Matan da za su yi takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2027

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027 ya ƙara ɗaukar harama, inda tuni ƴan ƙasar suka fara tattaunawa kan ƴan takarar da jam'iyyu suka tsayar domin fafatawa, musamman a zaɓen shugaban ƙasa.

Sai dai, bayan fafatawar da ake sa ran za a yi tsakanin manyan 'yan siyasa da jam'iyyunsu, akwai wani batu da ke ƙara jan hankali, wato yadda mata ke ci gaba da fafutukar samun gurbi a mataki mafi girma na siyasar Najeriya.

Tun farko, mata uku ne suka bayyana a matsayin ƴan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyunsu daban-daban.

Sai dai yanzu adadin ya ragu zuwa biyu bayan da Jam'iyyar Young Progressives Party (YPP) ta sauya sunan Anita Zugwai-Chukwu daga matsayin ƴar takarar shugaban ƙasa.

Wannan na nufin cewa duk da ƙarin kiraye-kirayen da ake yi na bai wa mata dama sosai a harkokin siyasa, har yanzu ba su da yawa cikin masu neman shugabancin Najeriya.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, ta sanya ranar Asabar 16 ga Janairun 2027 domin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun dokoki, kuma tuni ta fitar da jerin ƴan takara.

Esther Nkem Okereke

Esther Nkem Okereke na daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasa da ke da ke jan hankali matuƙa a kakar zaɓen bana.

Jarumar fina-finan Nollywood ce kuma mai shirya fina-finai, sannan ƴar kasuwanci ce kuma mai gudanar da ayyukan agaji.

Ta samu tikitin takarar shugaban ƙasa na National Rescue Movement (NRM) bayan babban taron jam'iyyar da aka gudanar a Abuja.

A shafinta na Facebook, Esther ta ce ayyukan da gudanar na jinƙai da taimakon jama'a ne za su taimaka mata wajen gudanar da mulki cikin sauƙi, domin a cewarta, ta san matsalolin Najeriya sosai.

Ta fitar da wani takenta mai suna 'Muradun ESTHER', inda ta bayyana a ciki cewa za ta mayar da hankali kan ilimi da tsaro da kasuwanci da fasaha da sauransu.

Ada Elizabeth Fredrick Okwori

Ada Elizabeth Fredrick Okwori ita ce ƴar takarar shugaban ƙasa ta National Democratic Party (NDP), kuma ƴar asalin ƙabilar Idoma ce daga jihar Benuwe da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

Kafin samun damar zama ƴar takarar jam'iyyar a babban zaɓe, ta taɓa kaancewa shugabar jam'iyyar a matakin ƙasa bayan fafutika da shari'a, inda daga bisani kotu ta ce ita ce shugabar.

A baya ta kasance a jam'iyyar, sannan ta taɓa assasa ƙungiyar siyasa ta Ward2Ward, wadda ke ƙarfafa jama'a su shiga harkokin siyasa tun daga matakin ƙananan hukumomi da mazaɓu.

Mataimakan shugaba ƙasa

Sai dai a wata ƙididdiga da jaridar Daily Trust, ta ce duk da cewa mata biyu ne yanzu suka rage cikin masu neman kujerar shugaban ƙasa, akwai wasu mata da ke cikin tikitin takarar mataimakin shugaban ƙasa.

Hajja Bintu Konto

Hajja Bintu Konto ita ce ƴar takarar mataimakiyar shugaban ƙasa ta Labour Party (LP), tare da ɗan takarar shugaban ƙasa Dr Chibuzo Sunday Okereke.

Ofordile Peace Egobia

Ofordile Peace Egobia ita ce ƴar takarar mataimakiyar shugaban ƙasa ta Action Peoples Party (APP), tare da ɗan takarar shugaban ƙasa Kabiru Yusuf.

Ndidi Patience Key

Ndidi Patience Key ita ce 'yar takarar mataimakiyar shugaban ƙasa tare da Peter Agada, wanda ya maye gurbin Anita Zugwai-Chukwu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na YPP.

