Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasu muhimman lokuta 13 da suka fi ɗaukar hankali a rayuwar Messi
Yayin da Lionel Messi ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasarsa ƙwallon ƙafa bayan rasuwar mahaifinsa, ɓangaren wasanni na BBC ya yi waiwaye kan wasu daga cikin muhimman lokutan da suka fi daukar hankali a rayuwar ɗanwasan na Argentina a fagen tamola.
A ranar Litinin 31 ga watan Agusta kaftin ɗin na Argetina ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasarsa wasa. Messi zai ci gaba da murza leda a ƙungiyarsa ta Inter Miami har zuwa 2028.
Lionel Messi wanda ya taɓa lashe kofin duniya - ya ci wa Argentina ƙwallo 125 a raga a haskawa 207, inda ya zama ɗanwasan da ya fi ci wa ƙasar ƙwallo a raga.
Jimilla ya ci ƙwallo 921 a raga a Barcelona da Paris St-Germain da Inter Miami da kuma Argentina.
Ga wasu muhimman lokuta na Messi a fagen ƙwallon ƙafa.
Cin 'hat-trick' na farko tun yana matashi
A wasan hamayya na El-Clasico Messi ya fara zazzaga ƙwallaye uku rigis wato 'hat-trick' a karawa da Real Madrid.
Messi ya ci ƙwallayen ne yana shekara 19, kuma duk shi ya ci wa Barcelona ƙwallayenta a ragar Real Madrid da suka tashi 3-3 a wasan Clasico a ranar 10 ga Maris na 2007.
Karon farko da ya ci ƙwallo uku rigis a raga a Camp Nou gidan Barcelona - musamman ƙwallo ta uku da ya ci bayan ya yanke ƴanwasan bayan Madrid.
Tun daga lokacin Messi ya fara jan hankalin duniya.
Gwanin yanke irin Maradona
Wata ɗaya bayan ya ci ƙwallaye uku rigis, Messi ya ci wata ƙwallo a raga da ake ganin na cikin mafi shahara a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.
Ya ci ƙwallon ne a wasan da Barca ta doke Getafe 5-2 a wasan dab da ƙarshe na gasar Copa del Ray a ranar 18 ga Afrilun 2007.
Tun daga tsakiyar fili Messi ya zari ƙwallo ya yanke ƴanwasa baya kimanin biyar ya jefa ƙwallo a raga - wani al'amari da ya sa mutane suka tuna zamanin Maradona.
Ƙwallon farko da ya ci a wasan ƙarshe a gasar Zakarun Turai
Wannan na iya zama abin mamaki a yau, can a shekarar 2009 wasu masoya kwallon kafa a Ingila da ƴanjarida sun nuna shakku Messi zai iya yin hakan ga ƙungiyoyin Ingila - bayan ya kasa cin ƙwallo a ragar ƙungiyoyin Ingila a gasar Zakarun Turai a haskawa 10.
Amma wannan shakkar ta kau, lokacin da Messi ya yi tsalle ya jefa ƙwallon da Xavi ya ba shi ta sama a ragar Manchester United - kuma wasan da ake ganin ita ce ta haifar da hamayyar farko tsakanin Messi da Cristiano Ronaldo.
Bayan shekara biyu zai sake zura ƙwallo a raga da ya samu nasara kan tawagar Sir a wasan ƙarshe a gasar Zakarun Turai.
Zura ƙwallaye huɗu a ragar Arsenal
Karon farko da Messi ya ci ƙwallo hudu a rayuwarsa ta tamaula inda ya Barcelona ta doke Arsenal a zagayen kwata fainal ci 4-1 a shekarar 2010.
Sannan ya sake irin wannan bajintar ta zuba ƙwallaye a raga bayan shekara biyu a wasan da Barcelona ta lallasa Bayer Leverkusen 7-1
Shi ne ɗanwasan da ya fi yawan ƙwallaye a gasar Zakarun Turai da 129, bayan Ronaldo.
Tarihin wanda ya fi yawan cin ƙwallo a Barcelona
Messi yana shekara 24 ya kafa tarihin wanda ya fi yawan cin ƙwallo a raga a Barcelona.
Ya kafa tarihin ne a wasan da Barcelona ta lallasa Granada 5-3 a ranar 20 ga Maris din 2012.
Ya yi kafaɗa da Cesar Rodriguez da ya ci kwallo 232.
Kafin ya bar Barcelona 2021 jimillar ƙwallayen da ya ci a raga sun kai 672.
Zura ƙwallo 91 a raga a shekara ɗaya
A 2012 Messi ya ci ƙwallo ta 91 a shekara ɗaya a wasan da Barcelona ta doke Real Valladolid 3-1 a ranar 22 ga watan Disamba.
Wannan nasarar ta sa ya shiga kundi tarihi na Guinness Book of Records.
Ya ci wa Barcelona ƙwallo 79 sannan ya ci wa ƙasarsa Argentina 12.
