Salah zai koma Trabzonspor, Bayern na zawarcin Sesko

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan gaban Masar mai shekara 34, Mohamed Salah na shirin komawa ƙungiyar Turkiyya Trabzonspor duk da cewa ya yi tattaunawar baki da Besiktas bayan barin Liverpool. (Foot Mercato)
Bayern Munich na son ɗauko ɗanwasan gaban Manchester United mai shekara 23, Benjamin Sesko, domin fatan haɗa shi wasa tare da ɗanwasan gaban Ingila mai shekara 33, Harry Kane, a ƙungiyar.(CF Bayern Insider)
Ɗanwasan bayan Aston Villa da Ingila mai shekara 28, Ezri Konsa, na sha'awar komawa taka leda a Arsenal.(Caught Offside)
KocinMan City Enzo Maresca na fatan sake yin aiki da ɗanwasan gefen Chelsea Pedro Neto, bayan sha'awar ɗanwasan Portugal ɗin da ƙungiyar ta nuna. (Sun)
Chelsea da Tottenham sun bi sahun Newcastle a faɗi tashin neman ɗaukar ɗanwasan bayan Atalanta mai shekara 22 Giorgio Scalvini, wanda aka yi wa farashin £42m. (Sun)
Ɗanwasan tsakiyarLiverpool Curtis Jones zai nemi komawa Inter Milan bayan tayin farko da aka gabatar a kan ɗanwasan ya gaza kai ga kammala cinikin. (Teamtalk)
Paris St-Germain ta ƙara ƙaimi kan ƙoƙarin sayen ɗanwasan tsakiyar Ajax, Mika Godts, wanda aka yi wa farashin £52m, kuma ƙungiyoyin gasar firimiya irin su ArsenaldaLiverpooldaManchester United da kuma Tottenhamna bibiyar ɗanwasa. (Teamtalk)
Chelseana shirin tsawaita kwangilarta da Joao Pedro, duk da cewa ɗanwasan Brazil ɗin mai shekara 24 yana da yarjejeniyar taka leda a ƙungiyar har zuwa 2032. (The Athletic)
Manchester Unitedba za ta sayi ɗanwasan gaban Everton Iliman Ndiaye, mai shekara 26 ba, bayan Al-Hilal ta bayyana aniyar biyan £75m da ƙungiyarsa ke neman a biya kan ɗanwasan na Senegal. (Football Insider)
Fulham na fatan ɗaukar ɗanwasan gaban Ireland mai shekara 24, Troy Parrott, daga AZ Alkmaar, amma tana fuskantar hamayya daga PSV Eindhoven da Real Betis da kuma Como. (Talksport)