Takarar mata a zaɓukan baya

A shekarar 1999, lokacin da Najeriya ta koma mulkin dimokuraɗiyya, babu mace ko guda da ta tsaya takarar shugaban ƙasa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Olusegun Obasanjo na Peoples Democratic Party (PDP) da Olu Falae na Alliance for Democracy (AD) ne suka fafata, inda Obasanjo ya yi nasara.

Sai dai a shekarar 2003, mata sun fi bayyana sosai a takarar shugaban ƙasa.

Daga cikin 'yan takara 20, biyu mata ne: Sarah Jubril ta Progressive Action Congress (PAC) da Mojisola Adekunle Obasanjo ta Masses Movement of Nigeria (MMN)

Sarah Jubril ta samu ƙuri'a 157,560, wanda ake kallonsa a matsayin mafi yawan ƙuri'un da mace ta taɓa samu a zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya.

Tun daga lokacin, yawan mata masu shiga takarar shugaban ƙasa ya kasance yana hawa da sauka.

A zaɓukan 2007 da 2011, mace guda ce kawai ta tsaya takarar shugaban ƙasa.

A shekarar 2015 kuma, Oluremi Sonaiya ita ce mace guda tilo cikin ƴan takara 14.

Daga baya, an samu ƙarin mata da suka shiga takarar shugaban ƙasa ko mataimakinsa.

Samun mata a tikitin takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa a 2027 na nuna cewa mata na ci gaba da neman ƙarin dama a siyasa.

Me ke hana mata tasiri a siyasar Najeriya?

A wata tattaunawar da ta yi da BBC, shugabar mata ta jam'iyyar ADC ta ƙasa, Naomi Lassara Abel ta ce cigaban Najeriya ta dogara ne a kan shirin matasa da mata na shiga harkokin shugabanci a ƙasar.

Sai dai ƴar siyasar ta bayyana cewa duk da kasancewar mata jigo ne a siyasar ƙasar, ba sa samun damar bayyana fasaha da ƙwarewarsu wajen gudanar da mulki a matakai daban-daban na ƙasar.

''Kamar yadda muka sani ana mana kallon kamar muna da rauni ne haka. Tun farkon siyasa musamman a Najeriya, mata da yawa ba sa shiga a dama da su ba. Sai a shekarun baya-bayan nan ne suka fara shiga harkar siyasa,'' in ji Naomi.

Naomi Lassara ta bayyana wasu abubuwa da ta ce suna cikin ƙalubalen da mata ke fuskanta kamar haka:

  • Al'adu
  • Addini
  • Ƙudi
  • Raunin mata
  • Yawan maza a harkar

Naomi wadda ta taɓa yin takarar majalisar jihar Gombe domin wakiltar mazaɓar Kaltungo ta Kudu da ma majalisar tarayya, ta ce ta yi takara, sannan ta yi shugabancin jam'iyya, don haka ta ga komai.

"Idan kin fito takara sai ki ga maza da yawa sun fito, don haka kafin ki fito ki nuna ƙwanjinki, sai ki ga sun kwashe komai,'' in ji ta.

Ta ƙara da cewa mata sun fi yawan ƙuri'u a zaɓen Najeriya, "Muna ƙoƙarin zaɓen kanmu. Ni na yi takara kuma lallai mata sun ban goyon baya sosai. Amma in maka misali, za ka ga shugabannin jam'iyya a mazaɓa, wataƙila a kujeru 18, ka ga mace ɗaya ce kacal wato shugabar mata.''

Ta ƙara da cewa idan ya kasance a babban zaɓen mazan sun fi yawa, to duk yawan ƙuri'ar mata ta tafi wajen mazan.

Sai dai ta ce ana samun cigaba sosai a yanzu, domin a cewarta, ƙungiyoyin mata da jam'iyyu na ƙoƙari sosai wajen wayar da kan mata da janyo su cikin harkokin siyasa.