Wurin da ake tsare masu ƙiba a China

    • Marubuci, Sarah Bell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Digital Health
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Wani faifan bidiyon ya nuna yadda wasu jerin mutane daban-daban suna motsa jiki a cikin wani babban ɗakin wasanni, sun jeru a wajen cin abinci da kwanciya da aka wallafa a kafafen sada zumunta.

Shirin motsa jikin na baya-bayan nan ba wai wuraren tausa ba ne, ko kuma wajen rage ƙiba na wani sansani sojoji a China. Wasu na bayana shi da kurkukun masu ƙiba, inda suke fuskantar takurar takaita cin abinci sau biyu a matsayin jadawalin rage ƙibar.

Wasu daga cikin kafafen yaɗa labarai na China sun ce akwai sansani irin waɗannan kusan 1000 a faɗin China, da mutane suke fuskantar irin wannan matsala ta ƙiba.

Da dala ɗari shida za ka iya neman gurbin zaman a wannan sansani, inda za a ba ka wurin kwana da abinci da horon na rage kiba.

Wata mai shirya bidiyo TL Huang, ta wallafa yadda ta shiga irin wannan sansani, a kafar sada zumunta ta Instagram, ta kuma shaidawa BBC cewa wajen ya kasance tamkar kurkuku, saboda ba ta bar wurin ba har na tsawon kwana 28, kuma sai da ta kula soosai wajen rage ƙibarta.

"Masu ba mu horo na sa ido akan mu, domin tabbatar da cewar ba mu faki ido ba wajen shigo da abinci masu sa ƙiba ba, da tabbatar da cewar mun halarci dukkan ajujuwan motsa jiki, ba sa bari mu tsallake ko da guda ɗaya, ko barin sansanin ba tare da wani ƙwakkwaran dalili ba" a cewar ta.

Sai dai yayin da Huang ta ce ta ga tsariri zaman da ta yi a chan, masu kula da cimma ka na cewar tsauraran matakai na tafe da hadari ga lafiya da shafar tunani.

Luke Hannan wani ƙwarare a fannin cimaka ya ce " wasu sansanin na kayyade rage kilo guda na ƙiba a koyaushe. hakan kum ayawuce ƙa'idar da aka shimfiɗa na rageƙiba ba tare da jefa rayuwar babba cikin hadari ba, ƙarƙashin kulawar masana harkokin lafiya".

To yaya ake tafi da irin wadan annan sansanin, kuma ta yaya suka zama fitattar aka sansu?

'Lokaci ya yi na sauyi'

Huang ta ce ta fara samun labarin sansanin ragekibar ne daga wajen mahaifiyar ta, wadda ƴa China ce. ta kasance ta yi fama da rashin lafiya, bayan da ta yi wata tafiya zuwa China, ta sauka daga kan tsarin da ak dorata ta cika cikin ta da abinci da ta sa oda aka kawo mata.

Sama da shekaru uku Huang ta ce ta ƙar aƙiba da kilo 20, wand ahakan ya janyo mata magangau a dangi, wanda hakan kuma ya sa ta shiga damuwa, a wannan lokacin na ji cewar lallai lokacin sauyi ya zo.

"Sai na ji kamar anan cimun zarfai don na yi ƙiba. Sai dai dai lokacin kuma, in atunanin sun ƙoƙarin nuna mun soyayyarsu mai tsauri gare ne" a cewar ta.

Ziyartar irin wannan sansani babbar "kaɗuwa ce ta al'ada" sai dai Huang ta ce akwai wanda da suka zo su ma don rage ƙibar inda suka himmantu wajen ganin sun cimma haka, tare da juna.

A kowacce rana ana fra motsa jiki da ƙarfe 7:30 na safe, inda ake farawa da mitsa jijki na tsawon sa'o'i 4, da ajujuwan tsere da sauran nau'in motsa jiki iri-iri. sai ɗaga kaya ƙarfi da nauyi don tabbatar da zabge ƙiba cikin hanzari.

abincin karin kumallo kuma dafafen ƙwai n eguda 4, sai rabin tumatir, da gurji (kukamba) guda biyu. A wani bidiyo Huang ta ce abincin ranar ta bai wuce gyararriyar ƙaguwa, da ganyayeki da aka turara, dai wake, da kifin sai ba, cauliflower.

Ta ce aminci na da dai kuma an samar da dukkan ƙa'idar dai-daita abinci mai gina jiki, a bisa tsarin abinci China.

Ana s a ran baƙi zasu iya shiga cikin jerin masu motsa jiki ne kai a zango na ƙarshe kafin a ci abinci dare, wato kafin lokacin gwada nauyi da ake yi dukkan ƙarfe 7:30 na dare, sannan sai a je a yi wanka a huta.

