Atiku ya kai wa Amaechi ziyara bayan lashe zaɓen fitar da ɗan takarar ADC
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar wanda ya lashe zaɓen fitar da ɗan takar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a ranar Laraba, ya kai ziyara ga abokin karawarsa tsohon ministan sufuri na ƙasar Rotimi Amaechi.
A lokacin sanar da sakamakon zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a ranar Laraba, shugaban jam'iyyar na ƙasa David Mark ya ce Atiku ne ya lashe zaɓen, inda ya samu ƙuri'a 1,846,370, inda ya kayar da mai biye masa Rotimi Amaechi da kuma wanda ya zo na uku Muhammed Hayatu-Deen.
Bayan sanar da sakamakon an yi ta raɗe-raɗin abin da zai biyo baya ganin cewa tun kafin a sanar da sakamakon ne sauran ƴan takarar suka nuna rashin gamsuwa da yadda ake tattara sakamakon.
Sai dai a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X da yammacin yau Alhamis, Atiku ya ce: "A wannan rana na kai wa ɗan'uwana kuma abokin tafiya, tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi ziyara a gidansa da ke Abuja.
"Mun yi tattaunawar gaskiya-da-gaskiya kan mawuyacin halin da ƙasarmu ke ciki, ƙaruwar matsin tattalin arziƙi, rashin tsaro da kuma buƙatar da ake da ita ta gaggawa wajen ganin an ceto ƙasar daga gocewa daga kan hanya da kuma faɗawa cikin mugun hali," a cewar Atiku wanda ya wallafa saƙon tare da hotunansa tare da Amaechi suna raha.
Ana kallon ziyarar a matsayin wani mataki na neman sulhu da Amaechi a siyasance bayan abin da ake ganin zai iya zama babbar matsala ga tafiyar manyan ƴan siyasar na hamayya waɗanda suka shiga jam'iyyar ADC da nufin ƙalubalantar shugaban Najeriya mai ci, Bola Tinubu a babban zaɓen ƙasar na 2027.
Shi ma ɗan takaran da ya zo na uku a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar ta ADC Mohammed Hayat-Deen ya yi ƙorafi kan zaɓen.
Masana da dama sun yi fargabar cewa za a iya samun ɓaraka bayan zaɓen fitar da gwani na jam'iyyu, kasancewar waɗanda suka gaza yin nasara a wasu lokutan kan fice zuwa wasu jam'iyyu na daban.