Karo na 7: Yadda takara guda shida da Atiku Abubakar ya yi a baya suka kasance

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A tsawon shekara 30 da 'yan kai da suka gabata, tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya kasance cikin duk harkokin siyasar da aka yi kasar.

Ya dade yana fafutikar siyasar tare da yunkurin neman shugabancin kasar mai dimbin al'umma da tarin arziki.

Ya yi takara a jam'iyyar SDP da PDP da APC da AC, amma fitaccen dan siyasar bai kai ga gaci ba.

A yanzu ya sake samun tikitin takara, wanda wannan ne karo na bakwai da yake takara, bayan lashe zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar ADC domin yin takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen ƙasar na 2027.

A lokacin sanar da sakamakon zaɓen fitar da ɗan takarar, Atiku ya samu jimillar kuri'a 1,846,370, inda ya kayar da sauran ƴan takara biyu - Rotimi Amaechi da kuma Muhammed Hayatu-Deen.

Rotimi Amaechi ne ya zo na biyu a zaɓen inda ya samu kuri'a 504,117, sai Muhammed Hayatudden a matsayi na uku da kuri'a 177,120.

A ranar Litinin 25 ga watan Mayu jam'iyyar ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin a jihohi na Najeriya da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

Wannan ya sa BBC ta duba lokutan da ya yi takara da yadda suka kaya.

1993: SDP zaben fid da gwani da Abiola

A lokacin da aka yi yunkurin komawa mulkin dimokuradiyya a zamanin mulkin Ibrahim Babangida na soja ne Atiku ya gwada sa'arsa ta takarar shugabankasa.

Ya yi takarar ne na shugabancin Najeriya a jam'iyyar SDP, inda ya fafata zaben fitar da gwani da Moshood Abiola da Ambasada Babagana Kingibe.

A zaben fitar da gwanin da aka yi a Jos, Abiola ne ya yi nasara da kuri'a 3,617 Atiku ya samu kuri'a 2,066.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa daga bisani Atiku ya janye tare da bukatar mutanensa su goyi bayan Abiola.

Zaben ne ya yi fice da sunan babban zaben June 12 da aka soke.

2007: Takara tare da Yar'Adua a AC

A lokacin da aka shiga Jamhuriyya ta hudu, sai Atiku ya tsaya takarar gwannan jiharsa ta Adamawa, amma sai Olusegun Obasanjo ya dauke shi a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Sun yi a aiki tare daga 1999 zuwa 2007, inda ya yi yunkurin maye gurbin shugaban, amma abin ya ci tura. Sai ya koma jam'iyyar AC ya yi hadaka da Bola Tinubu, inda ya fafata Umaru Musa Yar'Adua na PDP.

Bayan kada kuri'a ne INEC ta sanar da Yar'Adua a matsayin wanda ya yi nasara da kuri'a 24,638,063, sai tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari na jam'iyyar ANPP ya zo na biyu da kuri'a 6,605,299, sannan Atiku ya zo na uku da kuri'a 2,637,848.

2011: Fafatawar Atiku da Goodluck Jonathan a zaben fitar da gwani na PDP

Atiku ya sake komawa PDP domin fafatawa da wanda ke kan kujerar shugabancin kasar a lokacin wato Goodluck Jonathan domin samun tikitin jam'iyyar a zaben 2011.

Zaben ya dauki hankali ne saboda ana tunanin zamanin 'yan arewa ne domin karasa wa'adin Umaru Musa Yar’Adua da ya rasu yana mulki.

A karshe dai a zaben fitar da gwanin, Jonathan ya samu nasara da kuri'a 2,736, shi kuma Atiku ya samu kuri'a 805.

2015: Buhari ya doke Atiku a zaben fitar da gwanin APC

A shekarar 2014, Atiku ya fice daga PDP ya shiga sabuwar jam'iyyar hadaka ta APC da aka hada domin fuskantar Jonathan.

A zaben fitar da gwanin wanda aka yi a Legas, Muhammadu Buhari ne ya lashe da kuri'a 3,430.

Rabiu Musa Kwankwaso ya zo na biyu da kuri'a 974, sannan Atiku ya zo na uku da kuri'a 954.

Wannan hadakar ce ta kayar da Jonathan a zaben 2015.

2019: Atiku da Buhari

Bayan zaben ne Atiku ya sake komawa PDP, inda ya samu tikitin tsayawa takara domin fafatawa da Buhari.

A karshe Muhammadu Buhari ne ya sake samun nasara da kuri'a 15,191,847, shi kuma Atiku ya samu kuri'a 11,262,978, kamar yadda INEC ta sanar.

2023: Shan kaye a hannun Tinubu

A zaben 2023 Atiku ya sake tsayawa a jam'iyyar PDP, inda ya fafata da dan takarar APC, Bola Tinubu, da kuma Peter Obi na Labour sai kuma Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP.

A karshe dai Tinubu ne ya yi nasara da kuri'a 8,794,726, Atiku ya zo na biyu da 6,984,520, Obi ya zo ba uku da kuri'a 6,101,533 sai Kwankwaso ya samu kuri'a 1,496,687.

2027: Tikitin ADC

Tuni dai bayan gwagwarmaya da kai-komo kan makomar jam'iyyar hadaka to ADC, yanzu Atiku ne dan takarar jam'iyyar da zai fafata a babban zaben 2027.

Daga takara a jam'iyyar SDP a 1993 zuwa yanzu, Atiku ya tsaya takara a jam'iyyun SDP da AC da APC da PDP.