A shekarar ne ya lashe kyautar Ballon d'Or karo na huɗu a jere- duk da cewa Copa del Rey kawai ne kofin da ya lashe duk da yawan ƙwallayen da ya ci a 2012.
Tarihin yawan cin ƙwallaye a La Liga
Wannan ne karo na biyu da Messi ya kafa tarihi ta hanyar cin ƙwallo uku a lokaci guda.
Ya ci kwallo uku a wasan da Barcelona ta yi nasara 5-1 kan Sevilla a ranar 22 ga Nuwamban 2014 inda ya zama ɗanwasan da ya fi yawan cin ƙwallo a raga a tarihin La Liga
Messi ya yi kafaɗa da yawan ƙwallayen Telmo Zarra 251 a 1955 ɗanwasan gaba na Athletic Bilbao.
Ya kammala da yawan ƙwallaye 474 inda ya sha gaban Ronaldo mai yawan ƙwallaye 311 a Real Madrid.
Tarihin cin ƙwallo ta 500 a Barcelona kuma a El Clasico
Nasarar da Barcelona ta samu kan Real Madrid 3-2 a ranar 23 ga Afrilun 2017 ba za a manta ba a tarihin El Clasico.
Kwallon da Messi ya zura ana dab da hure wasa ta ja hankali. Kwallon da ta ba Barcelona nasara a El Clasico kuma ƙwallon Messi ta 500 a Barcelona goal kuma ta ba Barcelona damar ɗarewa kan teburin La Liga, kodayake Real Madrid ce ta lashe kofin gasar a shekarar.
Bayan ya ci ƙwallon Messi ya cire rigarsa ya ɗaga sama ya nuna wa magoya bayan Madrid a Bernabeu sunansa.
Messi ya yi kuka bayan kawo ƙarshen rayuwa a Barcelona
Abin da ake ganin ba zai faru ba ya faru a watan Agustan 2021 inda Messi ya bar Barcelona.
Bayan shekara 21 da ƙwallaye 672 da kofi 35, dole Messi ya tafi domin ƙungiyar ba ta iya cika sharuɗɗan yarjejeniyar sa saboda tsarin La Liga na takaita albashi.
A wani taron manema labarai Messi ya fashe da kuka.
"Ba na son barin wannan ƙungiyar - wadda nake so, kuma wannan ne lokacin da ban yi tsammani ba."
Duk da alaƙanta shi da Manchester City, daga ƙarshe ya koma Paris St-Germain.
Kofin farko da Messi ya lashe wa Argentina
A ranar 11 ga watan Yulin 2021, Messi - yana shekara 34 - ya lashe kofin farko a Argentina bayan doke Brazil 1-0 a Copa America wasan ƙarshe a Maracana.
Shi ne ya lashe kyautar gwarzon gasar bayan zura ƙwallo huɗu a raga.
Messi ya faɗi ƙasa bayan hure wasan kuma abokan wasan sa suka cira shi sama yayin da suke murnar nasara.
Ya sake lashe Copa America bayan shekara uku.
Nasarar lashe Kofin Duniya
Wannan nasara ce kuma lokacin da ake ganin ba zai taba faruwa ba, ganin cewa Messi ya taba sanar da yin ritaya kafin ya yi amai ya lashe.
Wannan ne babban ƙalubalen da ake alaƙanta shi da sauran zaratan ƴan ƙwallo musamman a muhawarar ɗanwasan ƙwallon ƙafa da ba a taba yi ba a duniya.
Messi ya ci ƙwallo biyu yayin da Argentina ta doke Faransa a bugun fanariti bayan an tashi wasan ƙarshe 3-3
Shi aka ba kyautar gwarzon ɗanwasa a gasar bayan ya ci ƙwallaye bakwai.
Tarihin lashe kyautar Ballon d'Or takwas
Messi ya ci kyautar Ballons d'Or biyu bayan ya bar Barcelona - ɗaya a Paris St-Germain ɗaya kuma a Inter Miami - inda haɗa guda takwas.
Ta ƙarshe da ya lashe ita ce a watan Oktoban October 2023 bayan lashe kofin duniya.
Yawan cin ƙwallo a raga a tarihin Gasar Kofin Duniya - na ɗan lokaci
Duk da gasar cin Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe ga Messi, amma ɗanwasan ya taka rawar gani.
Ya ci kwallaye takwas a gasar inda ya hada jimilla 21 a matsayin wanda ya fi yawan ƙwallaye a tarihin Gasar Cin Kofin Duniya kafin Mbappe ya zarta shi da ke da 22 a wasan neman na uku da Faransa ta doke Ingila.
Messi mai shekara 39, bai yi nasara ba a wasan ƙarshe - inda Argentina ta sha kashi a hannun Spain a wasan ƙarshe - amma tarihin ƙwallon ƙafa ba zai taba mantawa da shi ba.