Huang ta ce atisayen ya kasance abin doki a makon farko, sai dai daga baya sai ta fahimci cewar akwai buƙatar ta sake jira zuwa makonni uku. saƙonnin da ƙawayenta ke tura mata ne kawai ya sa ta jure ci gab ada zama.

Duk da yadda ta bayyana yadda zauren motsa jiki yake da kurkuku, Huang n ada ƙwarin guiwar cewar kwalliya ta biya kudin sabulu domin ta rage kusan kilo 6 a kwanaki 28.

"Ya sa na sami sauyi a rayuwata amma cikin tsauri, sannan na sami surara jikin da ne ke buƙata," a cewar Huang.

' Magance tushen dalilan da ke sa ƙiba '

Sai dai ƙwararu sun yi jna hankali. Matakan da sansanin rage ƙibar ke bi, abu ne da ke bayyana damuwa, saboda idan ana rage kiba, kana rasa tokoki na jiki, da kitse, a cewar wata ƙwarare a fanin motsa jiki a Landan Luke Hanna.

Idan kana amfani da hanyoyin masu tsauri kamara motsa jiki da ya wuce ƙima, to kana jefa kan ka cikin hadarin rasa wasu daga cikin tsokokin ka.

Hakan babbar matsala ce ga yara da matasa da suke age ƙiba ta wannan hanya.

"Kana cikin barazanar haifar da cikas ga wasu ci gab aga lafiya ka, wanda hakan kuma babban hadari ne ga ƙashin bayar lafiyarka, a cewarsa.

Haka kuma zai iya sahfar tunani, da suka haɗa da barazanar wargajewar tsarin cin abinci.

"Yanzu wasu mutane sun rage ƙiba sosai, wanda hakan za ka ga kamar wani abun kirki ne, sai dai da dama daga cikinsu, da wuri za su sake yin ƙibar, da zarar sun ci gaba da rayuwar su yadda suka saba a baya, saboda baa magance ainihin dalilan da suka sa ko haddasa ƙibar ba," a cewarsa.

Hukumar Lafiya ta Birtaniya, ta bayar da shawarar cewar a ringa rage ƙiba da kilo ɗaya.

Hannan ta ce yana da kyau mutane su mayar da hankali wajen rage ƙibarmataki zuwa mataki, musamman ta hanyar kula da abubuwan da ke faruwa a muhallansu, ta hanyar kula da cin abinci mai gina jiki, da cin abinci mai sinadarin gina jiki, da motsa jiki don samun kuzari, da nishaɗi, ba wai tamkar ladabtarwa ba.

Discrimination

An dai kafa sansanin a China ne a farkon shekarun 2000, biyo bayan wani shirin talabijin da aka yi kan yadda ake rage ƙiba, a cewar Wanqing Zhang daga sashen BBC na China. Masu horar da ƴan mosta jiki, ya yanke buɗe wajen rage ƙibar su. Sai dai akwai ƙaruwar irin waɗan nan cibiyoyi da ake ƙara buɗe su, a tsawon shekaru goman nan, sakamakon ƙarruwa kafafen sada zmununta.

"Idan ka je kafafen sada zumunta na China, za ka ga asu shirya bidiyo ko dai suna wallafa cibiyoyin rage ƙiba, ko wadan suka je cibiyoyin motsa jiki don rage ƙibar,a cewar Zhang.

Zhang ya ce zai iya kasancewa rukunin masu yi wa mutane kuɗin goro kamar, inda ita Huang ta je, sai dai ana iya yi masa kallon masta tsauri, tunda akwai kyamar nan ta CCTV a bakin ɗakunan kwana, ko da mutane za su saci jiki su shiga da abinci masu saka ƙiba.

Ginshiƙin ƙaruwar ƙiba a duniya dai shi ne, kashi biyu bisa uku na ƙasashe duniya, inda fiye da kashi 50 cikin ɗari na manya ake sa su a jin masu ƙiba, da kuma nauyi.

A cewar hukumomin lafiya a China kashi 34 cikin ɗari na manya da ke ƙasar, na cikin runukun masu nauyi, yayin da kashi 16 cikin dari kuma suke ajin masu ƙiba.

Hakan kuma wakilin BBC Zhang ya ce hakan na da alaƙa da al'ada, "China ƙasa ce da ke da karancin kula da matakan nauyi, inda hakan na nufin cewar idan kan ada nauyi, akwai yiwuwar za ka fusknaci wariya a wajen aiki ko kuma a bangaren soyyayya a duniya.

A ɓangare guda, shafin sada zumuntar Instagram na Huang, ya nuna cewar yanzu tana Thailand, ta sake shiga wani shirin rage ƙiba na kwanaki 30, inda ta ke motsa jiki na sa'o'i biyu a rana saboda tsananin zafi.