ne na fara faɗin haka, domin idan ba a manta ba a lokacin da ya shigo APC na ɗaga hannunsa a gaban duka sauran jiga-jigan jam'iyyar tamu, na kuma ce shi ne jagoran jam'iyyar a jiharmu'', in ji shi.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ci gaba da cewa ''na kuma bayyana a gaban duka ƴayan jam'iyyarmu shi kaɗai ne zai tsaya wa APC takara domin neman wa'adinsa na biyu a jam'iyyarmu''.
''Don haka abin da Abba ya faɗa maimaicin abin da na fara faɗa ne da kaina, ni ai dama ba na ba shi umarni, sai dai na ba shi shawara'', in ji Abdullahi Ganduje.
Ya ƙara da cewa matsayinsa yanzu a APC a Kano bai wuce mamba ba, kuma dattijon jam'iyya, ''kasancewar na girmi kowa sannan ni tsohon gwamna ne to don haka ni ne shugaban dattijan jam'iyyar''.
Murtala Garo: 'An ajiye ƙwarya a Gurbinta'
Dangane da zaɓen Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar, Ganduje ya ce wannan shi ne ya dace.
''Ai an ajiye ƙwarya a gurbinta, kuma dama kaya ne ya tsinke a gindin kaba, kujerar na buƙatar ƙwarewa da gogewa'', in ji shi.
An sai kai ruwa rana kafin a zaɓi Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan jihar, bayan murabus ɗin Aminu Abdussalam Gwarzo.
Ɓangarorin jam'iyyar APC da dama na jihar sun yi ta hanƙoron gwamnan ya zaɓa daga cikinsu, har ma a wani zama da suka yi suka gabatar da masa da sunayen mutum uku, ciki har da Garo domin zaɓar ɗaya a cikinsu.
To amma Ganduje ya ce Murta Sule Garo ya fi duka sauran cancanta da ƙwarewar aiki da kuma gogewa.
''Idan kika duba ya yi shugaban karamar hukumar, sannan ya riƙe muƙamin kwamishinan ƙananan hukumomi, don haka yana da ilimin gudanar da mulki'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
'Yadda na ji bayan komawar Gawuna ADC'

Asalin hoton, Aminu Dahiru Aminu/Facebook
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A farkon watannan nan ne tsohon mataimakin Ganduje lokacin da yake gwamna, kuma wanda ya yi wa APC takarar gwamna a zaɓen 2023 ya fice daga jam'iyyar APC zuwa ADC ta haɗakar ƴan hamayya.
Ficewar tasa daga APC ta bai wa mutane da dama mamaki, musamman komawarsa ƙarƙashin tsohon gwamnan Kano, jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u kwankwanso babban abokin hamayyar Ganduje.
To amma Ganduje ya ce hakan bai zo masa da mamaki ba, la'akari da siyasar zamani.
"Ni a fahimtata da siyasa bai min laifi ba, bai kuma yi min butulci ba, domin dimokradiyyar zamani ra'ayi ne kuma ra'ayinsa ne'', in ji shi.
Tsohon gwamnan na Kano ya ce ba bata wa aka yi da Gawuna ba, ba kuma faɗa aka yi da shi ba.
''Watakila ya ga gwamna ya shigo APC, kuma babu damar yin takara, kuma wataƙila yana ganin idan ya je wata jam'iyyar zai samu damar hakan'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Masu bibiyar siyasar jihar dai na ganin cewa haɗewar Kwankwaso da Gawuna kamar barazana ce ga jam'iyyar APC a jihar.
To amma Ganduje ya kore wannan tunani.
''Ai dama ya taɓa aiki da Kwankwaso har ya yi masa kwamishina, kuma haɗewarsu yanzu ra'ayinsu ya zo ɗaya, amma ba na ganin haɗewar tasu za ta yi tasiri kamar yadda su suke zato'', in ji shi tsohon shugaban APCn na ƙasa.
Wane ne Abdullahi Ganduje?
An haifi Abdullahi Umar a kauyen Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano a 1949.
Ya fara karatun Kur'ani da Islamiyya a kauyensa inda ya samu ilimin addini.
Daga nan kuma ya shiga makarantar firamare ta Dawakin Tofa daga 1956 zuwa 1963.
Ganduje ya fara makarantar sakandaren Birnin Kudu daga 1964 kuma ya kammala ta a 1968.
Bayan nan, Ganduje ya shiga makarantar horar da malamai da ke Kano tsakanin 1969 zuwa 1972 inda ya shiga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna.
Ya kammala karatun jami'a a fannin ilimi cikin shekarar 1975.
A 1979 ne kuma ya kammala digirinsa na biyu daga Jami'ar Bayero ta Kano sannan ya kara komawa Ahmadu Bello daga 1984 zuwa 1985 don karantar ilimin tafiyar da gwamnati.
A shekarar 1993 ne ya samu digirin-digirgir daga Jami'ar Ibadan.
Ganduje ya shiga jam'iyyar NPN a janhuriyya ta biyu sannan ya zama mataimakin sakatare na jihar Kano daga 1979 zuwa 1980.
Ya tsaya takarar wakiltar Kano a zauren majalisar wakilai a 1979 a jam'iyyar NPN amma bai yi nasara a zaben ba.
A shekarar 1998 ya shiga jam'iyyar PDP inda ya nemi jam'iyyar ta tsayar da shi takarar gwamna, amma bai yi nasara ba bayan da PDPn ta tsayar da Rabi'u Musa Kwankwaso.
An zabi Ganduje a matsayin mataimakin Gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso tsakanin 1999 da 2003. Baya ga haka, an nada shi a matsayin kwamishinan kananan hukumomi.
Daga shekarar 2003 zuwa 2007, ya rike mukamin mai bai wa ministan tsaro na Najeriya, wato Rabi'u Kwankwaso, shawara ta musamman a bangaren siyasa.
An zabi Ganduje a matsayin shugaban kwalejin fasaha a Ado Ekiti a 2008 daga nan kuma aka nada shi a matsayin babban sakataren Hukumar Kula da Tafkin Chadi da ke Ndjamena.
Ya kuma kasance daga cikin wadanda suka halarci taron yi wa tsarin siyasa a Najeriya garambawul a 2006.
Kwankwaso da Ganduje sun kuma yi rashin nasara a zaben da suka nemi ta-zarce inda Malam Ibrahim Shekarau ya samu nasara.
An sake zabar Kwankwaso da Ganduje ranar 27 ga watan Afrilun 2011 inda aka rantsar da su ranar 29 ga Mayun 2011 domin karasa zangon mulkinsu na biyu.
Bayan kammala wa'adinsu na biyu, Ganduje ya tsaya takara, kuma ya samu nasarar lashe zaɓen gwamnan a shekara ta 2015, inda ya yi mulki na wa'adi biyu a jere har zuwa 2023.
Dayan sauka gwamna ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Ganduje shugaban jam'iyyar APC mai mulki na ƙasa.
Sai dai bayan kwashe kusa shekara biyu yana jagorancin jam'iyyar, Ganduje ya sauka daga muƙamin bisa dalilai na neman lafiya.











