KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a kan Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya na ranar 30/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Rundunar ƴansandan Najeriya ta kori jami'inta da ya kashe matashi a Delta

    NIGERIA POLICE

    Asalin hoton, NIGERIA POLICE

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce ta kori wani jami'inta da ke dannu a kisan wani matashi Mene Ogidi a yankin Effurun da ke jihar Delta a Kudu Maso Kudancin ƙasar.

    Rundunar ƴansandan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, ta ce an sallami jami'in mai suna ASP Nuhu Usman bayan kammala bincikenta kamar yadda babban sufetan hukumar Tunji Disu ya ba da umarni.

    A wata sanarwa a ranar Laraba mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, DCP Anthony Placid, ta ce an kama Ogidi mai shekaru 28 ne a lokacin da yake yunkurin aika wani saƙo da ake zargin bindiga ce da harsashi hudu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar shi.

    Hukumar ta ce bayan samun waɗannan rahotannin ne, aka dauƙi matakin mayar da binciken zuwa hedikwatarta da ke Abuja babban birnin ƙasar.

    "Bincike ya nuna cewa cewa, jami'i ASP Nuhu Usman ya aikata laifin da ya ci karo da dokokin hukumar na 237 da kuma amfani da makami ba bisa ƙa'ida ba," in ji sanarwar.

    "Abin da ya aikata, rashin ƙwarewa ne da kuma cin amanar rantsuwar da ya yi na kare rayuwar al'umma da dokokin ƙasa".

    Rundunar ta ƙara da cewa bayan kammala matakan da suka dace, za a miƙa jami’an da abin ya shafa ga hukumomin shari’a da suka dace domin gurfanar da su.

  2. Tinubu ya ɗaga darajar Bianca Ojukwu zuwa ministar harkokin wajen Najeriya

    Bianca Ojukwu

    Asalin hoton, Bianca Ojukwu/Insta

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Bianca Odumegwu-Ojukwu a matsayin ministar harkokin wajen ƙasar, bayan murabus ɗin Yusuf Tuggar, wanda ya ajiye mukaminsa domin shiga takara a zaɓen 2027.

    Bianca ita ce ƙaramar minista a ma'aikatar kafin wannan sabon matsayin.

    Kamar yadda wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ta bayyana, an kuma naɗa Sola Enikanolaiye a matsayin ƙaramin minista a ma'aikatar, inda za a jira amicewar majalisar dattawa.

    Kafin a naɗa shi muƙamin, Enikanolaiye wanda haifaffen jihar Kogi ne, shi ne babban mataimaki na musamman ga shugaba Tinubu kan harkokin ƙasashen waje.

  3. Yau kotun ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan rikicin shugabancin ADC

    ADC

    Asalin hoton, ADC

    Nan gaba a yau Alhamis ne ake sa ran kotun ƙolin kasar za ta yanke hukunci kan shari'ar rikicin shugabancin jam'iyyar hamayya ta ADC.

    Hukuncin dai zai fayyace makomar jam'iyyar musamman hamayyar shugabanci tsakanin bangaren Sanata David Mark da kuma bangaren Nafiu Bala Gombe.

    Tun da fari dai jam'iyyar hamayya ta ADC ta fara neman a gaggauta yanke hukunci kan saɓanin da take ciki kan sahihancin shugabancinta, lamarin da za a iya cewa ya tsayar da harkokin jam'iyyar cak.

    Ana dai ganin jam'iyyar ADC ce babbar wadda za ta yi hamayya da jam'iyya mai mulki ta APC, musamman ganin irin manyan ƴansiyasar da ke cikin jam'iyyar da kuma tarihin su.

    Wani abu da ya ƙara ɗaukar hankali shi ne yadda ADC da PDP da wasu jam'iyyun hamayya suka haɗu, suka tattauna tare da ayyana ƙudurinsu na tsayar da ɗantakara ɗaya da zai fafata da Bola Tinubu a zaɓen na 2027.

    Sai dai ADC na ta fama da rikicin gida, inda yanzu haka ake Kotun Ƙoli, inda ake sauraron hukuncin da za ta yanke.

  4. Farashin ɗanyen mai ya yi tashin da bai taɓa yi tun daga 2022

    Fetur

    Asalin hoton, Costfoto/NurPhoto via Getty Images

    Farashin ɗanyen mai ya ci gaba da tashin gwauron zabi ba ƙaƙƙautawa - inda ya kai matakin da bai taɓa kaiwa ba na ƙoli- tun bayan da aka fara yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran a ƙarshen watan Fabarairu.

    Samfurin Brent - wanda shi ke zaman ma'auni ya ɗan haura dala 126 a kan duk ganga ɗaya, yayin da ake nuna damuwa kan tsawon lokacin da yakin zai ƙare.

    Wannan ya biyo bayan bayanan da aka samu ne cewa Shugaba Trump na tattaunawa da shugabannin harkar makamashi, kan yuwuwar tsawaita, rufe tasoshin jiragen ruwa na Iran da zirga-zirgar jiragen - tsawon watanni.

    Iran ta hana wucewar jiragen ruwa ta Mashigar Hormuz - wadda ta nan ne kusan kashi daya bisa biyar na yawan mai da iskar gas da ake amfani da su a duniya ke bi.

  5. Amurka na tuhumar gwamna a Mexico da safarar miyagun ƙwayoyi

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta ce ta tuhumi gwamnan jihar Sinaloa na kasar Mexico, mai ci - da laifin zargin hada baki da shugabannin kungiyar Sinaloa mai safarar miyagun kwayoyi, domin safarar tarin kwayoyi.

    Baya ga Rúben Rocha Moya, akwai kuma wasu jami'an na Mexico su tara - wadanda suke rike da mukamai a yanzu da kuma wadanda suka sauka, da su ma aka tuhuma.

    Wakilin BBC ya ce a tsakiyar wannan tuhuma ta gwamnatin Trump, shi ne zargin cewa Mista Rocha na amfani da wani bangare da kungiyar ta Sinaloa domin a zabe shi Wannan, wata babbar tuhuma ce da Amurka ta yi a kan safarar miyagun kwayoyi, wadda za ta iya kara tsamin dangantaka tsakaninta da Mexico.

    Shi dai gwamnan da wannan tuhuma ta shafa - Mr Rocha,wanda dan jam'iyyar Shugaba Claudia Sheinbaum ne, Morena, ya musanta tuhumar.

  6. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barkan ku da safiyar ranar Juma'a. Da fatan za mu samu albarkacin da ke cikin wannan rana. Allah ya sa hakan.

    Kamar kullum yau ma mun sake dawo muku da shafin BBC Hausa na kai tsaye inda muke kawo muku labarai da rahotanni dangane da irin wainar da ake toyawa a yaƙin Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu.