KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 01 ga watan Agustan 2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. Farashin mai ya ƙaru saboda fargabar cikas ga jigilar mai ta Mashigar Hormuz

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyen mai ya tashi a kasuwannin duniya bayan fargabar cewa rikicin da ke yankin zai iya haddasa cikas ga jigilar mai ta Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar da ake amfani da ita wajen safarar mai.

    Farashin ɗanyen mai na Brent ya ƙaru da kashi 1.2 cikin ɗari zuwa dala 90.12 kan ganga, yayin da ɗanyen man Amurka ya tashi da kashi 1.3 cikin ɗari zuwa dala 84.67.

    Hauhawar farashin ta biyo bayan rahotannin cewa an dakatar da wasu jiragen dakon mai ko kuma aka tilasta musu sauya hanya ta mashigar Hormuz.

    Yaƙin Iran ya rage yawan zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar, yayin da barazanar mayaƙan Houthi kan jiragen ruwa a Bab al-Mandab ke ƙara jefa sauran hanyoyin fitar da mai cikin haɗari.

  2. Iran ta ce za ta rufe mashigar Hormuz idan Amurka ta ci gaba da kai hare-hare

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, Ali Akbar Zolghadr, ya ce Iran za ta rufe mashigar ruwa ta Hormuz idan Amurka ta ci gaba da kai hare-hare ko takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.

    Ya gargaɗi cewa hakan zai iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya, kasuwar makamashi da kuma Amurka.

    A lokaci guda, kafofin yaɗa labarai na Iran sun ruwaito cewa Tehran ta shirya wani faɗaɗɗen shiri na mayar da martani idan Amurka ta kai hari.

    Wani babban jami'in tsaro da ba a bayyana sunansa ba ya ce rahotannin yiwuwar harin Amurka da Isra'ila kan Iran "rashin hankali ne", yana mai cewa martanin Iran zai haɗa da kai hari kan muhimman cibiyoyin Isra'ila da na makamashin Amurka a yankin.

  3. Trump ya musanta zargin Iran da kutse kan tsarin samar da ruwa a Minnesota

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce bai yarda cewa Iran ce ke da hannu a kuste ta intanet da aka yi kan tsarin samar da ruwa na jihar Minnesota ba, duk da cewa wasu rahotanni sun nuna cewa wasu jami'an Amurka na zargin Tehran da hannu a lamarin.

    Da yake magana a wani taron majalisar ministocinsa, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito, Trump ya ce: "Mun ji an yi kutse ta intanet a Minnesota kuma ana ɗora laifin kan Iran. Ni ban yarda da hakan ba."

    Maimakon haka, Trump ya dora alhakin kan jami'an jihar da Gwamnan Minnesota mai jam'iyyar Democrat, Tim Walz, ba tare da gabatar da wata hujja da ke goyon bayan zarginsa ba.

    A nasa martanin, Gwamna Tim Walz ya ce Donald Trump ya san waɗanda ke da alhakin kutsen, yana mai ƙara da cewa irin an samu iran waɗannan kusten a wasu jihohin Amurka ma.

  4. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da Safiya

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.