Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Abin da ya sa ba na cin naman layya duk da ni Musulma ce'
- Marubuci, Marve Kara-Kaska
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Turkish
- Aiko rahoto daga, London
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Nakan yi duk abin da kowa ke yi. Nakan sanya sabbin kaya, nakan ƙawata gidana, nakan ziyarci iyayena, mukan ci abubuwa da dama a tare da duk wani abin da kowa ke yi. Ba na jin kamar akwai wani abu da na rasa."
Aisha Younes ƴar shekara 30 da ke zama a ƙasar Wales ta bayyana kanta a matsayin Musulma wadda ba ta cin nama.
Ta bayyana cewa Idi lokaci ne na sadaka da sadaukarwa ga ƴan'uwa da abokan arziki.
"Nakan taimaka wa ƙungiyoyin bayar da tallafi da kuɗi, sauran mutane na iya yin irin tasu sadakar. Amma a nawa ɓangaren nakan gamsu cewa na sauke nauyin da addini ya ɗora min," in ji ta.
BBC ta tattaunawa da Musulmai wadanda ba sa cin nama a sassa daban-daban na duniya kan yadda suke bukukuwan sallar layya, lokacin da Musulumai ke yanka dabbobi domin yin layya, kuma ake yin badago da nama.
Fawzia Jafan wadda ke zaune a birnin Beirut na ƙasar Lebanon ta ce ta kasance mai ƙaunar dabbobi tun tana ƙarama.
Ta ce tana shiga mawuyacin hali a lokacin da ta ga ana yanka dabbobi sa'ilin bukukuwa na addini.
"Na tabbatar cewa akwai yara da yawa waɗanda ke shiga cikin tashin hankali idan suka ga ana yanka dabobi, to amma ba mu da ƴancin cewa me ya sa aka yi hakan," in ji ta.
Fawzia ta zama cikakkiyar mars cin nama ne a lokacin da ta kai shekara 18, inda ta koma cin abincin da ya unshi ganyaye da kayan itatuwa kawai sa'ilin da ake kullen cutar korona.
Akwai irin nau'in wadannan mutane biyu, sai dai abu aya da ya haa su shi ne ba sa cin nama kwata-kwata.
Sai dai yayin da wadanda ake kira 'vegetarians' ke iya shan madarar dabbobi, waanda ake kira 'vegans' ba sa cin komai da ya jiɓanci dabbobi.
Fawzia ta yi imanin cewa zaman ta wadda ba ta cin duk wani abu da ya fito daga dabbobi bai ci karo da tanade-tanaden Musulunci ba. Hasali ma, tana ganin cewa addini na matuƙar bayar da muhimmanci kan walwalar dabbobi.
A nata ra'ayi, maƙasudin sallar layya shi ne mutum ya sadaukar da wani abu mai matuƙar muhimmanci a gare shi domin taimaka wa mabuƙata.
Ta ce wani abu da zai iya maye gurbin nama shi ne abincin da aka samar da tsrirrai, wanda zai iya daɗewa mabuƙata na amfani da shi.
Ta kuma bayyana cewa hakan na rage illa ga muhalli ta hanyar rage ayyukan masana'antun dabbobi da kuma alkinta ruwa.
Zahra Albistan, ƴar ƙasar Turkiyya wadda rungumi haramta wa kanta cin nama daga bayanan da ta samu ta shafukan sada zumunta ta ce abubuwan da ke faruwa a lokacin sallar layya kan tayar mata da hankali ta wani fannin.
"Saboda akwai wani abu da nake matuƙar martabawa, amma kuma ana ɗaukar mataki a kansu, hakan na jefa ni cikin damuwa matuƙa," a cewarta.
Ta ce a ganin ta maƙasudin Idi shi ne ka sadaukar da abu mai muhimmanci gare ka.
Ya ake cin abinci lokaci sallar layya?
A lokacin sallar layya, ƴan'uwa da abokai kan taru a wuri ɗaya domin cin abinci, kuma wannan abu ne mai muhimmanci gare su.
Marasa cin nama sun ce su ma sukan shiga cikin irin wannan tarurruka, sai dai sukan yi taka-tsantsan.
Aisha ta rungumi rayuwar rashin cin nama tun shekara ta 2015, ta ce da farko ƴan'uwanta sun damu da halin da za ta iya shiga saboda haramta wa kanta cin nama, amma a yanzu abin ya zame musu jiki.
"Mahaifiyata kan tambaye ni me nake son ci da daddare. Takan tabbatar cewa ban rasa abin da zan ci ba," in ji ta.
Abin da nake ci lokacin idi
"Hatta surukaina suna hada min irin nawa abincin na daban," in ji Aisha. Asalinsu sun fito ne daga Hong Kong kuma mafi yawan abincinsu ya ƙusnhi nama ne da kifi... to amma yanzu sukan yi min kara domin samar min abincin da nake so".
Zahra ta ce abincin gargajiya na mutanen Turkiyya ya kunshi abubuwa da dama.
"Nakan ci ganyayyaki da man zaitun," in ji ta. "Mahaifiyata kan girka nau'in abincin baklava, amma irin wanda babu nama a ciki."
Sai dai Zarah ta ce ta sha jin ana yin wasu ƴan ƙananan maganganu a cikin dangi, sai ka ji wasu na cewa: "Me ya sa ba za ki ci abinci ba? ko, me ya sa ba za ki ci ba yanzu amma kada ki ci a sauran ranakun? ko, ki ci na yau kawai..."
Fawzia wadda ke rayuwa a ƙasar Lebanon ta ce a farko-farkon lokacin da ta rungumi wannan dabi'a ta ɗan shiga damuwa, saboda ana kallon ta a matsayin "yarinyar da ba ta son a yanka dabbobi ranar Idi," a kan haka na daina zuwa gidajen ƴan'uwa.
"Amma yanzu na saba, a matsayina ta ƴar fafutika, a matsayina ta ɗan'adam, a matsayina ta wadda ba ta cin nama...yanzu ina da ƙarfin gwiwa fiye da baya. Na gano yadda zan riƙa gabatar da hujjojina," in ji Fawzia.
Fawzia ta ce a halin yanzu muhawarar da ake yi kan sauyin yanayi ta sanya mutanen da ke kusa da ita sun fara sauya abubuwan da suke ci.
Ta ce a yanzu wasu daga cikin makusantanta sun fi karkata kan cin ganyayyaki.
"A matsayina ta Musulma mai hanƙoron hana cin nama, abin da nake cewa shi ne bai zama dole ba a ce sai mutum ya ci nama a wannan zamani da muke ciki," in ji Aisha.