Ba za mu mutu ba idan ba mu ci gaba da sarrafa uranium ba - Iran

Asalin hoton, Getty Images
Yousef Pezeshkian, ɗan shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian, ya ce rayuwar mutanen Iran ba ta dogara ne kan aikin sarrafa da inganta sinadarin uranium ba, yana mai cewa "idan ba mu yi hakan ba, ba za mu mutu ba."
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Yousef ya bayyana cewa ba ya adawa da sarrafa uranium, kuma yana biyayya ga duk wata shawara da Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran da kuma jagorancin ƙasar suka yanke.
Sai dai ya ce ya kamata a fahimci dukkan fa'ida da illa kafin ɗaukar kowace irin shawara.
Ya ƙara da cewa makamashin nukiliyar Iran ba ya dogara kacokan da aikin inganta uranium, yana mai nuni da cewa har yanzu man fetur ɗin da tashar samar da wutar lantarki ta Bushehr ke amfani da shi ana shigo da shi ne daga Rasha, ba a cikin gida ake samar da shi ba.
Yousef Pezeshkian ya kuma ce akwai wasu fasahohi da suka fi muhimmanci ga tsaro da gudanarwar ƙasar, amma ba a ba su kulawar da ta dace ba, yana mai cewa Iran ba ta nuna irin wannan ƙwazo wajen bunƙasa waɗannan fannoni.
















