Magungunan gargajiya 7 da gwamnatin Najeriya ta samar domin manyan cututtuka

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da sabbin magungunan gargajiya guda bakwai domin taimakawa wajen magance wasu manyan cututtuka.
Hukumar Bunƙasa Magungunan Gargajiya ta Ƙasar (NNMDA) ta samar da magunguan da aka ƙaddamar a ofishinta da ke Legas.
NNMDA ta ce daga shekarar 2023 ta samar da fiye da magungunan gargajiya 22 da aka sarrafa daga tsirrai da ganyayyaki na cikin gida, domin ƴan Najeriya ta amfani da albarkatun ƙasar.
Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Dakta Kingsley Udeh, ne ya ƙaddamar da magungunan yayin wata ziyara da ya kai hedkwatar hukumar da ke Legas a ranar Talata.
Sai dai wannan mataki na gwamnatin Najeriya na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takun-saƙa tsakanin wasu hukumomin gwamnati da masu sana'ar magungunan gargajiya, saboda zargin cewa wasu daga cikinsu na samar da magungunan da ba a tantance ingancinsu ba, waɗanda kuma ka iya yin illa ga lafiyar masu amfani da su.
Duk da haka, akwai ƴan Najeriya da dama da suka fi amincewa da magungunan gargajiya, musamman idan sun kamu da wasu cututtuka da suke ganin magungunan zamani ba su yi musu tasirin da suke buƙata ba.
To ko waɗannan sabbin magungunan gargajiya da gwamnatin ta ƙaddamar za su iya tabbatar da tasirin da ake sa ran za su yi wajen magance manyan cututtuka?
Me doka ta ce kan haɗa magungunan gargajiya a Najeriya?
A Najeriya, ba a haramta amfani da magungunan gargajiya ba. Sai dai dokokin ƙasar sun tanadi cewa dole ne a tabbatar da ingancinsu, amincinsu da yadda ake sarrafa su kafin a amince a sayar da su ga jama'a.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hukumar NAFDAC ce ke da alhakin yin rajista da kuma tantance duk wani magani da ake son sarrafawa ko sayarwa a Najeriya, ciki har da magungunan gargajiya. Hukumar na duba yadda aka samar da maganin, ingancin kayan da aka yi amfani da su, tsaftar wajen da aka sarrafa shi da kuma yiwuwar yin illa ga lafiyar mutane.
Sai dai yin rajista da NAFDAC ba yana nufin an tabbatar maganin na warkar da wata cuta ba.
Hukumar na yarda ne a sayar da magani idan ya cika ƙa'idojin amfani, amma ba ta amince masu haɗa magungunan su yi tallar cewa maganinsu na warkar da cututtuka masu tsanani kamar kansa, HIV ko ciwon sukari ba tare da hujjojin bincike da suka tabbatar da hakan ba, kamar yadda yake a sashe na 2(1) da na 4 na Dokar NAFDAC kan Rajistar Magungunan Gargajiya ta 2021.
A shekarar 2023 kuma, shugaban ƙasa ya rattaba hannu kan Dokar Hukumar Bunƙasa Magungunan Gargajiya ta Ƙasa (NNMDA), wadda ta bai wa hukumar cikakken iko na gudanar da bincike, bunƙasawa da inganta amfani da tsirrai da domin samar da magungunan gargajiya.
Dokar ta kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin NNMDA, cibiyoyin bincike, jami'o'i da masana'antun magunguna domin a samar da magungunan gargajiya da aka gwada ingancinsu kuma suka dace da ƙa'idojin ƙasa da na duniya.
Duk da haka hukumomin lafiya na ci gaba da gargaɗin jama'a su guji amfani da magungunan gargajiya da ba su yi rajista da NAFDAC ba, ko kuma waɗanda ke yin iƙirarin warkar da kowace irin cuta ba tare da hujja ba.
Manyan cututtukan da gwamnati ta samar wa magani

Asalin hoton, NNMDA/Punch
Ministan Kingsley Udeh da ya ƙaddamar da sabbin magungunan gargajiya guda bakwai da aka samar a cikin gida ya ce gwamnati za ta fara tattaunawa da manyan kamfanonin masana'antar magunguna domin ganin an fara samar da waɗannan magunguna a kasuwa cikin gaggawa.
"Za mu yi aiki tare da shugabannin masana'antun magunguna domin ganin waɗannan kayayyaki sun isa kasuwa, kuma al'umma sun amfana da su," in ji ministan.
A cewar hukumar NNMDA, magungunan sun shafi kula da cututtuka da matsalolin lafiya da suka haɗa da:
- Cutar daji (Cancer)
- Ciwon hanta (Hepatitis B)
- Gyambon ciki (Ulcer)
- Yawan sinadarin cholesterol a jini
- Hawan jini (Hypertension)
- Harkokin jima'i ga maza
Farfesa Emeje ya ce daga cikin magungunan akwai Namdavir, wanda aka samar domin maganin cutar Hepatitis B daga wani tsiron magani na Najeriya.
"Binciken da aka gudanar ya nuna cewa maganin na da tasiri sosai kan ƙwayar cutar."
Akwai kuma Namdacid, domin maganin gyambon ciki. A cewarsa, gyambon ciki na daga cikin matsalolin lafiya da suka fi addabar al'umma.
Farfesa Emeje, ya ce domin tabbatar da inganci da amincin waɗannan magunguna, hukumar na buƙatar gina dakin gwaje-gwaje na musamman da zai taimaka wajen gudanar da binciken kimiyya kan magungunan gargajiya.
Ya kuma buƙaci a gina masauki ga masu bincike, saboda a cewarsa sau da yawa suna shafe sa'o'i masu tsawo suna gudanar da bincike fiye da lokacin aiki na ƙa'ida.
Sai dai Farfesa Emeje ya ce har yanzu akwai mutanen da ba su yarda da magungunan gargajiya ba, duk da yake yawancin al'umma sun fi aminta da su a madadin magunguna zamani na asibiti.
Me ya sa wasu suka fi amincewa da magungunan gargajiya?
Duk da ci gaban da aka samu a fannin kiwon lafiya na zamani, har yanzu akwai miliyoyin ƴan Najeriya da ke ci gaba da amfani da magungunan gargajiya a matsayin mafita ta farko idan ba su da lafiya.
Ana ganin hakan na da nasaba da abubuwa da dama. Na farko shi ne sauƙin samun magungunan gargajiya, musamman a yankunan karkara da cibiyoyin kiwon lafiya ba su da yawa.
Haka kuma, galibin waɗannan magunguna suna da araha idan aka kwatanta da kuɗin zuwa asibiti ko sayen magungunan zamani.
Akwai kuma al'ada. A wasu al'ummomin, an saba amfani da magungunan gargajiya tun shekaru aru-aru, lamarin da ya sa mutane da dama ke ci gaba da dogaro da su saboda abin da suka gada daga iyaye da kakanni.
Wasu kuma sun fi amincewa da magungunan ne saboda sun taɓa samun sauƙi ko waraka bayan amfani da su, musamman kan cututtuka da suka daɗe suna fama da su ko bayan ɗaukar lokaci magungunan asibiti ba su yi musu tasirin da suke so ba.
Ko kwalliya za ta biya kuɗin sabulu?
Babban Daraktan NNMDA, Farfesa Martins Emeje, ya ce binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa yanzu sun kawar da shakkunsu kan tasirin magungunan gargajiya da aka gudanar da bincike a kansu.
A cewarsa, abin da ya rage yanzu shi ne tabbatar da bin ƙa'idojin sarrafa magungunan, domin a san adadin da ya dace a sha kamar yadda ake yi da magungunan zamani.
"Tasirin magungunan gargajiya ba abin tantama ba ne. Yanzu abin da muke yi shi ne tabbatar da an sarrafa su bisa ƙa'ida, tare da ƙayyade adadin da ya dace a sha."
Farfesa Emeje, wanda shi ne mataimakin shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Magungunan Gargajiya a Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), kuma ya ce abin farin ciki ne yadda yanzu ake samar da magungunan gargajiya samfurin ƙwayoyi da magungunan ruwa, maimakon yadda aka saba amfani da su a baya.
A cewarsa, hukumar ta samu gagarumin ci gaba wajen samar da magungunan gargajiya daga tsirran magani na cikin gida domin magance matsalolin kiwon lafiya da ake fuskanta a Najeriya.











