UAE ta fara binciken rassan Bankin Masar bayan matakin Amurka kan Iran
Babban bankin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ya sanar da fara gudanar da bincike na musamman cikin gaggawa kan rassan Bankin Masar da ke ƙasar, bayan matakin Amurka na katse alaƙar bankin da tsarin kuɗin Amurka domin ƙara matsin lamba kan tattalin arziƙin Iran.
A cikin wata sanarwa, babban bankin na UAE ya ce binciken zai haɗa da zurfafa nazari kan bayanan da suka shafi lokacin da hukumomin Amurka suka ambata a sanarwarsu.
Bankin Masar, ɗaya daga cikin manyan bankunan gwamnati a ƙasar Masar, ya ce zai tuntuɓi Ma'aikatar Kuɗi ta Amurka domin neman ƙarin bayani tare da ɗaukar matakan da suka dace.
Bankin ya kuma tabbatar da cewa rassansa da ke UAE na ci gaba da ba abokan hulɗa hidimomin banki bisa ƙa'idojin da suka dace.
Matakin da Amurka ta ɗauka na daga cikin ƙoƙarin farko a fili na ware tattalin arziƙin Iran, inda Washington ta ce ta gano hanyoyin da gwamnatin Iran da dakarun juyin juya halin Iran ke amfani da su wajen samun kuɗaɗen shiga, tare da gargaɗin cewa ƙasashen da ke taimaka wa Iran za su iya fuskantar irin waɗannan takunkumai.